P...16

531 73 12
                                    

*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*-•«Start, on 23/2/2020»•-*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*-•«•Be smart•»•-*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*16*

_Bayan kwana biyu._

_Yau ta kasance ranar weekend ce babu makarantar boko Islamiyya kuma hutu mu ke._
_Gidan ba kowa ya yi tsit daga ni sai Aunty Intisar da Aunty Khairat su kad'ai ke ta washshagale'walle a cikin gidan kasancewar su Mummy sun d'an fita su sha iska, saboda a wannan lokacin bana jin dad'in fitar ne shiyasa ban bi su ba wanda hakan ya sa na koma bedroom na yi kwanciyata ina sharb'ar baccina cikin kwanciyar hankali da walwala ba tare da fargabar komai a raina ba._

_Ina tsaka da sharara bacci na mai cike da jin dad'i, naji alamun kamar ana kokarin tayar da ni daga daddad'an baccin da na kwance ina yi._
_Firgigit na farka tare da mikewa zaune Ina kallon mutunen da ke kokarin tayar da ni cikin mamakin irin wannan mugun d'atun._
_Aunty Intisar ce tsaye a saman kaina tana bi na da wani wulakantaccen kallo cikin yanayi na ya mutse fuska kamar wadda ta ga Kashi_
_Kau da kai na na yi gefe cikin mugun jin haushin kalar wannan wulak'ancin, kai tsaye na ce mata "Lafiya?"_
_"K'alau.!" Ita ce amsar da ta bani daga bisani kuma ta ce "Sannu.! Sannu.! Sannunki Hajiya ko kuma na ce Sarauniya mai jiran gado.!_

_Murmushi mai cike da k'unar zuciya na saka kafin na ce mata "Idan wani abu kike buk'ata kiyi maganar ki kai tsaye ba sai kin tsaya shakku ba"_
_Ta ce "Awww hakane fa! Tuba na ke ranki ya dad'e shugabar masu Fitsarin kwance, ayi mini afuwa kar a hanani Abincin dare yau"._
_Banza na yi da ita na kashe kunne guda ina sauraren ta har ta gama surutan ta sannan ta ce "daman Madam Ya Abir ne ya ce na zo na tadoki ki had'a mashi Coffee Idan kin ga dama fa amma" Tana gama fad'in hakan ta kama hanyarta ta ficewa daga nan_

_Murmushi mai cike da k'ayatarwa na saka kafin na rairafo daga saman gadon na sauko k'asa, na ziyarce Bathroom domin biyan tawa buk'atar tukunna._

_Tana baro wajen da nake Zuciyarta cike fal da farin ciki ta samu Aunty Khairat da ta gama shirya duk wani abinda suke k'ok'arin shiryawa, Dariya suka saka tare mai cike da zallar mugunta sannan suka tab'a hannayensu waje guda suka rumgume juna cike da wani hamshak'in farin ciki, kamar wad'anda aka yi ma bushara da gidan Aljannah, sai dai lokaci guda kuma Aunty Khairat ta b'ata fuska ta ce "Anya Kina ganin wannan abin ba za a iya samun wata matsala ba kuwa?"_
_Murmushin mugunta Aunty Intisar ta saka kafin ta soma cewa wani abu, ta ce "Hmm Matsala? Wacce Matsala kuwa Aunty, bafa kowa a gidan yau duk da da wad'anda ta ke takama da su a gidan duk basanan yau sun yi wajen harkokin gabansu, kin ga ki kwantar da hankalinki koda wani abun ma ya faru ni nasan yanda zan yi mu fidda kan mu a ciki, kin gane?" dariya tayi kafin ta ce "amma fa gaskiya ke ba k'aramar makira ba ce k'anwata, shi ya sa nake mugun ji da ke wallahi"_
_Ita ma dariyar ta saka tare da jan hannun ta kamar k'aramar yarinya suka koma gefe._

.....

_Bayan na fito daga cikin Bathroom ba tare da na tsaya wani dogon shiri ba na finciko wani d'an guntun mayafina na rataya ma k'ok'on kai na, dan ya yi man kashedi akan dik sanda ya kara ganina ba mayafi a kai sai ya yi man Aski irin na tsofaffin dori._

_Ina saukowa k'asa direct hanyar shiga kitchen na nufa cikin karfin hali domin tun lokacin da na saka k'afafuwa na, na fara tunkarar wajen naji gabana na tuntsurewa sama yana dawowa k'asa ridididiii kamar wajenda bene mai hawa dubu ya redo k'asa wanda na kasa gane dalilin faruwar hakan, cikin wasi-wasin da zuciyata ke man nayi hakuri na dake abin a cikin zuciyata na saka full'stop a dai-dai bakin kofar shiga kitchen din dan ji nake kamar na fad'i k'asa kwance a wajen, kafin na ankara sai jin nayi an saka hannaye da dikkanin ilahirin k'arfin da Allah ya yi ma mai wad'annan hannayen Ya bangaza ni cikin kitchen d'in da k'arfin tsiya, wanda hakan yasa kai tsaye naje na rumgume wata katuwar tukunya wadda ke cike da tafasasshin ruwan zafi a cikinta gabadai ta wanke man jiki da su, wata rikitacciyar k'ara ce wadda ni kaina ban san da na iya ta ba naji na saki kai tsaye daga nan kuma ban sake sanin inda kai na ya ke ba._
_More comments_
_More typing_
*Follow me on wattpad and vote-Smart_Feenert*
*Be smart*
*^Pls shere^*

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now