*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**_Alhamdu lillah, dukkan yabo da godiya sun tabbata a gurin Shugaban halitta Allah (S W A), tsira aminci su dad'a k'aruwa a gurin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) Ameen ya rabbi_*
*_A jiya Laraba 12/8/2020 k'ungiyar Kainuwa ta cika sheka ukku da kafawo, ina rok'on Ubangiji Allah ya k'ara daukaka ta ya kuma k'ara haskaka ta ya k'ara mata d'imbin mabiya da masoya bila adadin wad'anda zasu amfane ta su kuma amfana da ita. Ameen ya rabbi_*
😍😍😍😍😍Allah ya ja zamanin kainuwa dashen Allah dashin da ba na mutum ba.!*_Wannan page gabad'ayanshi sadaukarwa ne ga K'ungiyar Kainuwa writer's da kuma mutanen dake cikinta musamman ma_*
*_Tawan 👉🏻 Zahra Abdul {Momyn Ahlan} tare da My 'Yar Aljannah Real Nana Aisha. tare da dikkanin wad'anda ke cikin kungiyar kainuwa Allah ya ja zamaninku Ameen Lov u more💋_**P...29*
Sosai su Daddy suka tsinci kansu cikin halin damuwa tare da tunanin abinda ke damunshi wanda har ya yi sanadiyyar jawo mashi wannan babbar lalurar haka. kwanan shi biyu a Asibitin ya d'an fara samun sauk'i, babu irin yanda su Daddy basu yi da shi ba akan ya gaya masu damuwar da take damunshi amma hakan ya gagara. Lokacinda ya cika 4day's a Asibiti aka sallame shi domin sauk'i ya zo mashi sosai sai dai koda hakanan an d'ora shi a bisa hanyar shan magani. ranar talata aka kai lefen Aunty Khairat. Wa'iyazu billah abin dai ba'a cewa komai domin naira ce tayi aikinta kamar abinda ake zula hannu ana tsamowa a cikin k'asa. haka su ma b'angarensu Amaryar sun zage damtse wajen fidda d'iyarsu kunya inda suka yi mota hud'u ta kayan Gara kamar ba a mutuwa. ranar Laraba abokanan Ammie suka je ganin d'akin Amarya, Ma sha Allah iya tsaruwa gidan ya tsaru kamar a kasar turai sai dai abinda ya d'aurewa 'yan ganin d'akin kai shi ne, gidan compound house ne yana da part3 had'i da na mai gidan, sannan dik abinda ke cikin part d'aya akwai shi a d'ayan, 2bedroom ne tare da Bathroom da kuma 1palour'n had'i da kitchen har izuwa wajen dinning table komai iri d'aya ne wanda hakan ya yi sanadiyyar saka mutane da dama cikin zullumi musamman babbar k'awar Ammie Hajiya Maryam da jiran komawarsu wajen Ammie kad'ai take yi domin kai mata rahoton abin tunda d'imi-d'iminshi. bayan 'yan ganin d'akin sun koma wajen Ammie har wasunsu sun fara tafiya gidajensu. Hajiya Maryam ce zaune kusa da Ammie inda take cewa "Ni fa wannan al'amarin Hajiya Rafi'a ya fara d'aure man kai, yanzu bakya ganin akwai wani k'udurin da suke da shi game da d'ayan apartment d'in?." Murmushi mai cike da takaici Ammie tayi kafin ta ce "hmm Maryam kenan! ai dik wani k'udurin da suke da shi yanzu lokaci ya k'ure masu, komai ya zo k'arshe dan tun farko sun riga sunyi asarar damar da suke da ita tuntuni! kuma kamar yanda suka nuna part d'aya ne namu haka zamu rik'a mu zuba masu Ido dan muga abinda zasu yi da shi!." Maryam ta ce "Yanzu kenan kina nufin a k'yale su kenan?." a d'an fusace Ammie ta ce "Allah yasa gaki Maryam ai dik wanda ya ci tuwo da ni wlhy miya ya sha! Ni yanzu Boka Dundum kad'ai nake jira dan ya ce ranar daren bikin nazo na same shi ayi mai gabad'ai! Ke bama wannan ba ni yanzu dik abinda yafi damu na a yanzunnan baifi assirin da nayi wa Abban Khairat ba da naga yana bid'ar k'aryewa.!" Maryam ta ce "Kamar ya kuma Ammie'n Khairat .?" sai da ta d'an numfasa kafin ta ce "wlhy kwanan nan dik na kasa gane mashi, yanzu wani irin hali ne yake nuna man wanda ban san da shi ba game da wannan auren, kwata-kwata yanzu baya son ya yi shawara da ni, dik wata shawara da zan bada game da wannan lalurar sai dai kiji ya ce man Ya ji, to me hakan yake nufi? shi ya sa nake tunanin ya kamata ace tun wuri naa taka mashi burki.!" da mamaki Hajiya Maryam ke kallonta kafin ta ce "Dama baki shirya ma wannan harkar ba kika fara ta?." Ammie ta ce "ban gane me kike nufi ba.!" ta ce "abinda nake nufi anan shine tun farko ke kika yi sake har ake son yi maki sakkiya ya kamata ace irin wannan shawarar sai dai ki bawa wani ba dai a baki ba, ke ko bada wannan auren da kike son ya tabbata ba ai irin Alhaji ba'a barinshi sakaka kamar iccen Dogon-yaro dole sai an had'a da Malamai idan ko ba haka ba kina zaune zaki ga mucciya tsaye a gabanki kun dai-daice ke da ita matsayinku guda a gidannan! yanzu abinda nake so dake shi ne, dik wani shakku da tsoron da kike jin suna addabar zuciyarki game da biyan buk'atarki ko wacce iri ce to ya zama dole sai kin fitar da su a cikin zuciyarki sannan zaki iya tsayawa kanki! ko yanzu idan har a shirye kike muna iya komawa wajen bokan kiji yanda za ayi.!" sake da baki Ammie ke kallonta harta ida k'ark'are zancenta ba tare da ta ce da ita ko uffan ba sai famar tunanin maganganun Maryam take da akwai alamun k'amshin gaskiya a cikinsu. ba tare da wani b'ata lokaci ba Ammie taje ta k'ara kimtsawa suka d'auki hanya. A b'angarensu Mummy kuwa suma shirye-shiryen bikin ne suke babu k'ak'k'autawa 'yan-uwa na nesa da na kusa wasu har sun fara zuwa. ranar Alhamis ta kasance daren ranar d'aurin auren, sai famar aikace-aikace ake dik da an nemo hayar masu yin aikin dan biki ne za'ayi bana wasa ba amma koda hakan suma su Mummy ba su yi zaune ba. haka ma b'angaren su Ammie. wajajen k'arfe 4:00pm muka dawo daga wajen gyaran jiki tare da anso d'unkunan mu na anko kala hud'u-hud'u dik da su Daddy sun hana ayi ko wanne Event a cewarsu sai bayan an d'aura Aure dan ba a lokacin Amare zasu tare a gidansu ba sai bayan biki da sati biyu wanda wannan shawarar tana d'ai daga cikin ta Mummy. haka ma b'angarensu Daddy su ma suna can suna fama da nasu tawagar a d'ayan gidansu wanda ke Area1 daman ya gina shi ne sabida manya-manyan bak'insu. washe gari bayan andawo daga wajen sallar juma'a aka taru a GeneralMosquit inda taro ya yi iya taro kamar taron sallar ED ba a wani b'ata lokaci ba aka shiga d'aura auren Ya Abir da Khairat daga bisani kuma aka sake d'aurawa da Fatima akan sanadaki ₦500k-500k Lakad'an ba Ajalan ba. wanda ya kasance dik su suka wak'ilce 'Ya'yansu na Fatima kuma Daddy ya wak'ilce ta Abba ya wak'ilce Ya Abir, daganan dai aka yi Fatiha kowa ya shafa sannan aka watse taron. Ya Abir tare da Ya Bikhram had'i da d'an k'aramin k'anensu Fadil kowa yaja abokananshi aka yi wajen cin abinci anan d'ayan gidansu dake Area1 da yake gidan part-part ne kasancewar tun lokacin da aka gina gidan Daddy ya ware masu nasu. tun lokacin da suka d'auko hanyar zuwa gidan jiri ke d'aukar Ya Bikhram kamar ya fad'i wanda hakan yasa ya bawa d'ai daga cikin Frnds d'inshi makullin motar yaja su. suna isa get d'in gidan suka yi horn Mai-gadi ya zo da sauri ya wangale masu shi, bayan sunyi parking wasu har sun fara fitowa waje wanda hakan yasa shi ma Ya Bikhram d'in fitowa sai dai k'afarshi ko k'asa bata ida sauka ba aka ga ya b'ingire ya fad'i k'asa ko motsi babu balantana numfashi, hankalin kowa dake wajen idan ya yi dubu sai da ya tashi musamman Angon da fitowarshi ke da wuya a cikin motar, a hanzarce yayo wajen d'an uwanshi yana jijjigawa shi tare da kiran sunanashi cikin wani mugun tashin hankali ganin shiru kamar babu alamun rayuwa a gangar jikinshi yasa nan take aka d'auke shi aka nufi hanyar Asibiti da shi. suna isa kai tsaye aka bashi gado, sai dai komai ya d'an fara lafawa hankalin kowa ya dawo a jikinshi sannan Ya Abir ya kira Daddy ya shaida mashi halin da ake ciki, ba'a d'auki tsawon wani lokaci mai yawa ba Daddy da Abba had'i da sauran abokanansu hud'u suka iso Asibitin cikin wani mugun tashin hankali. bayan sun je sun ga likita suka shiga d'akin da aka kwantar da shi suka duba shi har sun fito ta dalilin likitocin da suka shiga ciki zasu yi wasu gwaje-gwaje sai ga d'ai daga cikin likitocin ya fito anan kowa ya mik'e tsaye cikin zumud'i ya yo wajenshi yana tambayar abinda ake ciki, cikin damuwa likitan ya ce masu su kwantar da hankalinsu yanzu Allah ya ba su nasarar ceto rayuwarshi ya tashi, har ma yana son yin magana da Daddynshi, sannan ya k'ara da cewa "dan Allah idan yana kusa ya biyo ni dan ba lokaci.!" a rud'e Daddy ya rufa mashi baya har suka isa d'akin inda Ya Bikhram yake kwance rai a hannun Allah baka jin k'arar komai sai ta nak'urorin dake d'ahe a jikinshi. cike da mugun tausayi Daddy ya isa wajenshi da idanuwanshi ke lumshe kamar mai yin baccin, fita waje likitocin suka yi gabad'ai suka basu waje wanda a dai-dai wannan lokacin Daddy ya rugume d'an nashi cikin hawayen dake fita a cikin kwayar idanuwanshi ya ce "Bikhram me yasa zaka yi wa kanka haka? yanzu ka dubi halin da ka jefa kanka a ciki! wai meke damunka ne da har ya gagara ka fad'a muna?.!" dik a cikin wata matsananciyar damuwa yake mashi wad'annan tambayoyin. cikin k'arfin hali Ya Bikhram ya d'an bud'e idanuwanshi kad'an yana kallon mahaifinshi cike da tausayi daga bisa ni kuma cikin wata dashashshiyar murya wadda ko fita bata yi da kyau ya ce "Daddy dan Allah ku yafe man a yanzu bana buk'atar komai a gare ku sama da addu'a ko bayan bana raye domin ciwo na ba na tashi ba n.....!" cikin wani matsanancin tashin hankali Daddy ya ce "haba Bikhram, ban sanka da haka ba! tun kana d'an k'ank'anen yaronka kake da matuk'ar jajircewa akan komai baka tab'a sadaukarwa ba, dik wata wahalar da kake fuskanta ga abin zaka daure ne har sai lokacinda kaga ka samu yin galaba ga wannan abin! to dan Allah ko yanzu ka jajirce karka sadak'at da rayuwarka da wannan furucin.!" ya ce "A'a Daddy a yanzu mutuwa ita ce tafi komai futu a gare ni! ni kaina ina ji a jiki na ba zanyi tsawon rayuwa a cikin duniyarnan ba! Daddy na riga na rasa ta a rayuwa ta rasawa kuma ta har abada! Daddy na sota tun kan ta ida mallakar hankalin kanta! na kwallafawa raina burin aurenta da dad'i ko akasin haka! sai dai rana d'aya ta zamo tamkar ranar mutuwa a gareni wadda a yanzu har na fara jin rad'ad'in zuwanta ga ruhina! ranar da ta kasance ranar rabuwa ta da ita rabuwa kuma ta har abada domin koda na rayu a yanzu Daddy ina ji a jikina kamar ba zanyi tsawon rayuwa ba.!" a gid'ime Daddy ya ce "wace ce ita? ka gaya man my son! wlhy nayi maka alk'awarin koma wace ce sai nayi tsaye da k'afa ta dan ganin ka mallake ta koda kuwa hakan shi zai kawo k'arshen numfashi na a duniya muddin zaka samu salama a rayuwarka.!" hawaye masu zafi ne suka fara gangaro mashi a cikin dashasshin idanunshi da basu bud'e basu rufe sannan ya ce "Daddy a yanzu lokaci ya riga ya k'ure muna, ko da ka sani ni kaina ba zan tab'a yafewa kaina ba idan har ta sanadiyyata wani mummunan abu ya faru a tsakanin aurensu, a halin yanzu ina jin kamar nafi kowa farin cikin kasancewarta mata ga wanda yake matsayin Yaya ne a waje na! wanda nake da tabbacin zai bata dik wata kulawar da nake da k'udurin bata a duniyarnan zai bata dubunta sann........!" Numfashin shi ne ya fara sark'ewa a daidai wannan lokacin wanda hankalin Daddy ya yi k'ololuwa wajen tashi a guje cikin rud'ewa yaje ya kiranyo Doctor's wad'anda daman suna bakin k'ofa a tsaye, nan take suka yo wajenshi inda harda Ya Abir da Ya Fadil suka biyo bayansu cikin tashin hankali. Likitocin suka nufi wajenshi da niyyar taimaka mashi ya yi k'arfin halin d'aga masu hannu cikin k'ik'k'inniyar magana ya ce "karku wahalar da kanku a kaina dan mutuwa zanyi sai dai kafin lokaci na ya ida k'arasowa ina son in barwa d'an uwana wasiya.!" Inda yake nuna Ya Abir da d'an yatsan shi guda wanda a hanzarce ya k'araso wajenshi ya ce "K'ane na ka kwantar da hankalinka in sha Allah zaka tashi da k'afafuwanka ba zaka tafi ka barmu ba.!" Murmushi k'arfin hali Ya Bikhram ya sakar mashi sannan ya ce "Yaya mutuwa ita ce hutu a gare ni ba mai tsallake kwanakinshi! a duniya ina ji ba wanda ya kaini son Fatima, sai dai Allah ya k'addara ba nine mijinta ba kuma na d'auki k'addara hannu bibbiyu na rik'e kuma a haka ina godewa Allah da ya k'addara kai ne mijinta na gaskiya! Ina maku fatan alkhairi sannan wasiya ta a gareka shi ne ka kula da Fatim.......... nan take ya fara twari afujajun numfashin shi na tafiya sama wanda hakan yasa nan take Ya Fadil ya yanke jiki ya fad'i inda saura Doctors d'in suka yo wajenshi wasu kuma suka yi wajen Ya Bikhram sai dai kafin kace me tuni rai ya yi halinshi Ya Bikhram ya tafi. wani Dummm! ne ko wannensu yaji a cikin kanshi dik da likitocin sai da suka zubar da kwalla akan tausayin abin Daddy ba abinda yake nanatawa sai kalmar "Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un! Ya Abir kuwa a hankali ya tako ya yo wajenshi har ya kawo daf da gawarshi ya rikice inda ya shiga sambatu yana fad'in "karka tafi d'an uwa na ka barmu, me ya sa zaka cutar da kanka haka k'ane na? me yasa ka b'oye muna damuwarka ga Fatima dik dan ka faranta muna rai? a yanzu ba wanda yafi cancanta da ya aure Fatima sama da kai! Doctors dan Allah ku tada shi bai mutu ba! bai mutu ba fa....!" a hanzarce sauran likitocin suka kamashi suna son natsadda shi amma ina abin ya cutura da k'arfin ya fizge kanshi ga rik'on da suka yi mashi ya sake nufatar wajen da gawar Ya Bikhram take cikin wata k'ara wadda dik wanda ke cikin d'akin har wanda ke waje sai da ya girgiza da jinta nan take ya sulale k'asa ya fad'i kwance. tashin hankali ba irin wanda kowa bai shiga ba musamman su Daddy da suke wajen. Ya Fadil da Ya Abir dik kwantar da su aka yi a cikin Asibitin. sai da komai ya d'an lafa sannan Daddy ya samu damar kiran wayar Mummy da ita ma tun d'azu take cikin bedroom kwance a saman gado ta kasa sakewa illa fad'uwar da take jin gabanta nayi mata sama da k'asa, k'arar wayarta ce da taji ta soma ruri yasa a hanzarce ta d'auka da sallama, jin muryar Daddy wata iri ya k'ara tadda mata hankali nan da nan taji zuciyarta ta yanke inda cikin rud'ewa take tambayarshi abinda ke faruwa sai da ya yi kamar ba zai fad'a mata ba sannan ya cije dai ya gaya mata babu Ya Bikhram. Ammie ce tsaye a filin gidanta tana zabga rashin mutumcin tare da zage-zage, sai Khairat dake yanke jiki tana fad'uwa sai ta tashi ta koma, 'yan biki kuwa sai famar kallon ikon Allah suke yi, Hajiya Maryam ce ke cewa "wannan cin amanar har ina? ni ina na tab'a jin anyi haka? ai ko za ayi ana sanar da kai kam! wlhy koda wasa karki yarda idan har shi Alhajin ya yi shiru ya k'yale sabida yana d'an-uwanshi ke kam karki yarda ki k'yale dan 'yarki ce aka zalumta! yo ai ni naga mugunta, yanzu idan ba dan da Alhaji Sulaiman ya je d'aurin auren ba da hakanan za a kai maki 'ya ba tare da ta san za'a had'a ta da kishiy..........!" ihun da taji Ammie ta buga ne cikin kururuwa tana zagin wad'anda suka zo mata bikin ya katse mata hanzari inda taji tana cewa "Kai da kazat uba kowa ya sani inda yayyi an fasa bikin ba za a yi ba.!" cikin mutuwar jiki Hajiya Maryam ta zo da hanzari taja ta suka koma d'aki sannan aka tattalo masu Khairat aka jibge masu ita a d'aki daganan kowa ya fara harmar sanin inda dare ya yi mashi inda 'yan bikin suka yi gungu-gungu suna tafe suna labartawa tun kafin su bar gidan. bayan kowa ya watse ne Khairat ta farfad'o inda ta ci gaba da yin kukanta hinhinhin tana cewa "wlhy Ammie ba zan zauna da kishiya ba musamman Fatima! na tsane yarinyarnan ko kad'an bana sonta Ammie! Ammie me nayi ma Ya Abir ne da har ya yaudareni haka? me na mashi........ uhum uhum humhumhun!." tsananin kukanne ya ci k'arfinta wanda har sai da ta dawo rafka kanta a saman bangon d'akin tana fad'in yau sai ta kashe kanta, ita ma Ammie kama mata tayi suka yi zaune suka dank'are mai isarsu harda su shashshek'a, Hajiya Maryam kam sai jimamen abin take wanda har yanzu ta kasa gazgata k'arya ne ko gaskiya nan take taji wata shawara ta fad'o mata kai tsaye a hanzarce ta dafa kafad'ar Ammie da har ta fad'i kwance saman gado ta rufe fuskarta da pillow ta ce "Ina da wata shawara idan ta maku.!" Nan take kukan da suke ya tsaya cakk tare da bata aron hankalinsu gabad'ai cikin muryar wanda ya d'ank'are wani mahaukwacin kuka Ammie ta ce "wacce irin shawara ce?." Kai tsaye Hajiya Maryam ta fitar da sautin wani banzar murmushinta na makirci ta ce "me zai hana a kawar da Iyayen sannan a d'aura alhakin kisansu ga mayyar.!" wata irin mugunyar walkad'owa ce Khairat tayi da kanta ta dubi Hajiya Maryam nan take taji wani irin farin ciki ya mamaye ta kamar babu wata damuwar dake damunta ta ce "wannan shi ne sakamakon tukwicin da zamu basu.!" Ammie ta ce "tabbas shawararki abin dubawa ce Maryam amma ina zamu samo makasan ko mu zamuyi da kanmu?." Maryam ta ce "kubar komai a hanuna ni nasan yanda za a yi.!" wayar Ammie ce da ta soma ruri hankalinsu ya koma wajen, number Abban Khairat ce da ta gani a rubuce ranta ya soma b'aci sai da tayi kamar ba zata d'auka ba can dai ta yanke shawarar d'agawa taji abinda za ya ce dan ta samu damar zazzage mashi kayan bala'in da suke damunta a kai, tana karawa a kunnenta ba tare da tayi wata sallama ba ta ce "Ina fatan dai lafiya?." Kai tsaye ya ce mata "Ku same mu yanzu a gidan Mukhtar.!" a fusace ta ce "ko zan iya sanin dalili hakan babbak'un munafukai?." sai da Abba ya maimata wannan kalmar cike da mamaki ya ce "Rafi'at kina cikin hayyacinki kuwa? ni kike kira munafuki?." ta ce "to idan ban kiraka da munafuki ba wanne suna kake son na kiraka da shi?." ya ce "to shi ke nan kin kyauta! Bikhram ne Allah ya yi cikawa.!" yana gama fad'in hakan cikin k'unar rai ya yanke kiran dan karta k'ara b'ata mashi rai still kuma yana nanata wannan kalmar ta "munafukai." kyalci ya yi cikin mugun jin haushin abin ya koma cikin jama'a domin yi ma Ya Bikhram sallah. yana yanke kiran Ammie ta ce "aikin banza, ina ruwanmu da wata mutuwar ai dik alhakinmu ne ke fita tun yanzu sun fara ganin abinsu tun ba aje ko ina ba.!" a rikice Khairat ta ce "Ammie wani abu ne ya faru da Ya Abir?." a tsawace Ammie ta ce "ai da hakan ne ma wlhy da nafi kowa farin ciki akan wannan mummunar cutar da ya yi muna ya kunyata mu a gaban jama'a .!" sai a sannan Khairat taji hankalinta ya d'an kwanta tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai had'e da cewa "to me ke faruwa ne Ammie?." Kai tsaye ta ce "Bikhram ne wai ya rasu bayan an d'aura auren, to mu ina ruwanmu.!" nan da nan wani sabon kuka ya k'ara gwabcewa Khairat ta fad'a saman gado ta kwanta ruf da ciki, sake da baki su Ammie ke kallonta cikin mamaki da d'aurewar kai Ammie ta ce "meye ne na kuma kuka? Allah an na tuba ke da ya kamata kiyi farin ciki ko dan abinda suka yi muna amma sai ki cika mana kunnuwa da kuka haba dan Allah ki barmu da abinda yake damun mu ma ya ishe mu.!" cikin kukan ta ce "Ammie me zai hana ni yin kukan farin ciki kasancewar wannan abin, wlhy ko kad'an banji ciwon mutuwarshi ba dan da shi aka had'a baki aka cuce ni.!" dariya dukansu suka saka sai a sannan Hajiya Maryam tayi gyara murya ta soma cewa "Yanzu dai abinda yafi muhimmanci a gare mu shi ne, muje wajen Boka Dundum muji abinda za muyi kafin mu kaiga aikata abinda muke da niyya.!" Ammie ta ce "Eh kuma wannan shawara ce mai kyau, bara na d'auko mayafi na mu tafi gabad'ai.!" ta k'ark'are maganar ne tana mai mik'ewa tsaye. dukansu fitowa suka yi waje suka tafi a motar Hajiya Maryam. B'angaren su Mummy kuwa tun lokacin da Daddy ya sanar da ita batun mutuwar Ya Bikhram ta fad'i zaune dab'as ba tare da ta yanke kiran ba ko kuma ta ce da shi wani abu ba domin mutuwar tayi bala'in girgiza ta sosai, Kaka ce dake kusa da ita sai kuma Yumra dake k'ok'arin shigowa d'akin a daidai lokacinda taga Mummy ta fad'i zaune tana fitar da wasu zazzafan hawaye ta tsaya cakk tana kallonsu. cikin wani mugun tashin hankali Kaka ke tambayar Mummy abinda ke faruwa, cikin karkarwar murya Mummy ta ce "Allah ya yiwa Bikhram cikawa a Asibitin yanzunnan Hajiya.!" salati Kaka ta fara d'auka kafin ta fashe da kuka, ita ma Yumra wani rikitaccen ihu ne ta buga wanda saida ya yi sanadiyyar fitowar mutanen gidan a wajen nan take ta fad'i kwance sumammiya, kafin kace me? gida ya rud'e gabad'ai sai koke-koke ake na jimamen mutuwar, haka su Daddy suka zo suka same su wanda su ne suka yi k'arfin halin lallashinsu har suka samu suka yi shiru, cikin awa guda gabad'ai gidan ya cika tank'il da mutune kama daga mak'ota, abokanan arziki harma da sauran ma'aikatansu na waje dana ciki wasu ma jirgi suka biyo suka baro k'asar da suke domin Daddy babban mutum ne na bugawa a jarida gaunoni da manya-manyan 'Yan siyasa dik sun hallara a wajen ba'a b'ata wani lokaci ba aka yi ma Ya Bikhram wanka tare da yi mashi Sallah sannan aka d'unguma gabad'ai aka yi mashi rakkiya izuwa makwancinshi na gaskiya. Su Ammie ne zaune a gaban boka sun gama gaya mai dik wani abinda ke damunsu inda kai tsaye ya ce masu "dama irin wannan ranar nake jira, shin kin tuna sadaukarwar da nace za kiyi?.!" Ammie ta ce "na tuna boka.!" Ya ce "to lokacinta ne ya gabato! da farko sai bayan an gama maki wannan aikin komai ya kammala sannan zaki yi wannan sadaukarwa.!" Ta ce "na aminta Boka da ko wacce irin sadaukarwa ce ka umarce muddin buk'ata ta zata biya.!" Ya ce "to shi ke nan, na farko dai zaki amshi wannan kullin maganin da hannun haggu, zaki zuba ma surukinki da kuma mijinki ne a cikin abin sha wanda shi ne zai zame maku makami na k'ok'arin aikata abinda kuke son aikatawa cikin sauk'i, zasu zamo bayinku ne dik abinda kuka saka su za suyi maku shi kuma dik abinda kuka ce ya tabbata sannan wannan Layar da nake k'ok'arin baki kin ganta?" Ammie ta ce "Sosai ma Boka." Ya ce "Sunanta Kamkam! Ita ce makullin dik wani assirinki a duniyar nan idan har kika yi sake kika kuskure daga sharud'd'an wannan layar to ba wai assirinku ne zai tuno ba amma abinda zai faru sai kun gwammace da ma assirinku ne ya tonu a bisa halin da zaku jefa kanku ciki.!" Ammie ta ce "da yardar k'arfin assirinka Boka wannan abin ba zai tab'a faruwa ba.!" Ya ce "da kun cece kanku.!" sannan ya k'ara da ce masu "karku kuskura ku bari a kashe wannan yarinyar, ko bayan an yanke mata hukuncin kisa ne kuyi dik yanda za kuyi ganin ta dawo hannunku sannan kuje mak'abarta ku gina k'abari daidai ita sannan ku saka wannan Layar Kamkam a cikin bakinta kafin ku turbud'e ta da ranta a ciki daga wannan lokacin aiki ya kare.!" Godiya mai tarin yawa suka yi mashi kafin su bar wajen cikin hanzari inda Hajiya Maryam ta wuce da su wani wajen suka had'u da wasu manya-manyan matsafan 'yan daba wad'anda ke cin naman mutum d'anyenshi su kuma b'ace a lokacinda suka ga dama, ana yi masu lak'ani da JAN BULO, hantar Ammie ce ta kad'a a lokacinda dik ta kalle fuskokinsu gabad'ayansu babu alamun rahama ko jink'ai a tattare da su, idanuwansu jawur suke kamar garura, ba tare da wani b'ata lokaci ba suka gaya masu buk'atarsu tare da basu photon Daddy da Mummy da yake Ammie dik tana da su, had'i da yi masu dik wani kwakkwaran bayani ta yanda zasu shiga gidan da kuma inda zasu same mutanen gida tare da basu photon yarinyar da suke son su kai a d'akin da akayi kisan su mak'ale ta ciki dan a aza alhakin mutuwar a gare ta, bayan sun ida k'ark'are masu bayanin ne, wad'annan 'yan daban suka shaida masu da su sa a ransu kamar ma aikin ya kammala yanda suke son shi tare da shaida masu cewa su basa amsar komai sai sun kammala aikinsu. haka dai su Ammie suka baro wajen zuciyarsu fesss da farin ciki kamar su fad'o ma Allah. direct gidan gaisuwa suka wuce inda suka yi zaune suka darje kukansu son ransu wanda hakan ya k'ara rikita gidan gabad'ai aka sake d'aukar wani sabon kukan ita kam Mummy mik'ewa tayi ta shige cikin d'aki ta barsu a palour domin ita ma a yanda take jin zuciyarta kiris ya rage ta biye masu a taru a zama d'ai, anan dai bayan komai ya lafa suke tambayar Aunty Intisar Ya Abir dan basu ganshi a waje ba, nan ta kwashe komai ta gaya masu cewa Ya Abir na Asibitin an kwantar da shi shi da Ya Fadil, wani irin hamshak'in farin ciki ne suka ji ya lullub'e su dik da basu nuna hakan a fili ba, nan take suka mik'e tsaye suka je suka yi wa Mummy sallama akan zasu je su duba su Ya Abir a Asibiti, ita kam godiya kawai ta masu har suka bar d'akin kallonsu take cikin mamaki, suna fita waje bayan sun bar gidan Hajiya Maryam ta ce "Alhmdu lillah kunga komai ya zo gidan sauk'i! ai shine alamun nasara! yanzu bara mu samu wata super market mu tsaya mu saya mashi soft drinks muje mashi da shi kayan dubiya tunda naji ance ba kowa a wajenshi sai security kuma kin san a waje suke, kinga daganan sai muyi abinda Boka ya umarce mu.!" Ammie ta ce "hakan ya kamata kam domin a wajenshi ne kad'ai nake ganin da wahalar shawo kai amma yanzu komai ya zo k'arshe domin wannan dama ce muka samu idan ko har muka bari ta subce muna to gaskiya ina ganin da wuya mu iya samun wata nan gaba sai dai idan k'ila wani ikon Allah.!" Maryam ta ce "Haba ke ko ai yanzu ba irin dah ba ne kin manta auren dake tsakaninshi da d'iyarki.!" Ammie ta ce "ban manta ba ko kad'an amma kinsan ai daga yau d'innan ne ko?.!" Maryam ta ce "haka ne! fatan nasara.!". haka dai suke tafiya suna firarsu har suka iso wajen wata super market suka yi sayayya bayan sun gama har sun shiga mota suka bud'e d'ai daga cikin drinks d'in wanda kalarshi ta banbanta da sauran dan gudun samun wata matsala sannan suka barbad'a wannan kullin maganin da Boka ya basu suka saka mashi, sannan suka girgije lemun ya game gabad'ai a cikin kwalbar sannan suka tadda mota suka bar wajen a hanzarce suka nufi Asibitin. d'akin da aka kwatar da su Ya Abir bai basu wata wahala ba wajen nema suna isa suka gaya ma security'n dake tsare da shi yanda suke da shi sannan aka basu waje suka shiga. sun iske shi zaune a saman gadonshi tare da Doctor's biyu a cikin d'akin suna duba shi, bayan sun gama gaisawa da Doctors d'in ne wanda a dai-dai wannan lokacin Doctors d'in ke k'ok'arin fita, shi ma suka shiga yi mashi sannu ya jiki ya amsa masu a dak'ile sannan suka shiga yi mashi ta'aziyya ya amsa masu da godiya Jim kad'an Ammie ta fito da kayan dubiyan a wajen ta d'auko cup guda ta zuba mashi wannan lemun ta bashi ya sha, ya ce mata "Alhmdu lillah, bana jin zan iya shan komai a halin yanzu, na gode.!" gabad'ayansu kallon kallon suka shiga yi wa juna cikin d'aurewar kai Ammie ta ce "Haba kai ko Abir ya zaka ce ba zaka sha ba ai gwara kasha ko kad'an ne domin zama da yunwa ba dad'i gashi har yanzu jikinka bai ida wartsakewa ba ai haka sai wata cuta ta k'ara kamaka.!" sai da dai suka yi da k'yar da walahaula sannan ya amshi kofin yana juyawa, cike da farin ciki Ammie ta ce "kasha mana Abir.!" cikin rashin kwarin jiki ya kai cup d'in a bakinshi ya sha wannan drinks gabad'ai ya shanye shi tasss wanda cikin mugun jin dad'in abin Ammie ta ce "ko a kara maka ne?." ya ce "a'a wannan ma ya is....!" bai ida k'ark'are maganar ba yaji kanshi ya fara juyawa nan take ya fad'i kwance a saman gadon daganan kuma sai bacci, dariya sosai su Ammie suka yi harda su tafawa suna k'ara jinjinawa k'arfin kaidin da suke da shi Khairat kuwa babu kunya taje ta sumbace had'ad'd'en bakinshi gaba ga su Ammie tana cewa "Kai nawa ne ni kad'ai.!" dukansu dariya suka k'ara saki sannan suka tashi suka je suka duba Ya Fadil, bayan sun gama b'artayarsu suka sake komawa wajen gaisuwar sai misalin Karfe 5:00pm sannan suka baro gidan inda Hajiya Maryam ta ajiye su gida sannan taja motarta ta nufi nata gidan tare da ce masu sai sun jita, haka dai suka yini yinin yau cikin matuk'ar farin ciki. misalin k'arfe 9:23pm Abba ya dawo gida a zuciya ba tare da Ammie ta san da zuwanshi ba sai da taji an kabro kofar d'akin da karfi ta kulle, a hanzarce ta tashi tsaye cikin shirinta na bacci ta bud'e fridge ta dauko Lemu wanda ta tabbatar da ta zuba ma wannan maganin ta had'a mashi da kayan fruit sannan ta nufe part d'inshi. da sallama ta ida k'arasawa ciki ganin bata same shi a palour'n shi ba yasa ta wuce bedroom d'inshi tana isa taji alamun yana watsa ruwa anan ta zauna zaman jiranshi har ya fito ba tare da ya ce da ita ko k'ala ba ya shiga gyara jikinshi, nan take ta mik'e tsaye cikin wani salo na makirci ta nufe wajen da yake ta shiga sarfa shi cikin wani salon yaudara, dik da a hasale yake amma haka yaji ya neme damuwarshi a gareta ya rasa ita kuma da ganin hakan hankalinta ya kwanta ta shiga bashi hak'uri tare da salelanin k'arya har ta samu ta shawo kanshi ya hak'ura ya manta da komai aka shiga duniyar nishad'i daganan ta samu nasarar yin galaba a gareshi ta bashi wannan maganin ya sha nan da nan shi ma ya kwanta bacci, koda ganin hakan ta sake wani banzan murmushinta mai cike da wata bak'ar ustazuwar yaudara ta ce "da ni kake zancen.!" nan take ta mik'e ta lalabo wayarta ta kira aminiyarta Maryam ta shaida mata dik yanda akayi, dariya dukansu suka saka kafin su k'ara jinjinawa kansu da kuma babban malaminsu shaid'an da ya kasance tare da su a lokacin da suke buk'atarshi a kusa da su. Misalin karfe 10:00pm Mummy ce da Daddy da kuma Kaka da sauran mutanen gida zaune anan babban Palour inda Daddy ya fara bud'e taron da addu'a sai bayan da kowa ya natsu sannan ya ce "Nasan kunji komai game auren da aka d'aura tsakanin Abir da Khairat da kuma Fatima.!" wani irin gummm ne wajen ya yi na d'an wani lokacin kowa na jin abin a ba zata musamman ma ni da na kasa gane inda zancen ya dosa dik da Ammie da Kaka sun dad'e da sanin wannan maganar tuntuni amma su ma sai da suka ji abin ya zo masu a wani iri, Daddy ne ya yi hanzarin katse shirun da yaji anyi inda ya soma cewa "wannan ba yinmu ba ne yin Allah ne kuma kowa da irin tashi k'addarar sannan ba mai auren matar wani ko mijin wata ina son Fatima ki d'auka cewa wannan ita ce k'addararki a yanzu domin mu bamu isa mu hana abinda Allah ya yi ba sannan......!" a hanzarce na mik'e tsaye cikin mugun tashin hankali na ce "a'a! a'a wlhy! Kaka dan Allah kice man ba gaskiya ba ne.!" nan da nan naji zuciyata ta katse na fashe da wani matsanancin kuka ina cewa "Kaka dan Allah kice man ba gaskiya ba ne..!" Kaka kam kasa cewa komai tayi tana kallo na cikin tausayi domin ita ma abinda take gudu kenan, ban jira ta bani amsa ba na bar wajen aguje na nufi part d'ina, a dai-dai lokacin Daddy ya dafe kanshi yana nanata kalmar "Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un!!!" Mummy ce ta tashi a hanzarce ta biyo baya na, sai dai kafin ta ida kawowa daf da kofar d'akin tuni na kabro k'ofar da k'arfin na saka key na kulle, babu yanda ba tayi ba akan na bud'e mata k'ofar ta shigo amma hakan ya gagara wanda hakan yasa kai tsaye ita ma tayi nata part a fusace. b'angaren su Daddy kuwa suma nasu sashen suka nufa inda nan take Aunty Intisar ta kira Khairat domin ta shaida mata halin da ake ciki, sai dai tayi mamakin abinda taji Khairat ta gaya mata na cewa ta san komai. haka dai wannan daren kowa ya kwanta zuciyarshi cike da jimamen abin a rai da kuma jimamen mutuwar Ya Bikhram da ta girgiza kowa. 2:00am Mummy ce zaune ita da Daddy a saman darduma sun gama sallar nafila domin haka kawai suke jin fad'uwar gaba na damunsu sai dai sun d'aura alhakin hakan ne ga mutuwar Ya Bikhram, kwankwasa k'ofar dakinsu ne da suka ji anyi ya ankarar da su ba tare da damuwar komai a rai ba Mummy ta kalli Daddy da shi ma ita yake kallo ta ce "Yanzu haka Yubra ce, amma bara naje naji abinda take buk'ata cikin darennan.!" ba tare da ta jira amsar da Daddy zai bata ba ta mik'e tsaye ta nufe kofar, tana bud'e wa taji an bangazo kofar da k'arfin sai da ta tashi fad'uwa k'asa Daddy ya yi hanzarin tare ta tare da maida dubanshi ga k'ofar, wasu samudawan mutane ne yaga sun fad'o masu cikin d'aki wajen su 5 sagagaga rik'e da wata zangarneniyar wuka a hannun d'ai daga cikinsu sai famar walkiya take yi. cikin mugun tashin hankali Daddy ya ce "Me kuke nema a wajenmu.?" kai tsaye d'ai daga cikinsu ya ce "Rayuwarku.!" cikin kad'awar hanta Daddy ya yi k'arfin halin cewa "Rayuwarmu duka tana wajen Allah kuma shi kad'ai ya isa ya amshe ta ga dik wanda ya so kuma a lokacin da ya so.!" dariya mai rikitarwa d'ai daga cikinsu ya yi sannan daga bisani ya sake turmuk'e fuska ya ce "kana fusata ni kaina na min zafi.!" Mummy ta ce "dan Allah kuyi hak'uri ku fad'i dik abinda zamu b.........." bata kai ga ida zancen da take ba taji saukar kaifi a wuyanta sai da mak'ogoronta ya fita a wuyanta, wata irin kururuwa ce Daddy ya yi a dai-dai lokacin da yaga matarshi ta fad'i k'asa kwace tana mirgina a k'asa ta fitar rai, ya d'ago kanshi kenan da yunk'urin aikata wani abu yaji shima an aza mashi kaifi nan take ya fad'i kwance a wajen da yake matacce, wani irin rikitaccen ihu ne suka ji a bayansu wanda ya yi hanzarin maido hankalinsu a wajen nan take suka ga Kaka tsaye a wajensu da fitowarta kenan a part d'inta ta dalilin kururuwar da taji Daddy ya yi kasancewar ita ma a wannan lokacin ba bacci take ba. ganin gawawwakin su Mummy kwance a kasa ya saka ta firgicewa ta sandare tsaye a wajen da take kafin ta maida harmata ga kallon wad'anda su kayi aika-aikar aiko cikin mugun tashin hankali ta yunk'ura zata guda d'ai daga cikin 'yan daban ya tab'e mata k'afa ta fad'i k'asa kwance nan take suka yo kanta suka mata yankan rago. suna gama aikin da suke suka bi d'aki-d'aki suna neman Fatima har Allah ya kawo su part d'inta inda suna mird'a kubar d'akin suka ji shi a rufe nan take suka fiddo master key d'insu suka sakama d'akin ya bud'e ganinta a kwance can k'ololuwar gado yasa suka k'ara kallon photo'n dake hannunsu da kyau sannan suka yo waje na tare da kara shak'aman wata fowder a hanci sannan suka d'auke ni sukutun suka kai d'akin da su Mummy suke wanda ke rik'e da wannan yuk'ar da ya yi kisan su Mummy da ita ya aza ta a saman hannuna ya dumulmule ta da kyau ta yanda yatsuna zasu fito a jikin yuk'ar koda an kai ga yin bincike sannan ya d'ebe safar dake hannunshi ya saka a aljilhun wandonshi nan take suka b'ace daga wajen kamar aljannu, ba wanda ya san abinda ke faruwa a gidan ko kad'an. Safiya na wayewa koda na tashi daga nannauyan baccin da bansan dalilin yinshi ba na ganni kwance a cikin Jini rik'e da wuk'a a hannuna ga 'Yan-sanda ta ko'ina kewaye da ni ta wani b'angaren kuma 'Yan Jarida ne mak'il a wajen sai d'aukar photo na suke tare da video suna magana wadda nake jinta tamkar gwalamniya, juyawar da zanyi bayana keda wuya naga su Mummy kwakkwanci a cikin jini har an zane wajen da suke kwance da marker kamar ance na dubi gabana naga Kaka kwance cikin jini ita ma kanta har ya fita daga gangar jikinta, cikin mugun tashin hankali na buga wata irin kafurar k'ara wadda ni kaina ban san da na iya ta ba nan take naga wasu Police mata k'arfafa sunyo wajena rik'e da handcuffs a hannun d'ayar. a gigice na yunk'ura zan mik'e tsaye domin nufar wajenda Kaka ta take kwance ina kiran sunanta da k'arfi cikin wani matsanancin kuka wad'annan 'Yan-sandan suka daddanne ni da iya k'arfinsu motsin kirki ma na kasa yi daganan na shiga muk'ur-muk'un d'in kwace kaina daga gare su sai dai hakan ya cutura..........!
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*Pls share*
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...