P...10

659 70 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

           *P...10*

_Tafiya Muke mai nisan gaske,  Kala ina bacci ina tashi  har na daina jin shi kwata-kwata a cikin idanuwa na._

       _Yubra kuwa har an tsufa wajen yin baccin sabida rashin sabo, Yumra kadai ke falke idanuwanta zwakwai kamar kuli-kuli tana latse-latsen wayar dake hannunta._

         _"Wai Yumra har yanzu bamu isa gidan ba?." Kai tsaye na jefo mata wannan tambayar cikin muryar gajiya._

       _Sai da tadan sake wani hamshakin murmushi wanda ya kara fitar da annurin dake shimfide a fuskarta sannan ta ce "Fatiti badai har kin kai ga gajiya ba?._

       _"Gajiya ai dole ne, tin dazu fa muketa kwasar hanya kamar jirgin sama amma sai ganin nake kamar muna komawa bay....."_

             _"Kuyima mutane shiru dan Allah hakanan, dik kun rude muna kunnuwa, dan haka  karna kara ji".  Ita ce   maganar da Ya Fadil ya jefo mana kai tsaye tare da ci gaba da latse-latsen wayar da yake kamar abin dole._

         _Cike da mugun haushi wannan tafiyar da taki karewa da kuma wannan maganar da naji Ya Fadil ya yi, dik sai na fauze na juya gefe tare da lumshe idanuwa ina furzar da hayakin bakin ciki a cikin baki na._

    _Itama Yumra ko kadan bata sake bi takaina ba wanda hakan ba karamin kona man rai ya yi ba._

       ~~~

     _Haka dai mukaci gaba da tafiya, kamar tumakin sake,_
        _Sai da muka iso cikin wani garin da bansan sunan shiba, sannan aka tsaya muka gabatar da Sallar Azzahar, sannan muka nufe wani Restored dake bayan Masallacin muka ci Abinci muka sha ruwa sannan muka sake daukar hanya._

                   _Bamu sake tsayawa ba kuma sai da aka fara kiraye-kirayen Sallar La'asar, Bayan munyi Daddy ya tambaye mu "ko a kwai wanda ke jin yunwa a cikin mu?" ganin kowa ya ce "baya jin yunwar"  yasa nima na ce "bana ji" amma bawai dan bana jinta ba. Lol_

~~~

          _Tun daga nan muka kama hanya bamu sake tsayawa ba sai da muka sauka Abuja cikin wani Katafaren gida wanda tun kafin ayi parking nake kallon irin tsaruwar da gidan ya yi kamar ba'a Nigeria ba._

~~~

              _Bansan lokacin da aka tsayar da Motocin ba sai da naga Yubra tadan zungureni cikin Murmushi ta ce,  "To sarkin Kalle-Kalle sai a fito waje ko!".  Ta karkare maganar ne  tana mai kwasar dariyarta ta keta, domin abinda na dade da fahimtar shi gareta kenan shine Shakiyanci, ba tare da nace da ita ko uffan ba na biyo ta bangaren da ta fita nima na fita domin bansan yanda zanyi na bude Marhin motar ba._

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now