*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**P... 2*
_Dwaɗe da hanci Kaka tayi karfin halin tashi tsaye ta raramo turare ta shiga fesama dakin kamar ta kare kwalbar, Gwaggo Talatuwa kuwa haushi dik ya gama daukarta sama ya buga ga bango dakin kamar ta fashe da wani fitinannen kuka haka take ji, domin tasan da gangan ne Na sakar mata wannan kafurar tusar tunda sai da na kawo daf da ita na sake a bita cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar komai ba, sannan kuma na nuna mata halin ko in kula,_
_Sai da komai yadan lafa warin ya fara tafiya a sannan Kaka ta samu damar yin magana, amma kafin ta soma cewa wani abu, sai da tadan sauke wata nannauyar a jiyar zuciya, sannan ta ce "Waih Talatu kinji wannan irin bakin bala'in da Fatima ta sauke mana?",_
_Cikin tanke fuskar nan takin kamar anwa zawo yayyafi, ta ce "Hmm Inna kenan, ai da gangan ne tayi dan tasan zata muzguna muna, ba kiga yanda tayi ba? Sai da fa ta kawo dai-dai da kussayen hantuna na inda nake shakar iska ta sake man ita sannan ta wuce, wannan wacce irin bakar masiface haka, ni dai insha Allah gobe zan kwashe komatstsena na tafi na bata waje tunda naga alamar zama nane bata so a gid........"_
_Bata kai ga karasa zancen ba Kaka ta dakatar da ita ta hanyar ce mata, "Allah yasa gaki Talatu, yanzu akan Fatima zaki bar gidan nan, ai ni a tunani na kin kai matsayin da zaki iya hukunta ta idan ta yi wani abin da ba daidai ba, amma barni da makira wlhy yau kafin ta kwanta sai ta fadi uban da ya aike ta, dan sai na zane mata jiki tsaf inga wanda ya daure mata...."_
_Ni da ke labe a bakin kofar, kamar wata babbar munafuka, da na gama jin dik abin da suke tattaunawa akai, Dan ina gama lalurata a hanzarce na dawo bakin kofar na labe saboda daman nasan sai sunyi wata maganar a kaina,_
_Sai da nadan murmusa kadan kafin na kai ga fadawa cikin dakin dauke da wakar Alagidigo, dan ita ce makwahin sallamata,_
_Ina isa a bakin gado na hira sama-sama na farmashi, a daidai wannan lokacin naga Kaka na shirin sauka kasa daga saman gadon cikin siyasa da yunkurin daukar wani abu kasa,_
_Nan take na mimmike kafafuwana tsaye kwance a saman gadon, kamar mai mika, na dinga sakin ihu tare da sambatu iri-iri kamar wata tsohuwar mahaukwacciya, Kaka dake yunkurin daukar bulala tana ganin haka dik ta firgice tana fadin "Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un, Talatu kinga fa aljannunta ne suka tashi," ba tare da ta tsaya jin ta bakin Gwaggo talatuwa ba, a rikice ta sake cewa, "dan Allah Talatu dauko ruwa a tofa mata addu'a",_
_A fusace Gwaggo Talatu ta mike tsaye tabar dakin, cike da mugun jin haushina kamar ta shake man wuya na dauke wuta dan tasan ba wasu Aljannai da gareni iskancine kawai da nake neman zube mata shi yanzu,_
_Tana barin dakin, ko 2seconds ba'ayi ba, sai ga ta, ta dawo dauke da ruwan a hannu, ta mikawa Kaka tare da ce ma Kaka "ba sai tayi addu'ar ba ita tayi ta tofa," A rikice Kaka ta amshi ruwan ta shiga yayyafa man a fuska,_
_Nan take na sauke wata nannauyar ajiyar zuciya daga nan kuma na koma yin baccin karya, a sannan Kaka taji hankalinta yadan kwanta sannan ta maida duban ta ga Gwaggo Talatu da ke shirin komawa wajen zamanta, ta ce "Talatu halan wannan wacce irin addu'ace haka mai karfi kika karanta mata, naga ina yayyafa mata ruwan ta koma bacci"__Cikin wani mugun murmushi wanda na kasa gane dalilin yin shi, dan tun lokacin da na ji Kaka ta sako wannan tambayar kai tsaye ba tare da wata lankwasa ba, nan take na ji cikina ya fara mirdawa tare da bude ijjiya ta guda ina kallon Gwaggo Talatuwa da wutsiyar ido dan jin amsar da zata bada da kyau, ta ce "Hmm addu'a dai ce irin wadda kowa ke yi, Allah dai ya kara sauki". Tana gama fadin hakan ta kai kwance a saman lafatattar katifarta, ta Kaka da Kakanni, ta kwanta dan ita dai tasan ba abin da ta karanta ma ruwan yanda suke tsararokan su haka ta kawo su,_
_Itama Kaka gyara kwancin ta tayi ta koma bacci, nima komawa bacci na nayi cike da hamdala ga Ubangiji domin nasan da Kaka ta gano karyar Aljannai ne nayi da bansan irin dukan da zan sha ba yau cikin silisinin daren nan,_
~~~_Wa she gari._
_Misalin Karfe 8:00am na falka daga nannauyan baccin da yayi man zuwan ba zata, ko da na tashi naga Gwaggo Talatuwa har tayi sharar dakin tayi wanke-wanke ta gama, har sun dawo Palour'n ita da Kaka suna tattauna wani batun, ba tare da na ce da su ko kala ba, na kamo hanya ta cike da izza Ina tafiya, kamar wata matar shugaban kasa, dan sai da na duba gadon yau ko'ina naga ko kadan banyi fitsarin kwance ba,_
_Ko da na iso bakin fanfon na cika buta ta fal da ruwa na fada toilet, bayan nayi lalurata na fito, na fara gabatar da alwala ta cikin kwanciyar hankali,_
_Ina gama Alwalla ta na dawo dakin dan gabatar da sallar subahim, har na kabbarta sallar na fara karatun fatiha, na ji Kaka na cewa "Ai in sha Allah Balkisu na dawowa daga Dubai zan kirata tazo ta dauke ta su koma can ABUJAr tare, dan na gaji wlhy",_
_Gwaggo Talatuwa ta ce " Shin Dubai ne suka tafi? ai na zata Ummurah ce suka je dan naga can ne wajen zuwan su",_
_Kaka ta ce "A'a kinsan Abir da Bikram a can suke karatu, shine suka je duba su, ko shekaran jiya da muka yi waya da ita, ta ce, "tana tunanin cikin satin nan zasu dawo saboda Fadil ya matsa masu da sai sun dawo gida, dan ya gaji da zaman kasar"._
_Haka dai su kayi ta tattauna batun su,_
_Ni kuma bidar ɗe nake na karkare sallar na tadda ɓalli, dan gaba dai jinina bai hadu da na diyan Mummy Balkisu ba, gwandama Yubra da Yumra muna dan shiri da su kadan-kadan, amma Ya Abir da Ya Bikram da Ya Fadil, da kuma Aunty Intisar ko kadan jinin mu bai hadu ba, dik muka zauna waje guda sai sun zalince ni, tun da ganin suke bani da mutumci kamar yanda Kaka take kokarin lalata man suna idan suka zo, Ta yi ta basu labarin abin da nake mata harda maganar Fitsarin kwance da nake yi, suyi ta yiman dariya suna tsokana ta, kuma idan nayi yunkurin ramawa, za kuga an zwage belt, ana dukana da shi kamar jaka........_
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*Be smart*
*Pls share*
![](https://img.wattpad.com/cover/215007905-288-k317588.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
'YAR BALLAJJA'U
FantasiaSai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...