P...41

312 49 9
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•BE-SMART•»•—*

*_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

              P...41
Wani k'ayataccen murmushi ne ya sakar man mai cike da ban sha'awa da burgewa kafin ya ce man "Me yasa kike fushi da mijinki ne.?" kukan da ke k'ok'arin fitoman ne tun d'azu na hana shi shine ya kub'ce man kai tsaye na ce mashi "Ni ka rabu dani.!" tare da ci gaba da kukan da nake, gameni ya yi da jikinshi yana bubbuga bayana a hankali yana ce man "Ya isa Babyna, bana jin dad'in wannan kukan da kike yi ko kina son ni ma na tayaki ne?.!" k'ok'arin kwace kaina na shiga yi ina tureshi daga jikina sai dai dik yanda na yi kamar ma ina k'ara mashi kwazo ne inda ya samu nasarar makani ga bangon wannan wajen sannan ya shiga k'ok'arin taddo fuskata sama ina kwacewa tare da ce  mashi "Ni bana so, ka k'yaleni.!" amma hakan bai sa ya ragaman ba, sai kwatsan naji fad'awar bakinshi a cikin nawa, yana  mai jifana da wani mahaukwacin kissing dinshi mai saurin saka mutuwar jiki, k'ok'arin kwace kaina na shiga yi da dik ilahirin k'arfin dake jikina sai dai hakan ya gagara, mun kusan shahe 30mins a hakan  ya fahimce kukan nawa ya tsaya dik da ban mayar mashi da martanin komai ba illa dukan bayanshi da nake ta famar yi da iya k'arfi na, sai da ya gama wahalar da ni sannan ya fitar da bakinshi cikin nawa tare da ce man "So kike ki k'arya bayan mijinki?.!"  ko kallonshi banyi ba balantana ya saka ran zan amsa mashi tambayarshi, da yaga alamun na janye fuskata daga ta shi cikin hanzari ina fitar da sautin wani walhaltaccen nishina na k'arfin hali tare da k'ok'arin kwace kaina daga rik'on da ya yi man, ya sake ce man "sai fa kin bani amsar tambayar da na yi maki sannan zan k'yaleki Malama.!" kuka na k'ara sakar mashi na ce "Kai da ka tab'a gaya man cewa, Ka tsaneni! to meye kuma kake nema a gareni?.!" waro manya manyan idanuwanshi ya yi a waje masu cike da burgewa da kuma d'aukar hankali cikin mugun son kawar da wannan zancen gefe ya ce man "Yau she aka yi haka bani da labari?.!"  cike da takaice na ce "Ni ma ban sani ba.!" na murgud'a mashi bakina gefe ina hararar iska, sakina ya yi daga rik'on da ya yi man d'auke da murmushinshi wanda ba lalle ba ne ka iya jin sautin fitarshi ba, ni kuwa dama abinda nake buk'ata kenan, yana sakina aguje nabar wannan wajen, inda shi ma ya biyo bayana ko da na juya da niyyar na k'ara ganin wannan wajen da muka baro, sai dai ban sake ganin wajen ba, gefen da Papa yake na duba wanda yana wajenda yake tun d'azu suna tattaunawa da DPO tare da su Malam nan dai suka yi sallama Papa ya zo muka shiga mota gabada'i muka bar wajen, sai da muka yi nisa sosai sannan muka b'ace, wanda tun lokacinda na shiga cikin motar ko Mummy Zulfa ban tsaya yi ma magana ba na fad'a jikinta ina rusa kuka, sai dai na kasa gane dalilin yin kukan har nake ji kamar bai da nasa ga abu biyu zuwa ukku, in ma kewar su Yumra ko kuma gaskiyar da ta bayyana ko kuma tunawa da su Kaka da nayi, Mummy Zulfa ce naji ta soma man magana da cewa  "Papa'nki ya tura wasu daga cikin sojojinmu su kamo wad'annan 'yan daban wad'anda suka yi wannan kisan wanda DPO ne ya neme wannan alfarmar da kanshi domin mu kanmu munso mu d'auki wani kwakkwaran mataki a kansu sai dai mu burinmu a kullum dik bai wuce muga an bi ma su Hajiya hakkinsu ta hanyar da ta dace ba, wadda ba sai mun shigo ciki ba domin mu burinmu a kullum shine a tabbatar da shari'ar gaskiya a tsakaninsu, kuma  dik da hakan zamu tashi tsaye ne ga wannan al-amarin sannan tsakanin CP da wannan Alk'alim idan suka ki fad'in gaskiya a gaban shari'ar dole zamu tursasasu su fad'i kamar yanda muka ma su Rafi'at sannan bayan komai ya lafa zamu mik'aki ne a hannun mijinki domin mu yanzu bamu da wani iko a da ke, shine yake da hakki a kanki, sannan ki kwantar da hankalinki ki fidda komai a cikin ranki ki rungume k'addara ki kuma rungume mijinki karki tuna da abinda ya faru da ke a baya ki ce da shi zaki yi aiki domin Allah ma yana son mai hak'uri ke dai ki saka a ranki biyayyace zaki yi ma Ubangiji da ya k'addara k'addararki a haka zata zo maki, sannan ina da tabbacin Abir zai kula da ke fiye da wadda ya maki a baya sannan zai maki rik'on da ba zaki tab'a danasanin zamanki tare da shin ba, sannan ki rik'e maraicinki karki yarda ki aikata wani abinda kika san haramci ne a gurin ubangiji kiyi biyayya ga mijinki Allah zai baki ladar yin hakan......!" haka dai tayi ta yi man nasiha wadda ta ratsa dikkanin ilahirin sassan jikina kuma sosai wadannan maganganun nata suka shiga kunnena kuma na d'auka, Papa dake gefe yana saurarenmu shi ma ya d'ora nashi akan nata, sosai na sha kuka har muka isa gida domin nasihohi ne suke man masu matuk'ar amfani. b'angaren DPO kuwa tun a wannan lokacin bayan ya koma office ya shiga hahhad'a bayanai kala-kala akan shiri'ar da za a gabatar wanda a wannan ranar ce suka samu nasarar kamo 'Yan-janbulo tare da taimakon aljannun Papa da ya taimaka masu da su wajen dank'arsu sannan dik wani sihirin dake da wadannan 'yan jan bulo'n sai da wadannan aljannan suka yi k'ok'arin fiddashi daga jikinsu sannan suka koma gida, cikin kwana guda DPO ya tattara bayanan komai ya tura koto, ba a wani b'ata lokaci ba aka saka k'arar nan da kwana hud'u masu zuwa tare da turawa CP da Alk'ali takardar sammaci, cikinsu ba wanda bai shiga cikin  wani matsanancin tashin hankali da wata matsananciyar girgiza da wannan al-amarin ba musamman ma CP da ya kasa tsaye ya kasa zaune yana nema ma kanshi mafita, ta wani fannin kuma Alk'ali ko kad'an hankalinshi bai kai mak'ura wajen tashi ba idan ya tuna da cewa shi ma Lawyer ne Lawyer kuma babba gabad'ai wanda hakan ke k'ara saka shi jin dik duniyarnan ba mai iyawa da shi sai Allah kuma zaiyi dik yanda zaiyi dan ganin ya kare kanshi daga zargin da ake tuhumarshi. 
         Kwana ukku yanzu da faruwar wannan al-amarin har ana gobe za a fara gabatar da shari'ar.  tun lokacin da muka dawo gida ko kad'an Mummy Zulfa bata barni na futa ba akan wani mahaukwacin gyaran da take man, kala ina kuka tare da k'in shan wasu abubuwa akan rashin jin dad'insu, wasu ma har ina amai mai had'e da zazzbi, har yanzu na fara sabawa da su kwanannan biyu kad'ai da nayi ina amfani da su sabida Mummy Zulfa ma kwanan nan har wani canza man ta dinga yi dan ko kad'an bata bari na futa kuma tak'i bani fuska wadda zai saka ko dan ganin haka ya sa nak'i bata had'in kai, Fatima takwarata kuwa dik lokacin da taga ina kuka ko ina hawaye ita ma sai tayi zaune tana yi sai Mummy Zulfa ta shiga lallashinmu dan d'an zamannan da nayi tare da su sosai muka yi wani mugun sabo da ita, dik da na so a bani ita na zauna tare da ita a gidan Yaya Abir, amma Papa fir ya k'i yarda da buk'ata ta sai dai ya yi man alk'awari da cewa, zata dinga zuwa akai-akai ina ganinta. abubuwa dai gasunan sai hamdala ga Ubangiji  dan sosai nake jin dad'in zamana tare da iyayena har nake jin kamar ba zan iya rabuwa da su ba, ta wani b'angare kuma soyayyar Ya Abir ce da k'aunarshi ke k'ok'arin rikitarman da  kwakwalwa wanda kusan dik bayan second1 ba aikin da nake ta famar yi sai na tunaninshi. Haka shi ma b'angarenshi sannan ya kud'urci kudurin bani kulawa mai d'aurewa tare da yi man dik wani abinda zai faranta raina ko da kuwa shi zai bak'anta nashi ran. A kullum dukansu abinda suke fata dik bai wuce lokacin gudanar da wannan shari'ar ya gabato ba dan wadannan kwana hud'un da aka saka jinsu suke tamkar shekara4, sai dai su ko kad'an ba shari'ar ce suke yi wa wannan yak'in ba sai dan zukatansu....................
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

'YAR BALLAJJA'UOù les histoires vivent. Découvrez maintenant