*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**P...12*
_Nima dariyar na tuntsure da ita kafin na ce "Allah ya kyauta" sannan na kama mata ta ida tattara littafan, mu kayi wajen sha'anin gaban mu._
~~~
_Misalin; 6:OOpm su Mummy Suka ida karkare aikin gabadai, sannan kowa ya nufe sashen shi, domin ya yi wanka ya shirya._
.....
_Wata Mahaukwacciyar doguwar riga ce dark blue (Ta kanti) , Mummy ta fiddoman daga cikin kayanta ta jidda mata farali a saman lafiyayyen gadon ta, sannan ta turani bathroom nayi wanka._
......
_Bayan nayi wankan Na fito, tayi man wata yar Simple Make up a fuska, sannan ta saka man wannan Rigar._
_Sosai Rigar ta kama jikina kamar sai da aka auna girman jikina kafin a dinka, sannan naga ta dauko wani dan karamin akwati ta bude._
_Nan take naga ta ciro wata jahilar sarka a cikinsa ta sakaman a wuya tare da yan kunnenta, hadi da saka man wasu Takalumma masu dan tsini kadan suma bulaluwa ne, sannan ta saka man wani dan karamin agogo blue da kuma zobe mai duwasun blue a cikin sa.__Sosai naga nayi wani irin masifaffen kyau dana duba makeken madubin dake cikin dakin, Na koma kamar wata yar karamar baby'n Turawa._
_Sai da ta gama shirya ni tsaf, sannan ta shiga shirya kanta cikin wata Matsiyaciyar Atamka Light Blue mai futifutin milk a cikinta wanda hakan yasa ta saka komai Milk itama, sannan taja hannuna muka sauko kasa._
....._Anan babban Palour'n dake ƙasa, muka cinma Yumra da Yubra, Suma sunyi irin shiga ta, komai namu kala guda._
_Sai Daddy dake gefe yana kallon agogon dake tsintsiyar hannunshi, shima sanye yake cikin wani tartsatstsen Yadi Light blue Zubin Turkey._
....._Muna isowa kusa da su, Naje har wajen Daddy na gaida shi, cikin far'a ya amsa man tare da ce man "Nayi kyau sosai" yana mai janyo hannuna na zauna gefe kusa da shi._
_Suma su Yumra sarkin rigima dake zaune gefe guda, a hanzarce suka taso suka yo gefena suka zauna tare da zolayata akan "Yau dik sunga na wani zama saliha, sai wani kame-kame nake kamar wadda bata da ruwa a jiki". Itama Mummy dariya abin ya bata kafin ta soma ce masu "Ya'isa hakanan, bata son dogun tsurutu." Ni dai sukukuku nake galalaaaa kamar wadda aka tsamo a cikin ramen kwata, na kasa ce masu Umm! Ko Um'um!, Tunanin halin da zan shiga yanzu kadai nake yi tare da nema ma kaina mafitar yanda zan daura ɗamarar yaki da dik wanda ya kuskura ya sake shigowa haraba ta, Muryar Daddy ce da naji yana cewa "Aje a kiranyo su Aunty Intisar Idan zasu je airport din, dan lokacin na gabatowa ". Yubra ce ta mike a hanzarce taje ta kiranyo su, koda ta isa wajen su, har sun shirya tsaf, suna shirin fitowa Palour'n._
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...