*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*End. on 24/8/2020*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*
*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_Assalamu Alaikum_*
My Frnds and Fns, Ina fatan dikkanku kuna cikin koshin lafiya Allah ya sa hakan Ameen.
Ina mai baku hak'uri da yanda wannan littafin ya zo maku, ku sani tun kafin na fara Typing d'in wannan buk na tsara yanda zan rubuta shi, to dan Allah kuyi hak'uri da shi a hakan, wad'anda ba su ji dad'in mutuwar su Mummy ba ku ma ina mai k'ara baku hak'uri da hakan, Allah ya ba mu baki d'ayanmu Ameen.
Ina matuk'ar alfahari da ku my fan's ku ji dad'inku a wannan page..!
*P...30.*
Ina kucce-kucce mai had'e da wani firgitaccen ihu, wad'annan Police suka d'aga ni sama na mik'e tsaye ba tare da na shirya ba suka saka ni gaba. Ammie ce ta shek'o aguje wajen da muke kamar wani k'asungumin Zaki, ta ci kwalar riga ta cikin wani irin yanayi na fita a cikin hayyaci take cewa "Yau sai na kashe 'yar banza.!" a take sauran Police d'in da ke wajen suka yi hanzarin rik'o ta suka samu nasarar dawo da ita baya suka yada ta a wajen wanda a dai-dai wannan lokacin ta durk'ushe k'asa tare da noce kanta kamar mai yin sujada, ta shiga zuba kukanta hinhinhin kamar wata k'aramar yarinya, inda cikin yin kukan take fad'in "ki yafe man Hajiya Balki! ki yafe man! dik laifi na ne, da ace tun lokacin da kika kirani a waya na kawo maki d'auki na kawo maki a wannan lokacin da dik wannan bak'in al-amarin bai faru ba.!" ko da jin wannan zancen nata 'Yan Jarida suka maido akalar aikinsu wajenta tare da yi mata caaaaa suna jefo mata tambayoyi a jajjere wad'anda ba mutum d'aya ne ke mata su ba. nan take ta mik'e tsaye ta share hawayen da ke sauko mata a saman fuska ta amshi Mic ga wani d'an jarida ta soma bayani kamar haka "tabbas wannan kisan babu tantama ko kuma shakku ga wadda ake zargin ta aikata shi.!" d'ai daga cikin 'yan-jarida'n ya ce "Ko zaki iya yi ma masu kallonmu da masu saurarenmu wani takamammen bayani dangane da abinda kika sani akan wannan kisan gillan da kika ce wadda ake zargi da aikata wannan aika-aikar ita ce take da alhakin aikata hakan! to ko zaki iya sanar da mu abinda aka yi mata wanda har ya harzuk'ata haka ta aikata abinda take ganin shi ne mafita a gare ta.?" Kai tsaye Ammie ta ce "wannan abin dik ba akan komai ba ne sai dan ta sanadiyyar Auren da aka yi mata da yaron gidan wanda yake suruki ne yanzu a waje na, kasancewar an d'aura auren ne ba tare da saninta ba yasa ta d'auke wannan mummunan matakin akansu!, sannan tun kafin ta kai ga yi masu wannan mummanan aika-aikar Hajiya Balki ta kira ni a waya misalin k'arfe 12:00am inda take gaya man cewa tana jin kamar wani mummunan abu na son faruwa da ita a daren jiya wanda har na shiga kwantar mata da hankali, inda na nuna mata ba komai ba ne wannan abin da take ji kawai dai rud'in Shaid'an ne sannan na d'an bata shawara da ta ci gaba da yin addu'a in sha Allah ko ma mene ne Allah zai mata maganinshi.!" cikin kwarin gwiwa wannan D'an-jaridan ya sake cewa "ko mene ne hujjarki na d'orawa wadda ake zargi alhakin yin kisan? shin lokacin da kuka yi wayar ko ta gaya maki wannan yarinyar na bid'ar salwantar da rayuwarsu akan hakan?, shin ita wadda ake zargin da aikata kisan tana shaye-shaye ne ko kuma tana da tab'in hankali ne?.!" cikin mird'awar ciki Ammie ta had'iye yawun k'arfin hali cikin halin damuwa ta soma cewa "Eh tana shaye-shaye wani bin domin ko lokacind.........!" Abba ne ya yi hanzarin datse mata kuzari wajen jawota da hanzari dan dakatar da abinda take k'ok'arin aikatawa wanda hakan ko kad'an bai ma 'yan jaridar dad'i ba, aguje suka biyo bayansu da niyyar jin k'arshen labarin, sai dai kan su ida k'arasawa wajen 'Yan sanda sun taka masu burki a dai-dai lokacinda aka d'auko Ni giririri kamar Tunkiyar da za'a sayar, inda kuma d'ai daga cikin 'Yan sandan wanda nake ganin kamar shi ne babba a cikinsu ya buk'ace da Ammie ta biyo su Office domin jin kwakkwaran bayani akan abinda ta sani. sai dai wani abu! har muka bar gidan banga mutum ko guda a cikin su Aunty Intisar ba dukansu basa gidan harda su Yumra, duka wad'anda ke wajen bak'in fuska ne a gare ni dan zan iya cewa Ammie ce kad'ai sai Khairat da tun lokacin da Police d'in suka fito da ni waje take jifa na da wani irin banzan murmushinta mai cike da tuhuma, sai kuma Abba dake firgice dik ya wani zare, kafin ka ce me? K'asa ta shaida kowa ya shaida mutuwar babban Senator d'innan dake cikin kungiyar majalissar dattawa da cewa surukarshi wadda aka d'aurawa aure jiya da babban D'anshi na farko, tabi dare ta kashe shi shi da matarshi da kuma mahaifiyar matarshi a bisa Auren da suka yi mata ba tare da amincewarta ba!" Inda ta ko ina an baza faifen video Ammie wanda take yin wannan bayanin, wanda mutane kusan 99% sunyi Allah wadai da hali na 1% kad'ai ne ke tausaya man wad'anda suke ganin abin kamar k'age ne aka man. muna isa Police station aka yi rubuce-rubucen da ake tare da tattara dik wasu bayanan da Ammie ta k'ara masu da su suka k'ara da wanda suke da su aka aje a matsayin shaida kwakkwara wadda za'a gabatar da ita a Koto, ba a wani b'ata lokaci ba aka kawo takardun binciken da aka yi na Asibiti inda gabad'ai shaidun sun tabbatar da cewa ni ce mai laifin. wanda hakan yasa Abba ya yi hayar wani babban Lawyer wanda gwani ne kuma jajirtacce ta fannin aikinshi, dan ya kare wad'anda suke k'ara. Ni kam bana da wanda zai tsaya man sai Allah domin ban san kowa ba kuma ban san komai ba. bayan an gama yin dik wani kwakkwaran binciken da ya kamata ayi sannan aka dawo waje na, inda sunyi da k'arya sunyi da gaskiya amma na kasa ce masu ko k'ala, dan bakin maganar ma na neme shi na rasa, bayan wani d'an k'ank'anen lokaci aka tura case d'in Koto, cikin minti30 Alkali ya yi accepted d'in k'arar inda ya bada izinin nan da kwanaki ukku masu zuwa za a fara zaman kotu.. sai da komai ya d'an lafa sannan Ammie ta koma gida ta sake shiryawa dan gidanta ake saka ran za ayi zaman makoki domin gidansu Mummy kowa babu a ciki. shi kuma Abba yana wajen shirya su Daddy cikin suturansu ta gaskiya, sai dai an saka lokacin Zana'izarsu ne bayan an dawo daga sallar Azzahar dai-dai mutanen dake nesa sun ida k'arasowa. Ammie na shigowa gida ita da Khairat suka buga wani raki'in ihu na matuk'ar farin ciki harda tafawa sannan ta ciro wayarta dake cikin jaka ta kira Hajiya Maryam bayan ta d'aga cike da farin ciki Ammie ta ce mata , "aiki ya kammala k'awar arziki.!" cike da wani hamshak'in farin ciki Hajiya Mayam ta ce "dama na sani ai domin mutanen basu tab'a wasa da aikinsu! amma d'an shata man naji yanda aka yi tukun kafin na zo dan wlhy har na matsu banji ba.!" Ammie ta ce "hhh ai ni wlhy Maryam kin gama man komai a duniyarnan sai dai na ce Allah ya biya ki ya kuma k'ara maki kaifin sani game da ko wanne irin makircin da ya gagara ki gano shi.!" ga baki d'ayansu dariya suka saka kafin su amsa da "Ameen" sannan Ammie ta k'ara da ce mata "kin san wani abu kuwa? jiya ina bacci tunda subahim babbar munafukarnan wadda tayo gadon munafurci kamar mahaifiyarta wato Intisar, ta tada mu daga bacci da kiran wayarta, Ni kuma ina ganin kiran dama na san abinda zata fad'a man, na d'auki wayar da sallama! aiko bata ma tsaya amsa sallama ta ba cikin wani irin dabirtaccen yanayi take ce man, Ammie dan Allah kuzo ku taimaka muna Fatima ta kashe su Mummy, aiko da jin hakan bansan lokacin da na kece da wata mahaukwacciyar dariya ba wadda take kamar kuka harda su shashshek'ar kukan kamar da gaske, ba tare da b'ata lokaci ba na yanke kiran cikin wata mugunyar damuwa na shiga bubbugar Abban Khairat dake bacci, a take ya mik'e zaune firgigit ya shiga tambaya ta abinda ke faruwa, cikin kuka na shiga labarta ma shi komai, ina gamawa ban tsaya jiran abinda zai ce ba na mik'e tsaye a hanzarce na lalabo zane na na aza a saman rigar bacci ta sannan na saka zumdumemen hijab d'ina, Kai sai ka ce da gaske, a rud'e naje na tadda Khairat ko da muka fito waje shi ma har ya shirya ya fito, sai da muka fara zuwa gidan muka duba halin da ake ciki sannan muka wuce Police-station muka zo da 'Yan sanda tare da Doctors guda hud'u! Ni dai ban san yanda aka yi 'Yan Jarida suka zo ba sai ganinsu kawai muka yi sun fad'o gidan, ko da Doctors d'in suka yi binciken da suke suka gano basa numfashi dik da dai mu ma munga zahiri, aiko nan take dikkanin yaransu suka fara bori sai sun gudu a kamo su kamar wasu k'asungumen mahaukwata daga karshe dai sai da aka daddanne su da k'arfin aka yi masu allurar bacci sannan aka samu abin ya d'an lafa! bayan an kai yaran gabad'ai Asibitin ne Police d'in suka shiga jibgar shegiyar kamar Allah ya aiko su dik suka farfasa mata jiki ta ko ina sai da taji matsi sannan ta farfad'o daga nannauyan baccin da take.....!" dariya sosai Hajiya Maryam ta sha kafin ta katse mata hanzari da cewa "kai ashe dai wannan abin ya yi k'amari Ammie'n Khairat, ina ma ace nima ina kusa a wannan lokacin wlhy da na sha dariya, Allah dai yasa karsu kashe ta mukan su kai mu su baro.!" sai da Ammie ta fara kecewa da wata irin arniyar dariya marar kan gado sannan ta ce "ai ba za ma su kasheta d'in ba dan yanzu haka maganar da nake maki ba mu baro wajen ba sai da Abban Khairat ya yi tsaye aka tura case d'in a koto kuma nan da nan Alk'ali ya k'arb'i k'arar, yanzu ma maganar da nake maki har an saka ranar da za a fara yin shari'ar nan da kwana ukku masu zuwa.!" cikin matuk'ar farin ciki Hajiya Maryam ta ce "ki ce dai mu ma zamu je mu sha kallo.!" Ammie ta ce "sosai ma dan ke ma kiji yanda shari'at zata kaya ba sai na tsaya baki labari ba, kin ma san wani abu kuwa?.!" Maryam ta ce "a'a ina saurarenki.!" Ammie ta ce "Ni har an sakaya sunana a cikin jerin sunayen masu bada shaida.!" cikin wata dariya Hajiya Maryam ta ce "Amma dai gaskiya baki kashe wuta wlhy.!" Ammie ta ce "taya ko zan kashe wutar Ni da ke son kullum ta k'ara ruruwa indai akan buk'ata ta ce.!" Maryam ta ce "sai yanzu na fara jin zance ta waje na! ke dik ma ba wannan ba, wad'anda suka yi mana aikin fa sun kira ni akan suna buk'atar ganinmu dan mu kawo masu kud'ad'ensu!" cike da wata annashuwar da ke damun Ammie ta ce "haba dai? kice 'yan albarkan sun kira ki.!" Maryam ta ce "ba dole ba, ai sabida kud'insu dake hannunmu ne.!" Ammie ta ce "ba damuwa amma sun gaya maki ko nawa zamu ba su.!" Maryam ta ce "eh sun gayaman sai dai kud'in ba ma wasu masu yawa ba ne.!" Ammie ta ce "kamar nawa kenan?." kai tsaye ta ce mata "3M ne kawai." ba tare da damuwar komai a rai ba Ammie ta ce "to ba damuwa ya kamata muje yanzu mukai masu kafin a fara taruwa a gidan sabida gudun bakin jama'a wad'anda kana bacci suna maka hansari.!" Maryam ta ce "ke ma dai kya fad'a! bara na shirya yanzu na biyo maki sai mu tafi d'in.!" Ammie ta ce "to ba damuwa sai kin zo.!" daga haka suka yanke kiran kowaccensu ta shiga yin harkar da ke gabanta. a Asibitin kuwa sai misalin k'arfe 1:30pm su Yumra suka falka da wani matsanancin kuka na rashin iyayensu da suka yi wanda har yanzu sun kasa gasgata abin gaskiya ne ko k'arya, dan har su na ji ina ma ace mafalki ne suke wanda suke tauye da yinshi. b'angaren su Ya Abir kuwa bayan ya farfad'o ya tashi da wani matsanancin ciwon kai da kuma mugunyar fad'uwar gaba da yake jin tana taso ma shi babu dalili, dik da ba a yi niyyar sanar da su abinda ke faruwa ba da farko domin a cewar Doctors kar hankalinsu ya k'ara tashi bisa ga wanda suke ciki a yanzu sai dai hakan ya cutura domin ko da wasa Abba bai bari aka rufe masu zancen ba wanda shi da kanshi ya je ya sanar da su abinda ke faruwa wanda hakan ya k'ara janyo ma Ya Fadil wata gagarumar matsala a zuciya wanda numfashin shi ma ke bid'ar d'aukewa afujajun. Ya Abir kuwa ko da ya ji hakan yaji dik duniya ba abinda ke mashi dad'i sama da yaga ya d'auki fansar abinda aka yi ma iyayensu, nan take ya neme kasalar da yake ji a jikinshi ya rasa sai a lokacin ma yaji wani k'arfin hali mai cike da d'aukar fansa ya fara ziyartarshi kai tsaye ya shiga d'ed'd'ebe dik wasu nak'urorin dake d'ahe a jikinshi ba tare da ya tsaya b'atawa kanshi lokaci na jiran Doctors ba. security d'in dake kula da shi ko da suka ji an bud'e k'ofar d'akin da k'arfi ya sa dik suka mimmik'e tsaye da hanzari cike da mamaki suke kallonshi, nan dai d'ai daga cikinsu ya yi k'arfin halin cewa "Sir.....sir kana buk'atar wani abu ne, muje mu sayo maka.!" a takaice ya ce "bana buk'atar komai.!" ya ce "To sir ya kamata kaje ka futa kafin Doctors d'in su k'araso.!" cike da kallon rainin hankali ya dubi wannan security d'in ya ce "Shin a kwai wanda ya isa ya hanani zuwa wajen zana'izar iyayena ne ko me?.!" kai kawai wannan security'n ya iya girgiza mashi alamun "a'a.!" sannan Ya Abir ya ce "To ku kaini can.!" ba tare da b'ata lokaci ba ya soma tafiya, security'n na biye da shi a baya, sai da ya kawo daf da motar gidansu sannan aka bud'e mashi marfi ya shiga su ma suka shiga ciki daganan suka tayas. bayan Hajiya Maryam ta shirya ta biyo ta d'auki Ammie suka bar layin a hanzarce suka nufi wajen 'Yan-jan-bulo wanda Hajiya Maryam da kanta ta ciro kud'in ta basu da sunan bayan komai ya lafa Ammie zata dawo mata da kud'inta. K'arfe 2:10pm wajen zana'izarsu Daddy ya cika mik'il da d'an mutum kamar wajenda ake gudanar da sallar ED a wani gagarumin Masallaci, bayan an sallace su gabad'ai aka yi masu rakkiya izuwa makwancinsu na gaskiya. Ko da aka dawo daga wajen kai su direct Ya Abir ya wuce police-station d'in da aka kai ni, ba tare da b'ata lokaci ba aka fito mashi da ni wanda har a cikin rai na naji hankali na ya kwanta da naji ance shi ke son gani na, waje na musamman aka ware muna anan cikin Police-station d'in, zama nayi a wajen da aka nuna man har sannan ban iya taddo kaina na kalle shi ba, kai tsaye na ji hawaye masu zafin gaske sun faro gangaro man a saman kunce, jin shiru ya sa ni tadda kaina sama na kalle shi sai dai a hanzarce na sake maida kaina k'asa ganin wani banzan kallon da yake bi na da shi mai cike da tsana zallarta wanda hakan ya sa gabana k'ara tuntsirewa sama ya fad'i kafin na bud'e baki na mashi magana tuni naji sauk'ar wasu zafafan maruka guda biyu a jajjere a saman yakutacciyar fuska ta wadda dik Police sun gama faffasata da kulki, a fusace naji ya soma kiran sunana da k'arfi wanda sai da na taddo kaina sama against na k'ara kallonshi kafin na sake d'auke idona ga kallonshi, ya ce "Ashe so na zama k'iyayya har haka Fatima.! me na maki Fatima? Na ce, me na maki ne haka da har zaki saka ma iyaye na da wannan mummunan abin da kika aikata masu? shin kin manta da halaccin da muka maki ne?, mun sawo ki a jikinmu a matsayinki na d'ai daga cikin danginmu kuma 'yar uwa ta jini a gare mu amma Fatima dik kin manta?, da haka zaki saka ma wad'anda basu ji ba basu gani ba? wad'anda cin ki da shan ki dik yana a kansu, shin kin tab'a tunani dai-dai da second d'aya akan irin k'aunar da muke nuna maki Fatima? mun sawoki a jiki, mun d'auke ki tamkar wadda muka fito ciki d'aya da ita ba wani banbancin da muke nunawa tsakaninki da su Yumra har ba ma k'aunar b'acin ranki ko kad'an musamman Mummy da ko fushinki bata son gani dik ta dalilin k'aunar da take maki, haka ma Daddy! gaskiya kin bani kunya kuma kin fidda dik wata alak'ar dake tsakanina dake a cikin rayuwa ta, wlhy na tsane ki, irin tsanar da nake jin na fi k'aunar alade akanki, wlhy ko kad'an bana son na sake ganinki Fatima.!" cikin wani matsanancin kuka mai had'e da tawakkali na soma cewa "Ya Abir dan Allah ka yi hak'ur....!" a tsawace ya dakatar da ni wanda sai da naji jiyojin jikina sun kusa katsewa akan tsoro domin ban tab'a ganinshi cikin irin wannan yanayin ba, ya ce "Hak'uri!? hak'uri kuma Fatima? wanne irin hak'uri ne wannan?.!" ban iya bashi amsa ba illa kallon da nake mashi mai cike da damuwa ina ci gaba da kukan da nake, Sai da ya fitar da sautin wani nannauyan murmushi mai cike da k'unar zuciya sannan ya ce "ai ban hak'uri ba naki ba ne Fatima! ban hak'urin namu ne!, dan ba ke ya kamata ki bamu hak'uri ba, mu ne ya kamata mu baki hak'uri a bisa kuskuren janyoki a jikinmu da muka yi har kika saka muna da hakan, ban tab'a nadamar sananki a rayuwa ta ba Fatima sai yau, ban tab'a nadamar kasancewarki 'yar uwa a gare mu ba Fatima sai yau, sanadiyyar haliccin da muka nuna maki da kuma k'aunar da muke maki ne ya sa rayukka da dama suka salwanta kuma dik ta sanadiyyarki! Ni yanzu ba abinda zan iya cewa da ke, sai dai ki jira ranar da za a yanke maki hukuncin da ya dace da ke, butulu kawai.!" yana gama fad'in hakan ya tashi ya bar wajen a fusace. ban san lokacin da na game kai da gwiwowi ba na shiga zuba kuka cikin kururuwa tare da ambaton sunayen Ubangiji da ya taimake rayuwata ya kawo man d'auki a cikin wannan sark'ak'k'iyar da aka jefa ni ciki, a haka Police d'in dake kula da ni ta zo ta same ni, a takaice ta fincike ni da k'arfi tayi cikin cell da ni ta jefa ni ciki sai da goshi na ya buge bangon d'akin sannan ta jawo k'ofar da k'arfi ta rufe da key. Ko 2mins ba a yi ba, wani matashin saurayi wanda shekarunsa ba zasu haura 35years ba, ya zo Police-Station d'in da neman izinin ganina, bayan an fito mashi da ni ne, yake sanar da ni matsayinshi na Lawyer'n government wanda yake a shirye da yaga ya kare ni idan har na bashi had'in kai, ta yanda ya b'ullo man ne ya sa hankali na ya d'an kwanta har naji na gamsu da bayananshi, sai a sannan na soma yi ma wani mutum bayani a kan abinda na sani kuma na gani, sosai shi ma naga ya girgiza da jin wannan al-amarin, ba tare da b'ata lokaci ba, ya yi sallama da ni ya tashi ya yi tafiyarshi, sannan wannan Police d'in ta sake maida ni cikin cell. b'angaren Ya Abir kuwa tun lokacin da ya baro waje na ya ji hankalinshi ya kasa yarda da abinda aka sanar mashi, tafiya yake saman hanya a hankali yana tunane-tunane a cikin ranshi yake cewa "anya nayi ma wannan yarinyar adalci kuwa? anya ba zan sassauta fushina akanta na gano yanda bakin zaren ya ke ba? kamar Fatima ace har ta iya kisan mutum ukku kuma dik a lokaci guda, wadda k'yank'yanso ma abin tsoro ne a wajenta?" nan take kuma ya ji wata zuciya ta soma ce mashi "Hmm karka tab'a yarda da wannan tatsuniyar da zuciyarka ke k'ok'arin yi maka gizau da ita, Idan har ba ita ke da alhakin aikata hakan ba to wane ne? bacin dik wasu kwararan shaidun da aka samu sun tabbatar da cewa ita ce mai laifin!, shin ko kana tantama da abinda kaji kuma ka gani ne.?!" wani d'an siririn tsaki ne ya ja kafin a fili ya ce "ko ma dai mene ne ba zan tab'a k'asa a gwiwa ba har sai naga an tabbatar da adalci a cikin wannan shari'ar da za a yi.!" ya k'ark'are maganar ne a dai-dai lokacin da ya kawo daf da motarshi dake parke a cikin parking space, ya zagaya ya shiga. Har wannan Police d'in tabar wajen ban tsayar da kukan da nake yi ba, sai kalmar "Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un.!" nake nanatawa tare da tunanin abinda ya rinjaye zuciyata da har zata mantar da ni da tawakkali ga Ubangiji domin na san shi kad'ai ne shaida ta kuma shi kad'ai ne zai iya fiddani daga cikin wannan k'angin na rayuwa, hannu na saka na share hawaye na tare da tsayar da kukan da nake ina tunanin maganganun da Ya Abir ya yi man. a b'angaren Ammie kuwa gida ya cika mak'il da 'yan zaman makoki sai famar hurar hanci take tana yakushe fuska sabida ganin yawan taron da aka yi a gidan wanda har take jin kamar ta fice daga gidan ta basu waje domin dik yanda tayi tunanin abin ya wuce nan kasancewar ita mace ce marar son bak'i da kuma rashin son cinkoson da ba na ta ba. su Intisar kuwa sai wajejen k'arfe 3 aka dawo da su gidan Ammie tare da akwatunansu na kayan tufafinsu wanda hakan ya tabbatar mata da cewa a wajenta za su ci gaba da zama dik da ita ko kad'an bata so hakan ba, sai dai ta danganta alhakin aikata hakan ne ga mijinta wanda take jiraye da shi a halin yanzu. b'angaren Ya Fadil kuwa, da k'yar da walahaula aka samu nasarar shawo kan matsalar da take damunshi sai dai ko da hakan an kasa sallamarshi a Asibitin a cewarsu sai yanda hali ya yi. Bayan kwana biyu, Hajiya Maryam ce zaune a cikin makeken Palour'n Ammie inda Ammie ke ce mata "Ai ni wannan zalumcin ko kad'an wlhy bai min ba, shari'ar nan kad'ai nake jiran a gama na tadda b'alli dan ba zan tab'a yarda da hakan ba.!" Hajiya Maryam ta ce "Gaskiya kam, abin dai kam ya yi yawa! Yo da me zaki ji ne? da kukan da suke maki kullum ko da d'awainiyarsu, ace abu yanzu kusan kwana biyu da faruwarshi amma sun kasa hak'uri da shi?." Ammie ta ce "Ba iskanci ba ne, yanzu a ce kamar su Yumra har sai an tsaya ana lallashinsu kullum kamar k'ananan yara, haka ita ma waccen ballagazar 'yar'iska marar amfani Intisar, kullum abin ya k'i ci ya k'i canyewa?, kuma dik wannan bak'in bala'in ba kowa ne ya ja man shi ba wlhy sai Abban Khairat! ni da ma barinsu ya yi a gidan ubansu wlhy da yafi, dan wlhy fitina dai kam ta man yawa gaskiya, shin ni yau da me ma zanji ne? kwakwatar 'yan zaman makokin ko ta su, Maryam?.!" ta k'ark'are maganar ne tana mai kallon Hajiya Maryam dake k'ok'arin numfasawa kafin ta ce mata "Ni fa wannan matsalar ganin nake dik ba laifin kowa ba ne illa taki, tun farko me ya sa baki nuna mashi b'acin ranki game da hakan ba.!" a raunane Ammie ta ce "har yanzu fa yak'i dawowa gida balle ya ga halin da muke ciki!." mamaki shimfid'e a fuskar Hajiya Maryam, ta ce "Bai dawo gida ba shin? To yana ina?." Ammie ta ce "Yana can tare da bak'inshi a sabon gidan da ya gina.!" kai tsaye Hajiya Maryam ta ce "Anya Ammie'n Khairat kin yi amfani da wannan kullin maganin da boka ya baki kuwa?.!" sai da Ammie ta d'anyi jugun kamar ba zata ce komai ba sannan ta ce "Wlhy Maryam na yi dik yanda ya ce na yi.!" Maryam ta ce "to ko kinga canji ga abin kuwa?." Ammie ta ce "Ina ko naga wani canjin bacin na gaya maki yanzu ko gida ya daina bacci dan karen kanshi.!" Maryam ta ce "A wajen Abir fa?." Ammie ta ce "Eh shi kam an fara samun canji sosai a wajenshi domin yanzu kusan kullum sai ya kira baby da dare yana fad'a mata yanzu babu abinda yake muradin gani sama da ya ga an yankewa Fatima hukuncin abnda ta aikata ma iyayensu.!" dariya kad'an Hajiya Maryam ta yi, ko shi kuwa ba dan ta so ba sai dan kada 'yan zaman makoki dake Palour zazzaune su ji su, sannan ta ce "ki kwantar da hankalinki k'awa ta! domin Ina da tabbacin Abba'n Khairat ma ya kamu dan ni tun lokacin da kika gaya man shi da kanshi ya saka k'arar Fatima a kotu ba tare da ya jira an gama binciken da ake yi ba tukun, na san shi ma ya dad'e da kamuwa.!" cike da far'a Ammie ta kalle ta, ta ce "Allah ko k'awar arziki.?" Maryam ta ce "ke baki ga alamar hakan ba halan?.!" Ammie ta ce "Gaskiya kuma haka ne wlhy.!" haka dai suka yi ta firarsu dik cikin nishad'i mai cike da b'adda kama, dik wanda ya shigo d'akin ya yi sallama da Ammie akan zai koma mazauninshi a haka yake isko su kuma yake barinsu.!" wa she gari, misalin k'arfe tara9:00am muka halarta a babbar koton dake cikin garin Abuja, kafin mu shiga cikin kotun 'yan-jarida tare da sauran mutane'n dake wajen dik suka yo kanmu kowa so yake ya ga yanda nake sai dai ko kad'an Police d'in ba su basu wannan damar ba, anan muka cinma jami'an gidan-yari tsatstsaye dik sun kewaye wajen wanda hakan ya k'ara bada damar shiga da ni cikin koto d'in, wanda hakan ya sa dubun mutane biyo bayanmu da hanzari ba tare da wata-wata ba aka cika koto'n mak'il har wajen da za a zauna ya buwaya, Alkali na fitowa daga cikin d'akin da yake kowa ya mik'e tsaye, sai da ya zauna sannan kowa ya samu damar maka masukkanshi ga wajen zaman, na tsaye kuma suka yi tsaye, nan take aka shiga gabatar da k'ararmu, kai tsaye Alk'ali ya neme gani na, na je na tsaya a wajen da aka ware ma irinmu tare da taimakon d'ai daga cikin Police d'in da suka kawo ni wajen wanda hakan ya sa gabad'ai idanuwan mutane suka yo kai na, ta b'angaren guda kuma 'yan-jarida ne suka fara gudanar da aikinsu inda kai tsaye suka shiga d'aukar fotuna ta ko ina tare da bidiyo suna yad'awa duniya, nan take aka soma shari'a bayan Lawyers sun gama gabatar da kansu, d'ai daga cikin Lawyers d'in Abba ya taso yana man wasu tambayoyi amma ban iya bashi amsa ba kamar wadda aka rik'e ma baki, haka dai har ya gama ya koma mazauninshi inda kuma wani lawyer ya mik'e tsaye ya k'ara gabatar da kanshi a matsayin wanda yake kare wadda ake k'ara, ba tare da b'ata lokaci ba ya yo kaina inda shi ma ya soma tambaya ta abinda ya faru a wannan ranar, kukan da nake yi ne ya soma cin k'arfi na har na kasa tsayar da shi, wajen ya yi gummm kowa yana saka ran jin ta baki na, sai da wannan Lawyer'n ya k'ara maimaita mini tambayar a sannan naji wani k'arfin hali ya fara zuwa man, cikin wani matsanancin kuka nake cewa "Ban san yanda aka yi ba, kawai dai na falka ne na ga Police gewaye da ni.!" aiko da jin hakan mutanen dake cikin koto'n suka shiga cece-kuce wanda har baka ma gane abinda suke fad'a akai.!" daganan Alk'ali ya bada order aka yi tsit kafin lawyer'n su Abba ya mik'e tsaya ya jefo maganarshi da cewa "Ya mai girma mai shari'a ya kamata a dakatar da wannan tatsuniyar da Lawyer government ke k'ok'arin aikatawa da wadda yake karewa, domin dik wasu hujjoji da kwararan shaidun da muka samo sun nuna cewa wadda ake zargi da aikata Kisan babu tantama ita ce da alhakin aikata wannan kisangilar, Ni a gani na wannan wasar kwaikwaiyon zai b'atawa koto lokaci ne kawai.!" aiko daganan ce-ce-kuce ya soma b'arkewa a tsakanin lawyer's d'in, kowa bid'ar yake ya nuna kwarewarshi ta fannin aikinshi, nan dai Alk'ali ya dakatar da su inda ya buk'ace shaidu da su fito su gabatar da abinda suka sani, Ammie ce ta farko kafin 'yan-sanda da Dctors d'in da suka yi binciken gawawwakin, bayan komai ya kammala ne Alk'ali ya tattara bayanan gabad'ai ya aje gefe inda kai tsaye ya bada umarnin hutun awa1 sannan a dawo zama na biyu, daganan kowa ya tashi ya koma waje bayan Jami'an gidan-yari sun zo sun d'auke ni giririri suka aje a cikin wani d'aki da bashi da mararraba da kogo. Ammie ce tsaye ita da Hajiya Maryam tare da Khairat had'i da su Intisar da su Yumra dake wani gefe zaune suna jimamen abin domin har yanzu ganin abin suke tamkar tatsuniya, sai kuma sauran mutane. Bayan an dawo hutun awa d'ayan da ake je kowa ya zauna ya natsu baka jin k'arar komai a wajen sai sautin kuka na dake fita kad'an-kad'an wanda tun kan mu shigo koton nake yinshi har yanzu ya kasa tsayawa, sai da Alk'ali ya fara gyaran murya tukunna kafin ya ce "A bisa wani kwakkwaran nazari da kuma bincike akan wannan case da aka gabatar a cikin wannan court mai adalci wanda koto ta kama Fatima Almustapha da hannu dumu-dumu da aikata Kisan-kai ga wad'anda suke tamkar iyaye ne a wajenta wanda a bisa kwararan hujjojin da aka gabatar a wannan koto mai adalci tayi duba da su Inda ta yankema Fatima Almustapha hukuncin d'aurin rai da rai ta hanyar rataya ba tare da d'aukaka k'ara ba..!" Ko da jin hakan ban san lokacin da na sake wani irin firgitaccen ihu ba, kafin Jami'an gidan-yari su kai ga k'arasowa wajen da nake tuni na sulale daga wajen na fad'i kwance sumammiya, Alk'ali na gama yanke hukuncinshi ya tashi ya bar wajen cikin hanzari, wanda mafi yawancin mutanen da ke wajen sai da suka zubar da kwalla akan tausayi na inda kuma wasu ke fad'in "Alhmdu lillah Allah mun gode maka" bayan an fito cikin height court din gabad'ai kowa ya sani inda dare ya yi mashi sannan tako ina an baza hukuncin da aka yanke man a kafafen sada zumunta har ma a wasu wajajen. Ko da su Intisar suka fito waje ba su ga su Ammie ba sunyi masu ko k'asa ko bisa, nan dai Khairat da taga alamun kwakkwanton su Aunty Intisar na son ya yi yawa, sabida gudun kar hankalinsu ya gano inda bakin zaren yake ta shiga shashartar da su ta hanyar jan hankalinsu suka koma gida direct. Ammie ce zaune a cikin Office d'in Alk'ali tare da Hajiya Maryam, inda Ammie ta soma cewa "Yallab'ai mun gode fa da wannan hukuncin da ka zautar gaskiya ya yi dai-dai fatanmu dai shine a gaggauta yanke mata hukuncin domin ba ma son a yi tsaiko cikin wannan al'amarin har wasu hukumomi su kai ga sako bakunansu a ciki.!" Murmushi mai cike da k'ayatarwa Alk'ali ya yi kafin ya ce "ai ko kad'an karku damar da kanku akan wannan abin domin ko da ba ku biya ni ba wannan hukuncin ne ya dace da ita amma fa a bad'ilance domin kuwa a zahirance sai dai a wawwake ta ta sanadiyyar yanda aka rik'a wuk'ar lokacin da za a aikata b'arnan ba hakan aka yi aiki da ita ba, kunga ko wannan kad'ai yana iya zama shaidar da zai bada tabbacin ba ita ke da alhakin aikata hakan ba domin bincike mai tsawo za a yi har a gano yanda kan wannan al'amarin yake, sannan ko Doctors d'in da suka kula da wannan case tunaninsu ba zaya tab'a ganar da su wannan abin da nayi ba domin kwata-kwata hankalinsu ba zai kai ga wannan ba.!" cike da farin ciki suka shiga yi mashi godiya kafin su tashi su bar wajen cikin wani salo na tako dan kar wani ya kama su. Abba da Ya Abir kuwa ana gama shari'ar bayan an yanke hukunci suka komawarsu gida ba tare da sun tsaya magana da kowa ba ko wannensu abinda ke damunshi kad'ai ya ishe shi. Su Ammie na baro Koto'n suka nufe gidan-yarin da aka kai Ni, ba su sha wata wahala ba wajen neman Office d'in CPS (Comptroller Prison Service) inda kai tsaye aka yi masu rakkiya har izuwa office d'inshi, bayan sun isa Office d'in aka basu izinin shiga ciki, a saman kujerarshi ta mulki suka cinmashi zaune yana rubuce-rubuce a wani file, kujerun alfarmar da ke wajen ya masu nuni da su zauna kafin ya tambaye abinda ke tafe da su, murmushi k'arfin hali ne ya fara kub'cema Ammie domin bata ga alamun wasa ko kad'an ga wannan CP ba, tambayar da suka ji ya yi masu ne ta katse masu hanzari wajen ci gaba da abinda suke k'ok'arin yi, inda kai tsaye suka ji ya ce masu "Me ke tafe da ku?.!" sai da Ammie ta d'an had'iye yawun k'arfin hali kafin ta ce "Da ma yallab'ai wani aiki ne muke son ka taimaka muna da shi.!" shiru kawai ya yi yana saurarenta, ta k'ara da cewa "Aikin mai wahala ne sai dai ta wata fuskar ba mai wahala ba ne a wajenka, kuma a shirye muke da ko nawa ne mu biya indai aikin ya kammala kuma ya yi kyau kamar yanda muke fatan shi.!" Jin ya kasa cewa da su ko uffan yana binsu da wani mugun kallo yasa hankalinsu ya dad'a tashi, sai can bayan 20seconds ya katse shirun da cewa "Wanne irin aiki ne wannan?." murmushi Hajiya Maryam ta yi kafin ta ce "Yarinyar da aka kawo maku yau Fatima Almustapha wadda aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya a yau d'innan muke son ka ba mu.!" a tsawa ce ya ce "Ban gane ba.!" cikin mugunyar rud'ewa Ammie ta ce "Yau mun shiga ukku assirin mu ya tonu Maryam.!" dubanta kawai Maryam ta yi da kyau kafin ta ciro wata takarda ta cheek a cikin jakarta ta fara rubutu, tana gamawa ta aza mashi takardar a saman bencinshi ta ce "Idan ka bamu yarinyar ba wanda zai san da wannan maganar domin muma kawar da ita ne za muyi.!" Numfasawa ya yi a hankali kafin ya maida hankalinshi gare su ya ce "Amma kun san wannan aiki ne mai matuk'ar wahala? ya zanyi idan aka neme wannan yarinyar aka rasa.!" cike da annurin da fuskar Hajiya Maryam ke nunawa ganin ya fara sakkowa a hankali ya saka ta yin wata 'yar sililiyar dariya sannan ta ce "CP! kai ko kake da yanda zaka yi musamman idan ka kwantar da hankalinka kayi tunani akan wannan al-amarin, amma bara na d'an k'ara maka haske a cikin wannan lamarin! shin me zai faru idan har aka mata allurar bacci ta kwana d'aya, bayan ta kwanta bacci sai ka yi wani d'an rubuce-rubuce na cewa, zuciyarta ta buga a wannan lokacin kuma ta mutu, idan aka turo Doctors su k'ara duba ta dan a tabbatar da gaskiyar zancen, sai kayi dik yanda za kayi wajen ganin ka shawo kan wad'annan Doctor's sun aminta da buk'atarka, bayan an gama ka kira mu mu saka hannu mu amshe gawarmu, daga nan kuma yallab'ai zancen da nake gaya maka maganar nan ta mutu an wuce wannan wajen.!" ajiyar zuciya mai nauyi ya fara saukewa kafin ya ce "Shawararki tayi dai-dai da tawa, dama kuma ina da Doctors ukku wad'anda suke taimaka man idan za ayi irin wannan aikin, to amma kud'in da naga kin rubuta d'inne kamar ba zasu isa ba.!" Murmushi mai k'ayatarwa Hajiya Maryam ta saki kafin ta ce "wannan 2M d'in da kaga na rubuta maka a wannan takardar, ba yana nufin su kad'ai ne ba akwai cikonsu amma sai bayan aikin ya gama kammala ne zamu ida biyanka.!" ya ce "kar ku da mu! ku k'addara ma kamar komai ya kammala ne.!" Ammie ta ce "Alhmdu lillah, haka muke son ji yallab'ai amma yanzu kamar yaushe zamu same ta?." Ya ce "wannan ba damuwa ba ne misalin 7:00pm ma ya yi, dan yanzu kuna tafiya zan fara aiki na.!" Ammie ta ce "Ya yi kyau yallab'ai, godiya muke sosai.!" a haka suka yi mashi sallama sannan suka tashi suka yi tafiyarsu zuciyarsu cike da farin ciki. Bayan sun tafi ne CP ya fara gudanar da aikinshi kamar yanda suka tsara, sai bayan da komai ya kammala Misalin k'arfe 7:00am ya kira su Ammie ya sanar da su aikin ya kammala, ko 30mins ba a k'ara ba sai gasu sun iso wajen tare da Khairat, suka d'auke Ni kamar gawa domin bani da mararraba da gawar, kai tsaye gidan Hajiya Maryam suka wuce da ni wanda hakan dik yana cikin shirinsu. Sai da dare ya tsala misalin k'arfe 12:30pm suka tafi bayan gari cikin wata tsohuwar mak'abarta, anan suka tarar da wad'anda zasu yi masu aikin hak'on ramen, a hanzarce aka shiga hak'on ramen cikin gaggawa sabida gudun kar azo a same su anan assirinsu ya tonu, jin k'arar wasu karnuka dake k'ok'arin nufato wajen da suke ya sa a d'inauce suka jefa ni cikin wannan ramen suka rufe ni da k'asa suka daddale, a guje suka baro wajen cikin wani matsiyacin gudu domin kad'an d'e ya rage a kama su dan sunga alamun ana yade-yaden fitila cikin mak'abartar, sai da suka kusan kawowa dafda motarsu Ammie ta juyo da k'arfi cikin wani mugun tashin hankali ta ce ma Khairat "Ina fatan dai kin saka wannan layar a cikin bak'inta kafin a binne ta.?" a tsoroce Khairat ta wawwaro idanuwa waje ta ce "Ammie Layar ba a hannunki ta ke ba.?" Hajiya Maryam kam bata san lokacinda bakinta ya
furta "Babbar bu...ubannan." a harzuk'e Ammie tayo wajen Khairat da k'arfi ta fincike jakar dake hannunta ta shiga k'ok'arin zwage zip d'in jakar, tana soka hannunta cikin jakar ba ta wani sha wata walahar nema ba taji ta kamo wannan layar, aiko cike da wani mugun tashin hankali ta fiddo layar waje tana kallonta kafin ta kurma wani kafurin ihu tana fad'in "Maryam yau mun shiga ukku Khairat ta kaimu ta baro! wayyo Allah'na! Allah dai ya isa tsakanina da ke Khairat shegiya d'ebabbiyar albarka d'iyar shaggu. Ko 1second ba a k'ara ba da guduwar su Ammie a mak'abartar wata guguwa mai k'arfin gaske ta tashi a wajen wanda nan take gabad'ai yashin da suka saka suka daddale ni da shi ya fita daga cikin wannan ramen............!
..........wasa farin girki.
FAD'IMATUL FIDDAUSI S/BAKI (SOKOTO) SMART FEENERT ^BE SMART.
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*^Pls shere^*
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...
