P...3

1K 105 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*P...3*

_Ina karkare sallar nayi addu'a na shafa, Ko ina kwana ban tsaya yi masu ba, kai tsaye na ce "Wai Kaka wa ake nufin Mummy Balki zata zo ta dauka?"._

_A hasale, kamar wadda akawa wani abu, ta ce, "Ba a sani ba bakar munafuka, wato sallah kike amma kunnuwanki na wajen mu ko! danɗe kicihi." Ta karasa maganar tana mai watso man ruwan harara, Ita kuma Gwaggo Talatuwa tsaki ɗai taja tare da kauda fuskarta gefe tana kallon wani gurin na daban kamar wadda aka yima tayin kashin alade,_

_Cikin mugun jin haushin su gabadai, na ce "Daga tambaya kuma sai a hauni da bak'ar magana kamar...... ban ida karasa zancen ba Kaka ta katse ni ta hanyar daka mani tsawa tana fadin "Maza na tashi nayi shirin makaranta tun kafin lokaci ya kure, ko wallahi yanzu jikina ya gaya mani,"_

_Aiko ina jin Tayi maganar zuwa Makaranta, na barke da wani shagwababben kuka ina fadin "Ban wallahi zuwa, dik naje Makarantar Boko sai yara sun man dariya, su na ce man katuwa cikin kananan yara, ga Malam Fasa'kauri yaki ya bani monitor sai Zara'u Muhammad ya dauka ya bawa, shi kuma Malam Aminu 'Yar budurwa dik ya shigo aji kafin ya ce wani abu, sai ya sakani tashi tsaye yafi sau100, da ya fara rubutu a saman allo, sai ya ce nazo na goge ya sake yin wani, 'yan ajinmu su yita yi man da.........." Hannu Kaka ne da naji yayi gaggawar sauka a saman baki na ya ankarar dani, cike da masifa take cewa "Dan ubanki tambayar ki na yi?, Fatima! Fatima!!, Fatima!!!, wlhy ki kiyaye ni, ba zaki tashi ki bace man daga gani ba ne, sai na kara maki da shuri! ja'irar Yarinya kawai,_

_A hasale na mike tsaye dan bugun da tayi man a baki har yanzu radadin shi nake ji, a zuciye na shige daki na dauko uniform dina da sun yi kusan sati biyu basu ga ruwa a saman su ba, ga kuma wandon da ya gama barkewa sosai harga mugun waje, sai dai ya ji dashin wata farar shadda, da nakai wajen tella ya saka man, dan cewa ya yi, "wandon ba ya dunkuwa dole sai anyi mashi dashi". dan dole na hakura na aminta aka yi,_

_Bayan na fito palour, na afkawa jikina su, gaba ga su Kaka, ko kunya babu, sannan na dauke ledar littafaina zan kama hanya, dan yau ko naira gomar da nake amsa wajen Kaka ban tsaya cewa ta bani ba, har na juya zan bar dakin, na ji Kaka na kirana, cikin izza tare da shan kamshi, na juyo baya ina tafowa wajen ta, dan dik a tunani wani abin kirki ne zata bani, nan sai naji ta ce "ga Zazahe (dimame) nan da Talatu ta yi na tuwon jiya, ta zubaman a cikin Langa na je da shi,_

_Wani irin kololon bakin ciki ne naji ya tokare man makogoro, akan mugun jin haushin wannan maganar, bansan lokacin da na fazge da wani raki'in kuka ba, ina fadin "Wai ni yaushe za'a maidani 'yar bariki, ace kullum da tutun kato da miyar ɓakko (ku ka) ake hadani na je da su makaranta, ga su Hauwa Ahmed, kullum daga Shinkafa sai Taliya suke tafiya da su makaranta, wlhy yau sai dai na zauna hakanan banci komai ba,_

_Gwaggo Talatuwa ta ce "Iyyeee lallai Fatima wuyanki ya isa yanka, yanzu Inna kike gayawa wadannan bakaken maganganun?,_

_Cikin rai na, na ce "Kunji ita kuma kanwa uwar gami, to na fada din"._

_Kaka ta ce "Hmm Talatu kenan, ai wallahi yanzu ganin kanta take dai-dai da ni, amma barni da shegiya" ta karasa maganar tana mai raramo wani gundumemen icce da ke gefen kujerar da take zaune,_

_Aiko ina ganin hakan aguje na zarce tare da daukar Zazahen na fece, zuciya ta cike da kudirin daukar fansa anjima idan na dawo daga makaranta, ko zan'iya huce haushin su,_

_Ina kawowa daf da bakin kofar fita garka na yi kicibus da wani mutum irin gayun nan na kauye, ya zo wucewa, sai ƙambo yake yana wani doro, dan ya saka sabbin kaya, irin yana jin ranar yau kamar ranar Babbar Sallah, Aiko ban san sanda Langar Zazahe na ta kai ma jikin shi ziyara ba......._
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*Be smart*
*pls shere*

'YAR BALLAJJA'UDonde viven las historias. Descúbrelo ahora