*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**_WANNAN BUK YA DAWO SUNANSHI KAMAR YANDA KUKE GANI SABIDA WASU DALILAI INA FATAN BAN RIKITAR DA KU DA YAWA BA MY FAN'S._*
*P...33*
"Papa?." Ita ce tambayar da tayi gaggawar fitowa daga cikin bakina, nan da nan naji wani irin mugun firgici ya k'ara turmuk'eni fiye da wanda nake ciki, a tsorace na d'aga daga wajen da yake tare da da dafe kunnayena biyu da hannayena na runtse idanuwana gam a firgice nake fad'in "A'a! a'a!! a'a ba shi ba ne.... Papa'na ya dad'e da rasuwa! wai me yake son faruwa da ni ne.....?." wani hatsabibin kuka ne da naji ya yi gaggawar kub'ece man kai tsaye ya sa na duk'e k'asa ina ci gaba da kukan tare da marad'in gasgata abinda nake gani ba mafalki ba ne, d'ago kaina sama da zanyi na k'ara kallon wajen naga yana k'ok'arin nufato wajen da nake, a firgice na mik'e tsaye tare da ja da baya na daka mashi tsawa a razane na ce "Kai ba Papa'na ba ne! idan ka matso wajen da nake wlhy sai na kashe ka na kashe kaina.!" cakkk ya tsaya yana kallona cike da mamaki, har a wannan lokacin wannan murmushi bai gushe a fuskarshi ba, wani ihun farin ciki ne da naji anyi a bayana ya ankaran da hankalina a wajen. Gurnanin wani abu ne da suka ji har a cikin kogon zuciyarsu kamar na zaki ya sa a firgice suka falka daga nannauyan baccin da suke yi kowaccensu ta mik'e zaune tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ganin rana b'uru-b'uru ta fito a fili suna kallonta kafin daga bisani su tsintsin kansu cikin kwakkwanton tuno abinda ya faru da su a daren jiya har ya kai da sun same kansu a irin wannan wahalallen yanayin sai dai suna jin kamar hakan na son gagarar kwakwalwarsu, nan take Ammie ta yi firgigit ta mik'e tsaye tunawa da wani abu da ta yi, cikin fuskar fita a cikin hanyaci ta shiga kwasar gudu wanda hakan ya sa su Hajiya Maryam rufa mata baya ba tare da musu ko kuma kwakkwanton inda suka nufa ba, kai tsaye Ammie cikin wannan tsohuwar mak'abartar ta nufa sai dai bata ida kaiwa wajenda zata nufa ba ta tsaya cakkk tana kallon wajen a rud'e. Abba ne shi da Alhaji Sulaiman zaune gaban D.P.O suna jiran jin inda binciken na su ya dosa, sai dai DPO bai ida k'ark'are masu bayanin da yake masu ba yaga gabad'ayansu sun b'ingire sun fad'i kwance a wajen da suke kuma dik a lokaci guda, cike da mugun tashin hankali D.P.O ya kira d'ai daga cikin officer'nshi, bayan ya zo ya kawo mashi ruwa ya shiga yayyafawa su Abba amma shiru babu alamun kingin numfashi a tattare da su wanda hakan ya sa aka d'auke su gabad'ai aka nufi Asibiti da su. Misalin k'arfe 2:00pm Intisar da Yumra tare Yubra suka shirya tsaf suka nufi Asibitin da aka kwantar da Ya Fadil, bayan sun isa Asibitin shigarsu d'akin kad'ai ke da wuya bayan sunyi sallama Ya Abir ya amsa masu ba tare da yin firar komai akai ba suka ga Ya Abir ya zame jiki ya fad'i k'asa wanda hakan ya sa a gid'ime suka je suka kiranyo Doctors nan take aka shiga bashi taimakon gaggawa. Cike da wani matsanamcin tashin hankali Ammie ta nufi wajen kamar wata zautacciya tana fad'in "Maryam ina gawar da muka saka jiya? Maryam ina gawa? Ina gawar na ce.?" ba tare da ta tsaya jiran amsar da Hajiya Maryam zata bata ba ta fad'a cikin ramen tsunbul tana yakutar dik inda hannunta ya cab'a cikin wani mugun tashin hankali take fad'in "Ai bamu saka ta dai-dai ba Maryam! wlhy bamu saka ta dai-d........!" kukan da ta kece da shine ya ci k'arfinta wanda hakan ya sa Hajiya Maryam tafowa wajenda take a raunane ta dafa kafad'arta a hankali take ce mata "Karki d'aga hankalinki da yawa akan wannan abin domin abinda ki ka gani ba shine gaskiyar al'amarin ba kuma ba shine k'arshen aikin ba, yanzu abinda nake so da ke ki kwantar da hankalinki mu koma wajen Boka mu gaya mashi dik abinda ke faruwa ina da tabbacin koma me zai faru zai fito muna da wata mafitar ta daban, yanzu mu yi sauri mu bar wannan wajen kar a kama mu.!" banda kuka ba abinda Ammie ke yi, haka dai har suka samu ta fito daga cikin ramen, Khairat kam tsaye kawai take gefe tana kallonsu cike da takaicinsu a rai har suka samu suka bar wajen a hanzarce..............
Banada isasshen caji, dan Allah ku yi manage da wannan.
*FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert*
*#Be-smart*
*^Pls share^*
![](https://img.wattpad.com/cover/215007905-288-k317588.jpg)
STAI LEGGENDO
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...