*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*P...37
"Shekarata biyar a cikin wannan kogon Allah ya kub'tar da ni daga shairinsu inda kai tsaye na tunkare wata masarauta dake nesa da ta mu kasancewar sarkin garin abokin mahaifina ne tun yana raya wanda hakan ya k'ara man kwarin gwiwar rok'on wata alfarma a wajen sarkin wannan masautar akan ya taimaka man da mayak'a domin na je na amshi garina na kuma dakatar da zalumcin da ake aikatawa a cikinshi, cikin wata ukku kacal muka shirya mayak'an ba tare da sun san da zuwanmu wajen ba muka mamayesu har Allah ya bamu nasarar cinsu da yak'i tun daga wannan lokacin na amshi sarautar wanda har a yanzu ni ne a matsayin sarki.!" yana kawowa daganan ya dasa aya tare da share wani d'an guntun kwalla da ke k'ok'arin fad'o mashi a saman fuska ya sake wani k'ayataccen murmushin shi na k'arfin hali dan bai kai ciki ba sannan ya tumkare wajen da Zulfa take tsaye da ita ma dik hawaye ya wanke mata fuska, ya rik'o hannunta a hankali sannan ya sake cewa "Bayan komai ya dawo dai-dai na fara tunanin abinda zanyi ma wannan nagartaccen jarumin sarki dan naga na saka mashi, sai na fara tunanin auren 'yarshi guda d'aya tilo wadda ita kad'ai Allah ya bashi kasancewar wata ukkun da muka yi a tare shak'uwa mai k'arfi ta wanzu ga junanmu ya sa ba a d'au tsawon wani lokaci ba muka yi aure.!" ya k'ark'are maganar ne yana mai kallon fuskar Zulfa cikin wani k'ayataccen murmushinshi mai cike da burgewa sannan ya k'ara da cewa "wannan ita ce Zulfa'u bn Lirwan, wato d'iyar nagartaccen sarkin da nake baki labari!, a lokacinda kike k'arama 'yar kimanin shekara5 bayan na bata labarin mahaifiyarki sosai ta tausaya ma wannan al-amarin da kuma halin da zaki taso ki tsintsi kanki a ciki na maraici wanda hakan ya sa kusan kullum idan kina bacci sai ta d'aukoki ta zo da ke cikin wannan masarautar mu yita rainonki har lokacin tashinki daga bacci ya yi ta je ta maidaki, haka muka ci gaba da rainon k'aunarki da sonki a cikin zuciyarmu har kika kai matakin shekara takwas a wannan lokacin ne muka d'an daga maki k'afa sabida wasu dalilai sai dai ba dan zuciyoyinmu sunso ba har Allah ya azurta Zulfa da samun ciki, ta haife abinda Allah ya bamu 'ya mace, sabida tsananin k'aunar da muke maki ne ya sa muka saka mata sunanki!, Allah shi kad'ai ya san abinda yake nufi da kamanninku da komai na ku ya zamo iri d'aya!, sannan wad'annan matan da ke d'awainiya da ke tun lokacinda kika tashi kika same kanki a cikin wannan masarautar, tun kina 'yar shekara 5 suke tare da ke kuma suke d'awainiya da ke!, abinda ya faru da ke ki d'auka cewa shi ne k'addararki kuma shine jabawar da Allah ya zana maki dikkanmu nan mun shiga jarabawa iri-iri amma ko da hakan muna cikin godewa ubangiji domin shi kad'ai ya san irin tanadin da ya yi muna ranar gobe k'iyama sannan mutuwarsu Kaka ki k'addara cewa lokacinsu ne ya yi domin babu mai wuce lokacinsa, aurenki da aka d'aura da Abir ba yin kowa ba ne sai na ubangiji ta'ala ina son ki d'aukeshi a matsayin alkhairi ne a wajenki, Allah ya azurta mu da abinda ya fi k'arfinmu.!" yana gama fad'in hakan ya juya zai fita a d'akin cikin wani matsanancin kuka na tashi daga saman gadon naje na rungumeshi ta bayanshi ina kuka hinhinhim, juyoni ya yi ta gabanshi ya shiga shareman hawayena cikin tausayawa yake fad'in "Ya isa! Ya isa kinji ki daina kukan ya isa haka.!" Ya k'ark'are maganar ne yana mai janyoni muka dawo wajen gadon a dai-dai wannan lokacin Zulfa ta taso ta rik'o hannuna ta zaunar da ni ta aza kaina saman k'irjinta tana bubbuga bayana tana cewa "Karki da mu d'iyata yanzu komai ya zo k'arshe, dik sihirin da aka maki da kuma na sauran dik na saka an k'aryashi ki bamu d'an lokaci kad'an zamu maida ki gida kinji.!" cikin shashshek'ar kuka na ce "Mummy ni bana son na koma na fi son na zauna tare da ku na rama maku abinda kuka man.!" Murmushi ta yi mai ban sha'awa ta ce "Ke d'iyarmu ce kuma jininmu dik abinda muka maki kanmu muka wa a koda yaushe fatanmu ki kasance cikin farin ciki mai d'aurewa a ko wanne irin yanayi Fatima! Allah ya albarkace rayuwarku.!" tare muka amsa da "Amin ya rabbi." Ni da Papa, murmushi Zulfa ta yi kafin ta ce man nakwanta na futa zuwa anjima zata zagaya da ni cikin masarautar "To Mummy.!" kawai na iya cewa da ita cikin annashuwa mai had'e da hawayen farin ciki wad'anda sun kasa tsayawa sannan na kwanta kamar yanda ta umarceni, sai da ta gyara man kwanciyata da kyau sannan suka bar d'akin ita da Papa, tashi nayi zaune ina tunanin abubuwa da dama, wasu su sakani murmushi wasu kuma su sakani kuka, tunowa nayi da maganar da Papa ya yi man ta cewa "Aurena da Abir na d'aukeshi a matsayin Alkhairi ne a wajena.!" Murmushin takaici nayi mai had'e da kwalla na ce "Hmm Abir! Abir!! Abir!!! dan ba ku san k'unar da zuciyata ke yi ba ne idan har aka kira man sunnan wannan marar imani kuma marar tausayin ba ne! wlhy Abir ka yaud'areni kuma ka ha'ince rayuwata! a haka kake son nayi zaman aure da mutum irinka, zaman da babu komai a cikinshi sai yaudara! zaman da ba zaya tsinanemu da komai ba sai tarin nadama da danasani! zaman da za'ayishi cikin k'iyayya da k'untatawa juna! inaaaa wlhy har abada ba zan tab'a zama da macucin mutum irinka ba Abir! kuma dik yanda ya kamata nayi zanyi dan ganin an datse igiyar dake tsakanina da kai, wallahi na tsaneka na tsane mutum mai irin halinka.!" a haka nayita zuba sambatuna har babban b'arawonnan mai bak'in uwa bacci ya zo ya yi awon gaba da ni.......!
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
VOCÊ ESTÁ LENDO
'YAR BALLAJJA'U
FantasiaSai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...