P...19

423 55 6
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

_Assalamu Alaikum_

_Ina mai bawa masoyan wannan littafin hak'uri a bisa rashin jina da kuka yi kwana biyu, wannan matsalar ta faru ne ta sanadiyyar wasu uzururruka da suka gifta man uwa-uba ga matsalar Nepa da muke fama da ita a halin yanzu, dan Allah ku k'ara hak'uri da ni Fan's insha Allah zaku dinga samun typing a ko wanne lokaci idan na samu caji, Na gode sosai da kulwar ku gare ni_
_Masu kira na da masu turomin text ta inbox ina godiya sosai Allah ya bar zumunci Ameen_

*P...19*

Bayan su Mummy sun dawo gida, kai tsaye part d'inta ta nufa, ganin ta duba a ko ina har a cikin bedroom d'inta ba ta same Fatima anan ba yasa kai tsaye ta nufi part din su Aunty Intisar.

Sai dai da mamakin ta ganin su tayi kwakkwance a saman gadon su na alfarma kamar kayan wanki sai famar sharb'ar baccin su suke cikin kwanciyar hankali da walwala wanda hakan yasa taji alamun jikinta na bata kamar ba baccin gaskiya ne suke ba, nan take cikin wata tafasasshiyar murya mai cike da ruwan bala'i ta soma kwalawa Aunty Intisar kira wanda hakan ya yi sanadiyyar mik'ewar su zaune a zabure kamar wasu Akuyoyi cikin mugun tashin hankali
Kai tsaye abin da ta fara tambayar su akai shi ne,
"Ina Fatima?"

Cikin wani irin mugun yanayi na shakkun bata wannan amsar kowaccen su ta kalle d'aya cikin kollo-kallon junan su kamar wasu k'asungumen munafukai kafin Aunty Intisar ta soma kwakwalo murmushin k'arfin hali sannan ta soma magana cikin Inda-inda inda take cewa "Eh! to daman Fat....tii...." tsawar da taji Mummy tayi gaggawar daka masu ne ya yi hanzarin dawo da hankalin su waje d'aya inda Mummy ta soma magana cikin fad'a take cewa "Dik na d'ago da ku, gabadayan ku babu alamun gaskiya a tattare da fuskokin ku! Shin zaku fad'a man gaskiya ne ko sai gabadayan ku na sassab'a maku kamannun fuskoki?."
Cikin wani irin k'arfin halin had'iye yawu kamar mayya Aunty Intisar Ta soma yi mata bayani, inda ta kwashe komai ta sanar da ita, sai dai ba yanda abin yake ta fad'a mata ba.
Aunty Khairat kam ji take kamar ta tado Aljannun k'arya dan ta samu damar dank'o wuyan Mummy ta shak'e har sai taga alamun numfashin ta ya daina fita da kyau a jikin ta akan haushin yanda taga dik ta wani d'aga hankalin ta akan rashin ganin mak'iyiyar ta Fatima da ba tayi ba.

Suman zaune Mummy ta fara yi tare da ambaton sunayen Ubangiji 99 kafin ta soma lalabar wayar ta a cikin Jaka, ta shiga kwalawa Ya Bikhram kira kamar ta fashe screen d'in wayar gabadai a futa akan wani mugun tashin hankalin da take jin yana tsakulo ta.
Sai dai wani abin ban haushi, kiran da ta mashi yafi a k'irga amma shiru take ji yak'i ya d'auki wayar balatana ta d'an ji sassaucin tafarfasar da zuciyar ta keyi,
sai da tayi da gaske wajen d'inga jera mashi kiran a jajjere kamar abin dole dak'yar da wala-haula ta samu ya d'auki wayar kai tsaye tambayar Asibitin da ya kai Fatima tayi, yana gama gaya mata wajen ta yanke kiran inda ba tayi k'asa a gwiwa ba wajen kiran Daddy da Ya Abir ta sanar da su halin da ake ciki, aiko ba tare da wani b'ata lokaci ba sai gasu sun bayyana gabadai a gidan, kai tsaye aka dunguma gabad'ai aka wuce Asibitin harda su Aunty Intisar
Gidan ya koma wayauuu babu kowa a cikin shi sai tulin 'yan aiki dik da suma dik hankalin su a tashe yake dan gudun ganin abin da zai iya biyowa baya akan sakacin da suka yi.

~~~

A Asibiti kuwa, ba irin taimakon da ba'a bawa Fatima ba wajen samun Numfashin ta ya dawo dai-dai, amma hakan ya cutura

Mummy kam da su Yumrah sai famar koke-koke ake ana rok'on Allah da ya tashe kafad'un ta,

A b'angare guda kuma su Aunty Khairat ba abin da ke cikin zuciyoyin su sai tulin farin ciki da godiya a gurin Ubangiji da fatan kar ta tashi lafiya dik da ba su nuna alamun hakan a fuskokin su ba.
Mummy ce aka ji ta fara sambatu tana cewa "Yanzu Idan wannan yarinyar ta rasa rayuwar ta ina zan saka kai na! Amanar Allah da amanar mahaifiyar ta da ta mutu ta bar muna amma ace mun kasa rik'ewa, shin ni yanzu da wanne irin Ido ne zan kalle Hajiya? Me zan gaya mata? da wanne irin kalami ne zan iya wanke kai na? Kaiiii amma banyi adalci ba, Babu yanda wannan yarinyar bata yi ba akan ba zata biyo mu ba amma na takura ta ta hanyar janyo hankalin ta har ta aminta ta biyo mu, a maimakon na kula da ita yanda ya kamata amma yanzu ku dubi abin da sakaci na ya haifar har ina ji kamar ni na fiye son k........... bata kai ga k'arasa zancen nata ba su Aunty Intisar suka fara lallashin ta cikin wata kisisina ta munafurci domin su Mazan gabadayan su suna wajen Doctor da tun zuwan su a Asibitin ya kira su ciki.
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*Pls shere*

'YAR BALLAJJA'UOnde histórias criam vida. Descubra agora