*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*P...36
Wata had'ad'd'iyar doguwar riga ce pitch color mai zanen golden a cikinta naga sun bud'e widrop sun fiddo, tunanin wannan rigar wa ce na fara kafin nayi yunk'urin mik'ewa tsaye na d'auki tufafin da na cire d'azu da niyyar sake maidawa, na ji d'ai daga cikinsu ta soma man magana cikin wata tausasshiyar muryarta da cewa "Ranki ya dad'e Mai-Martaba ne ya ce mu baki wannan rigar ki saka.!" ta k'ark'are maganar ne cikin duk'ar da kanta k'asa tana mai mik'o man wannan rigar, murmushi da bansan da zuwanshi ba naji ya kub'ce man a hankali na amshi wannan rigar a hannunta, a dai-dai wannan lokacin na ga ta saka hannu ta amshi wata jaka dake hannun d'ai d'aga cikinsu ta sake mik'o man, ina amsar wannan jakar a hanzarce suka bar d'akin gabad'ayansu cikin ladabi, saman gado gabad'ai na sauke ma wad'annan kayan farali kafin nayi yunk'urin bud'e wannan jakar, kayan wanduna da bra ne a cikinta, tsaki nayi tare da mik'ewa tsaye na shiga shiryawa sai da na saka wannan rigar naji alamun ana kwankwasa k'ofar kai tsaye na ce "Shigo" shigowar suka yi rik'e da mayafin wannan rigar tare da takalumma da sauran tarkacensu sarkok'i da dai sauransu, murmushi suka man gabad'ayansu wanda hakan ya sa ni ma sakar masu nawa, bayan sun gama shiryani tsaf suka dawo da ni gaban madubin d'akin Wa'iyazu billahi fad'in had'uwar da naga nayi ma b'ata lokaci ne sosai nayi matuk'ar kyau kamar sarauniyar kyau ta indiya, ja na suka yi a hankali muka bar part d'in muka nufi wani b'angaren wanda da farkon shigarshi har k'arshenshi cike yake da masu tsaro kala-kala, wata zumdumemiyar k'ofa ce wadda muna kawowa daf da ita ta bud'e nan take wani had'ad'd'en waje yabayyana a cikinta mai cike da kayan lambu iri-iri, wasu kyawawan mata ne na hango suna tashi sama kamar tsuntsaye suna wasannaninsu cikin nishad'i, k'afafuwana ne naji sun fara mazarniyar rawa dan tunda nake ban tab'a ganin mutum ya tashi sama ba, tafiyar da naji alamun anayi da ni ne a saman iska ya k'ara d'aga man hankali wanda ihun da nake murad'in saki kuma ya gagara, nan take naji na zame jiki na fad'i a wajen sumammiya, daga nan kuma ban sake sanin inda kaina yake ba!. K'asa ce suka ga ta tsage wata iggiyar k'arfe ta fito daga cikin k'asar ba tare da Boka Dundum ya ankara da hakan ba tuni ya ji ta mashi damk'ar tarmani gabad'ai ta laulayeshi a razane ya sake wani irin wawan ihu wanda sai da ya dawo da hankalin su Ammie a wajen ganin k'asa na k'ok'arin rufewa da Boka Dumdum a gaggauce yasa su Ammie firgicewa kafin suyi wani yunk'urin guduwa tuni kangon Boka ya shiga girgiza ta ko ina ya rud'e baka jin k'arar komai a wajen sai k'arar sautin wata mahaukwacciyar dariya mai had'e da kukan Jaki wadda ko za a kashe ka ba zaka ce ga wanda yake yinta ba. DPO ne zaune a gaban wani shahartaccen Malami wanda DpO'n dik ya gama yi mashi bayanin abinda ke faruwa, murmushi wannan Malamin ya yi kafin ya dubi DPO ya ce mashi "Tabbas wannan matsalar ba aikin komai ba ne sai aikin assiri.!" da mamaki shimfid'e a fuskar DPO ya ce "Assiri?.!" a tsanake wannan malam ya d'an numfasa kad'an ya ce "kwarai kuwa wannan aikin sihiri ne yallab'ai, kuma abin mamaki na tare da su ne ke da alhakin aikata masu hakan, sai dai nayi matuk'ar mamakin yanda aka yi komai ya zo masu da sauk'i haka domin wannan aikin da aka masu shi ake kira da AIKIN BAK'IN SIHIRI zan iya ce maka wannan cases na su shi ne na hud'u da aka tab'a kawoman anan cikin makaranta ta, kuma wlhy sai an tashi tsaye an sha da k'yar sannan yake fara fita a jikinsu in takaice maka zancen ma akwai wanda ya tab'a har shekara guda a wajennan yana jinya sai da aka je mashi aikin hajji sannan aka samu sauk'in abin, sai dai yanzu da na gansu gabad'ai naga alamun assirin ya fara fita a jikinsu.!" cikin hamdala mai had'e da numfashin girgiza da wannan al-amarin DPO ya ce "Alhamdulillah! amma Malam! yanzu kamar wa kake tunanin yake da alhakin aikata hakan.?" Murmushi wannan Malamin ya sake yi kafin ya ce "babu wanda ya san gaibu sai Allah amma ina da tabbacin cewa! in sha Allah dik wanda yake da alhakin aikata wannan abin gobe-gobennan zaka ganshi ya zo nan wajen da k'afafuwanshi sannan da bakinshi zaya fad'i dik irin abinda ya yiwa wad'annan bayin Allah.!" Kai kawai DPO ya iya girgizawa alamun ban al-ajabi sannan ya ce "To Allah ya bayyanasu kuma ya toni assirinsu.!" Malam ya ce "Ameen ya Allah.!" sannan suka yi sallama da DPO akan su zasu koma wajen aikinsu sai gobe da safe za su dawo tare da ajiyewa wannan Malamin tukwici mai tsoka wanda sai da ya saka shi godiya sannan ya yi masu rakkiya har wajen da suka yi parkin, sai da suka bar k'ofar gidan sannan ya dawo ciki inda ya ba wa almajiranshi umarnin yi mashi rubutun da zaya bawa su Ya Abir..... Bud'e idanuwana nayi a hankali ina kallon mutanen da ke wajen, wata kyakkyawar budurwa ce ajin farko wadda shekarunta ba zasu haura 24 ba na fara tozali da ita, sanye take cikin kayan sarauta wadda kana ganinta ka ga sarauniya ko ba a fad'a maka ba, mik'ewa nayi zaune ina bin ko ina da kallo har idanuwana suka kai ga Papa dake tsaye ya kasa zama, wannan matar ce ta yi k'arfin halin kai hannunta saman nawa a hanzarce na gwabce hannuna dake k'asan nata a raunane na ce "Ku su waye?! me nake yi a wajenku?.!" Murmushin k'arfin hali wannan matar tayi kafin ta ce man "Da farko dai.........!" Papa ne ya yi k'arfin halin katseta da cewa "A'a Zulfa wannan tambayar hakkin amsata ya rataya ne a wuyana sai dai kafin na kaiga bata amsar tambayoyinta zan so na fara bata wani d'an tak'aitaccen tarihina wanda ta wata fuskar ya shafe wani abu daga cikin tambayoyinta.!" shiru wajen ya yi na d'an wani lokaci kafin Papa ya nisa ya d'an fara zagayen d'akin lokaci guda ya sake numfasawa kad'an alamun shiryawa sannan ya ce "Ni sunana Muhammad bn Mutallif, ni ba mutum ba ne kamar yanda kike gani yanzu a zahiri, hasali ma wannan duniyar da kike cikinta a yanzu ba d'an adam ko guda dake rayuwa a cikinta domin Allah bai bashi wannan damar na zama acikinta ba, kuma a haka muke rayuwa a cikinta kamar yanda muka taso muka cinma kakanninmu da iyayenmu suna yi, sunan wannan masarautar! MASARAUTAR KISRAN, masarauta ce mai d'auke da d'imbin tarihi kala-kala wadda ta kwashe tsawon shekaru ana mulki a cikinta tun zamanin zamannai, a dah mahaifina ne sarkin wannan masarautar kafin ni wanda tun a lokacinda yake raye ya so ya dank'a ragamar mulkin wannan shahartacciyar masarautar a hanuna kasancewar ni kad'ai ne d'a a gareshi kuma namiji, tun ina d'an k'aramin yarona Allah ya yiwa mahaifiyata cikawa wanda hakan ya sa mahaifina d'aura so da k'aunar duniya a gareni, lokacinda mahaifina ya zo man da wannan maganar ta mik'a mulkin a hanuna, ko kad'an raina bai so da hakan ba kuma na nuna mashi rashin dacewar hakan kasancewar a kwai k'annenshi a raye su biyu wad'anda suke uba guda da shi sai dai fir ya k'i amincewa da buk'atar hakan wanda hakan shi ya yi sanadiyyar janyo wata gagarumar k'iyayya a tsakaninshi da 'yan uwan na shi har ta kai ga sun had'a kai da wasu bak'ak'en aljannai christoci suka b'atar da ni inda suka jefoni cikin duniyar mutane sannan suka nakkasani ya zamana na koma kamar wani marar amfani domin dik wani k'arfin da ke jikina sai dai suka yi nasarar dak'ileshi inda na sauka a Kebbi wanda kai tsaye na had'u da wani natsatstsen malami dik da cewa ya san ni ba mutum ba ne amma haka ya d'aukeni ya sakani a jikinshi ya k'aramin ilimi har Allah ya had'ani da mahaifiyarki muka yi aure ba wanda ya san sirrina sai wannan malamin da ya rik'e ni da amana lokacinda wad'annan mugayen aljannun suka same labarin auren da na yi a cikin duniyarku da kuma wanda ya bani gudumawar yin hakan suka zo suka halakashi shi da iyalanshi ni kuma a dai-dai lokacinda mahaifiyarki ke asibiti zata haifeki ina kan hanyata ta zuwa asibitin suka zo suka d'aukeni daga duniyarku bayan sun kashe mahaifina suka sake ajiyeni a cikin wani kogo wanda babu komai a cikinshi sai azabar duhu da zafi........"
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shared
ESTÁS LEYENDO
'YAR BALLAJJA'U
FantasíaSai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...