P...8

661 100 5
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*P...8*

_Bayan nayi wankan na shirya tsaf cikin wata sabuwar atamfata wadda Kaka ta dinkaman tunda dadewa, sannan na ranbada powder a fuska naja jagira harga mugun waje, ni kaina da na kalle madubi nasan nayi kyau sosai tare da ganin kalar fuskata ta koma sak data tunkiyar Matar Baba mai fuskar munafukai (Wato tunkiyar makotan mu), sai dai na basar da abinda nake kokarin fahimta, ta hanyar wurgar da madubin gefen domin nasan idan naci gaba da kallon shi to babu shakka zan iya gurzar fuskata da susun karfe._

...

_Cike da rangwada nake tafiya ina bankare gaba, kamar wata cikakkiyar 'yar duniya, harna kawo dafda kofar shiga part din,_
_Ba tare da fargabar komai a raina ba, na fada ciki, bakina dauke da sallama, a guje Yumra da Yubra suka taso cikin farin ciki suka rumgume ni, kamar daman nice bakuwar, sake da baki galalala kamar wata wawuyar kaza, nima na rumgume su ina masu sannu da zuwa sannan na karasa wajen Mummy Balkisu itama na kwashe gaisuwa tare da tambayarta Aunty Intisar, ta ce "Ai tana gida daman bata bisu ba, sabida lokacin suna Exam ne a skull"._
_Cikin Raina na ce "Alhmdu lillah gwanda da Allah ya kaddaro da hakan."_
_Juyawar da zanyi gefe na hango Gwaggo Talatuwa make waje guda ana ta famar taunar kassa ana sharce zufa, kamar abin dole, a takaice na mike tsaye na tashi da hanzari nabar wajen domin na lura Itama Kaka tun lokacin da na shigo cikin dakin take bina da harara, Sai da na tabe karamin bakina tukunna kafin na soma cewa wani abu a cikin zuciyata, na ce "Oho dai"._

~~~

_Somai-somai na dinga tafiya kamar wadda bata da lakka a jiki, domin dik haduwar da nake tunkahon nayi Yau, da naga tasu Yubra naga dik na koma kamar wata Kazar Allazi....._

*_—•«•ASALIN LABARIN•»•—_*

_Malam Mudassir, Shine cikakken sunan shi, Batoranken garin Sokoto ne, sai dai asalin shi daga karamar hukumar sokoto ya fito, wato (Dange shuni), Inda kasuwanci ya kawo shi cikin garin Birnin Kebbi, a nan ya hadu da Asma'u wato (Kaka) har suka sasanta junansu magana takai wajen iyaye suka shigo cikin, ba tare da bata lokaci ba akayi Auren._

...

_Cike da Soyayya suke more rayuwarsu cikin farin ciki tare da aminci da kaunar junansu, da dadi da akasin hakan._

~~~

_Bayan Shekara guda Allah ya azurtasu da samun karuwar Diya macce wadda taci sunanta da Balkisu, sosai suka bata kulawar da ta dace tare da saka ta Makarantar Islamiyya harda ta Boko domin ta samu ingantaccen ilimi wanda zata iya kula da kanta da kuma Ƴaƴanta Idan Allah ya kaddari tana dai daga cikin masu tsawon rai a cikin duniyar._

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now