P...11

523 68 0
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

             *P...11*

_Misalin 1:00am, na ji Mummy na kokarin tayar da ni daga wani hadadden baccin da nake yi wanda ke cike da Mafalkin Jin dadi._

                 _A hankali na bude idanuwana na sauke su gareta, Murmushi mai kayatarwa ta fara sakar man daga bisani ta jefoman wata tamabaya mai nuni da cewa "Kina jin fitsari kuwa diya ta,". Kai, kawai na iya gyada mata alamun "Eh", domin ko kadan baccin bai ida saki na ba._

                _A hankali taja Ni har Izuwa toilet din  tare da nuna man yanda zanyi, taja man kofa ta rufe, sai da na gama lalura ta sannan na fito,_

              _A nan bakin kereriyar gadon na sameta zaune  tana jirana._

                  _Kai tsaye na sake komawa saman gadon na kwanta, sannan ta gyaraman kwanciyata, daganan kuma bansan lokacinda na tayas ba._
               _Ban sake falkawa ba sai da Subahim da Tazo ta sake tayar da ni na yi wanka sannan na yi  Alwallah, da yake  Akwai masallaci a gidan muka bi jam'i._
             _Dik da ni wadannan abubuwa na tashi tsakar dare ko kadan ban saba da su ba, dan ko Kaka ta tayar da ni Kirikiri zanki tashi ko kuma na saka mata kukan rashin son tashin._

                _Bayan mun gama Sallar ne, Dik na matsu naje na kwanta, sai kuma naga an bude wani sabon shahin, inda Mummy ta kawo mana littafai Hizob 5_5 na Alkur'ani muka shiga karantawa, sauran kuma suna bitar karatun su na Islamiyya._
              _A wannan lokacin kuka ne kawai banyi ba shima kuma dan babu yanda na iya ne._
                _Sai da Haske ya fara Bayyana ne,  na shiga yi ma Daddy Ina kwana Tare da Mummy da Ya Fadil da Aunty Intisar harda su Yumra, bayan an gama gaisawa ba tare da an sake yin wata firar ba kowa ya nufe part dinshi,   Ita kuma Mummy ta ziyarce Kitchen ta hada mana kayan breakfast._

      _Ina komawa bedroom na dale gado, daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba._

                 ~~~

  _10:00am, Mummy tazo ta tayar da ni nayi wanka na sake canza tufafin dake jiki na._

               _Komai dai cikin  mamaki nake zautar da shi, domin naga alamun su rayuwarsu ta daban ce dik da bansaba da wasu abubuwan ba, amma haka nake Kwikwitawa nayi dan nima ina son na zama kamar su._
               .....

_Bayan mun fito Babban Palour anan muka same su Yubra zaune a saman dogowar kujera guda dake mahe a dakin, kamar gunki._

              _Suna gani na, suka mike tsaye cikin farin'ciki suka jawo ni na zauna kusa da su,  tare da yiman ban gajiya, nima dai biye masu nayi  na mike kafafuwa na muka wataya, ita kuma Mummy direct Part din Daddy ta nufa._

           ~~~

             _Wasa-wasa  yanzu kusan Sati na guda cif a gidan._
                 _Sosai na fara sabawa da wasu abubuwan musamman tashi tsakar dare na yi fitsari da kuma Subahim._
                _Ɓangaren  Kaka kuwa babu ranar da bamu waya.!    Tsakanina da 'yan gidan kuwa farin ciki babu irin wanda basa bani._
            _A bangaren Mummy kuma Idan naga zata shiga Kitchen ita da Yan aikin gidan nima sai na biyota  domin na tayasu, sabida abinda na fuskanta,  kusan dik rabin aikin kitchen din ita ke yinsa, idan su Yumra na gidan suma suna kamawa harda Aunty Intisar, dan ita ke matsa masu dik da suma naga har sun saba._

           ~~~

_Cikin Sati na biyu aka shirya man komai na makaranta, inda a makarantar boko direct aka kaini primary6, Islamiyya kuma aka sakani Class3, class din da su Yumra suke kasan cewar inada Hizob10 ga kai (wato harda) kullum Direba ke kaimu kuma ya dawo da mu._

              ....

            _Sosai nake ganin canjin yanayi ba irin wanda na saba da shiba, sannan na samu ingantacciyar rayuwa irin wadda nake fata._

              _Bayan Wata Guda; abubuwa da dama na fara fahimtar su, musamman bangaren karatun Boko dana Islama, wanda dik inda nake gargadar iyawa su Yumra ke daura ni a layi._

      _A bangaren Ya Fadil kuwa tun lokacinda muka cikin sati na ukku ya koma Skull, kasan cewar futun su ya kare,_

                ~~~

            _Bayan Wata Ukku; Misalin12:30pm,  koda na tashi daga baccin ranan da nayi, kasan cewar yau ranar weekend ce, ba makarantar Boko kuma Islamiyya anyi mana hutu na 1week,_

    _Koda na fito waje naga Mummy sai famar buleken aiki take tare da yan aikin gidan  babu kakkautawa,  ganin banga su Yumra a wajen ba yasa naje wajen Mummy Kai tsaye na tambayeta kamar haka,   "Mummy baki zamuyi  ne?"_
                   _Murmushi shimfide a fuskarta ta ce "Yannen ki ne zasu dawo gida yau daga wajen karatu". Cewa da (Ya Abir da kuma Ya Bikhram)_
                 _Wata irin tsuwace kulululu naji cikina ya yi wanda sai da nakai na dahe shi, a guje na ziyarce toilet ba tare da na tsaya bata amsar komai ba._

                 _Itama ci gaba tayi da aikin dake gabanta dan kar su makara,  sabida suna sa ran zuwa 7pm zasu  sauka._

          ~~~

_Karfe 4:00pm,   Wata jahilar mota ce da akayi horn daga waje, Mai gadi ya tashi a hanzarce ya wangale mata get ta shigo, Direct Parkin space aka nufa da motar, kafin matukin wannan motar ya kaiga fitowa dik hankalina ya dunguma izuwa wajen._
               _Nan take naga fitowar wata matashiyar budurwa wadda shekarunta ba zasu wuce na Aunty Intisar ba, Itama  fara'ce sosai, kuma tana da kyau iya gwargwadon nata, sanye take cikin doguwar riga ta  atamfa Baka mai zanen pitch color a cikin ta, da bisa dan guntun mayafin dake yafe a saman kokon kanta har izuwa takalunman ta da yar karamar jakar dake hannunta tare da agogon dake make a tsintsiyar hannunta dik pitch color ne, sai dai ko kadan ba wani jiki ne da ita ba._

           _Kinkime da akwatinta a hannu ta ida karasowa wajen mu, a guje su Yumra suka je suka tarbota tare da yi mata Oyoyo suka amshe akwatin dake hannunta, sannan taje wajen Mummy suka gaisa cikin kulawa._

             _Sai dai wani abin mamaki, muna  Ido biyu da ita naji ko kadan bata kwanta man arai ba, haka itama a yanda ta nuna man domin da harara take kallona harta ida shegewa cikin Babban Palour._
             _A nan ta samu Aunty Intisar zaune tana dannar Laptop dinta, kirar (Apple MacBook)._
                  _A hanzarce naga wannan budurwar ta maza ta fauce wannan Laptop daga hannun Aunty Intisar wanda hakan shi ya dawo da hankalinta wajen, cike da tsantsar farin ciki, suka rumgume junansu fuskokin su dauke da annashuwa,  sannan suka kwashe tarkacensu gabadai suka nufi Part din Aunty Intisar._
            _Yumra dake shirin daukar kayan Littafainta da ta gama Assignment da su, nayi hanzarin karasawa wajenta na dan lafceta kadan na ce "Ke wai wannan wacce Kazar ce?"_
              _Cikin rashin fahimtar inda zancen nawa ya dosa, ta ce "A ina kuwa Fatiti"_
                      _Kai tsaye na ce "Wannan Matar mana da ta zo yanzu"._

                _Ai ko sai da ta tuntsure da wata arniyar dariya Kafin ta bani Amsa ta ce "Aunty Khairat'ce fa, diyar Yayan Daddy'nmu, Ita ce wadda aka zabama Ya Abir, da ta gama karatun Degree dinta na farko, za ayi auren"._
*Follow me on wattpad and vote— Smart_Feenert*
               *Be smart*
                      *Pls shere*

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now