P...21

478 64 8
                                        

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

               *P...21*

Sai da ya kalli wannan belt d'in dake hannun shi da kyau wanda su ma shi suke kallo sannan ya maida duban shi gare su ya ce
             "Ance lokacin da wannan abin ya faru ku kad'ai ne a cikin gidan sai 'yan aiki..!"
               Cike da wani mugun tashin hankali ko waccen su ta gyad'a mashi kai alamun eh
                Cikin wata tattausar murya wadda tafi kama da ta mugunta ya ce
             "Amsar tambaya ta nake buk'ata.!"
                   Cikin rawar murya ko waccen su ta amsa mashi da
                  "Eh.!"
      Sannan ya kara tambayar su da cewa
             "Shin ko kuna buk'atar ku likkid'u tuburan a hannu na ne?.!"
             Cikin sharce zufa mai had'e da ruwan hawaye tare da makarkatar murya suka amsa mashi da
           "A'a"
Ya ce
             "To ina jin ku.!"

Aunty Intisar ce ta soma yi mashi bayani cikin Inda-inda tare da bid'ar shashashe zancen, kafin ta ankara tuni taji saukar wannan mugun belt a jikin ta
      Ko da Aunty Khairat  ta lura da hakan cikin wani mugun firgici ta mik'e tsaye da niyyar tsiratar da lafiyar jikin ta kamar farar kura, aiko nan take ya dank'o hannun ta da k'arfi ya jefa ta wajen da Aunty Intisar take daganan ya shiga jibgar su gabadai kamar Allah ya aiko shi.
       Kuka suke suna ihun neman taimakon gaggawa a wajen mutanen gidan sai dai hakan ya gagara domin ko da wasa ba wanda ya yi yunk'urin zuwa wajen da suke domin taimakon su dan dik wanda yazo sai dai ya yi tsaye yana kallon Game.
       Nan dai Ya Bikhram ya haura sama ya tado Daddy suka dawo wajen, wanda hakan ya sa cikin wani mugun tashin hankali Daddy ya tunkare wajen da Ya Abir yaje domin dakatar da shi amma hakan ya cutura domin ya kasa
             Kai tsaye Daddy waje ya fito yana neman k'attan da ke aiki gidan domin su kawo d'auki sai dai ko da suka zo har su Aunty Intisar sunyi Suman karfin hali sannan jikin su ko ina ya ji masu wani mummunan rauni,
               Salati Daddy ya fara ja tare da sauke haushin abin ga Ya Abir wajen yi mashi fad'a sosai sannan ya wuce part d'in shi
            Daganan kuma kowa da ke wajen ya yi nashi b'angaren, haka shi ma Ya Abir ko kallon wajen da su Aunty Khairat suke bai yi ba dake kwakkwance a saman center carpet rai a hannun Allah.
                Shi ma wucewa ya yi part d'in shi domin ya watsa ruwa
              A take 'Yan aikin gidan mata suka bayyana a wajen da su Aunty Intisar suke cikin tashin hankali, wanda daman suna a lab'e a lokacin suna kallon abin da ke wakana
              Wasu daga cikin su kuwa dariya suka fara tuntsirewa da ita kafin suyi wani yunk'urin ziyartar wajen da Fridge ya ke suka fiddo k'ank'arun ruwan sanyi a ciki sannan suka samu bokiti babba guda suka zuba ma ruwa tare da jefa wannan k'ank'aran a cikin ruwan sai da suka tabbatar da ruwan sun d'au raba sosai sannan gabadai suka juye masu su a jiki.
           Firgigit ko waccen su ta falka tare da mik'ewa zaune cikin sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sai dai ganin ko su waye suka yi masu wannan mummunan wulakancin ko waccen su ta sake fashewa da kuka tare da mik'ewa tsaye suka shiga jibgar wad'annan 'Yan aikin kamar Allah ya aiko su domin jidda haushin su gare su
                   Su kam dariya suka b'arke da ita tare da guduwa suna shigewa d'akunan su suna gark'amewa da key tare da maida su kamar wasu kasungumen mahaukwata.
            Nan dai Aunty Khairat da taga abin ya fara zama rainin wayo ta dawo cikin babban Palour'n tayi tsaye ta shiga  banka zage-zage tare da alfasha iri-iri kala-kala harda su Allah ya isa, da taga alamun ba wani wanda ya kula da ita
             Aunty Intisar ma part d'in su ta koma domin ta kakkanta jikin ta dan ta fuskance dik zagin da Aunty Khairat ke yi sai ta saka iyayen su a ciki, sai dai koda hakan bata ganin laifin ta domin ita ma da tana da hali da ta biye mata sunyi tare.
                   A fusace Aunty Khairat ta koma part d'in su ta shiga Kakkantar kayan ta gabadai sannan ta d'auki mukullin motar ta ba yare da tayi ma kowa sallama ba ta bar gidan a takaice cikin k'unar da zuciyar ta ke mata
                Direct gidan su ta nufa, Mai gadi na wangale mata get a fusace ta fad'a ciki ko parkin bata tsaya gyarawa ba.
           Kai tsaye Gadina ta nufa domin ta san anan kad'ai zata iya samun Ammie yanzu.
                  Nan take ta tsinkanyo ta gincire a saman wani makeken Carpet, ta aza gwiwwar hannun ta a saman Titmayya tana guntsurar Apple a bakin ta tana tauna cikin isa da tak'ama

             Zubewa tayi kwance a saman jikin Ammie tana fitar da wani sautin kuka mai cike da k'unar rai.
            Cikin wani irin mugun tashin hankali Ammie ta d'ago ta zaune tare da tallabo fuskarta sama wadda dik ta gama lalacewa da jini kamar abin da aka yanka da wuk'a ta ce
               "Baby me nake shirin gani haka ne? Had'ari kika yi ne ko kuma me?.!"
           Kafin Aunty Khairat ta kaiga bata amsa tuni ta sake duban jikin ta dake kwald'e kamar sassak'in Icce, cikin tashin hankali ta kara cewa
             "Ke naga gabadai dik jikin ki jini ne kamar shaud'in bulala, gayaman wani shegen ne wanda uwar shi tayi asarar haifo shi duniya ya yi maki hakan.?"
                 Cikin wani matsanancin kuka ta kwashe komai ta gaya mata.
             Wata dungureriyar Ashshar ce Ammie ta fara ja kafin ta mik'e tsaye cikin wani bak'in bala'i ta nufe part d'in Abba.
         Shi ma a yanda ta sanar da shi ko k'adan baiji dad'in abin ba amma hakan ya daure ya shiga kwantar ma Ammie da hankali a kan tayi hak'uri tabi komai a sannu har a gano inda bakin zaren ya ke amma firrrr tak'i yarda nan take ta dawo part d'in ta ta d'auki mayafin ta tare da makullin motar ta sannan taja Aunty Khairat suka fita.
                Direct Asibitin da muke suka nufa
                 Suna isowa  a nan wajen shan iskan dake cikin harabar Asibitin bayan d'akin da aka kwantar da ni suka same Mummy ita da su Yumra suna shan Iska domin a cikin d'akin da nake, Doctors ne shak'e a ciki suna k'ara yi man wasu gwaje-gwaje dan k'ara tabbatar da lafiyar jiki na.!
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*^Pls shere^*
More Comments
More Typing 😉

'YAR BALLAJJA'UWo Geschichten leben. Entdecke jetzt