P...35

305 61 16
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•BE-SMART•»•—*

*_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

P...35

Ko da na gama wanka na fito daga bathroom d'in jin shiru ya sa na d'an gincira saman gado ina tunanin ta inda zan juya kaina na ga maih dan na shafa ma jikina nan dai hankalina ya kai ga wajen mirro na mik'e zumbun na nufi wajen sai dai ba abinda na iya gane kanshi a cikin kayan kwalliyar dan ko wannensu matsayin bak'o yake a wajena, tunanin ta inda zan fara na soma yi kafin nayi yunk'urin tab'a wani abu a wajen naji an bud'e kofar bedroom d'in wanda har a cikin zuciyata naji dad'in ganinsu ba tare da sunce da ni ko k'ala ba kamar yanda ni ma bance da su ba, kai tsaye naga ko waccensu ta kama nata b'angaren inda biyu suka shiga gyara man gashin kai na dake banye sauran kuma suka shiga yi mani kwallayi cikin d'an k'ank'anen lokacin suka gama komai wanda ni kaina ba k'aramin tsorata nayi da hikimar da Allah ya basu ba, mirror na kalla naga na koma kamar ba ni ba wanda hakan ba k'aramin mamaki da kwankwanton asalin wace ce mai wannan fuskar ya sakani ba dan a yanda nake gani kamar ba ainahin fuskata ba ce. Su Ammie na isa wajen Boka a rikici suka fito cikin mota kamar wad'anda aka koro suka fad'a cikin kangon Boka, Ammie ce ta riga kowa shiga ciki a hanzarce inda ta cimma shi zaune a saman wundi yana kwarara ruwan ashshar, a rikice ta zube wajenshi da cewa "Baka ka cece ni! Ka cece rayuwata Boka, Khairat ta kaini ta baro.!" ta k'ark'are zancen ne a dai-dai lokacinda su Hajiya Maryam ke k'ok'arin shigowa ciki, cikin rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa dikansu suka zazzauna a k'asa kamar almajiran gidan Malam Jabiru, sake da baki suke kallon Ammie da kukan da take sharb'a har yana son ya ci k'arfinta inda take cewa "Boka assirina ya gama tonuwa, mun turbud'e yarinyar amma mun manta bamu saka wannan layar ba! wayyo Boka ka cece mu dan darajar sihirinka da muk'amin da k.........!" tsawar da ya daka mata ne kamar saukar aradu ya sa hantarsu kad'awa, a tsawace Boka ya tsoma tsine masu albarka tare da zage-zagensu ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sannan ya kara da cewa "Allah ya d'ebe ma Khairat albarkar dan matsalar dukansu ta shafa domin shi ma umarni yake bi.!" cike da wani mugun tashin hankali Ammie ta ce "Haba Boka ya zaka tsine mata albarka dik da kasan addu'ar uba ga d'a kamar lalle take a gareshi!." a rikice Khairat ta ce "Ammie meye had'ina da shi da zaki ce haka.?" Ihun da suka ji Hajiya Maryam tayi ne ya yi hanzarin dawo da hankalinsu wajen inda suka ji a tsiwace take cewa "Wlhy ba zai yu ba! inaaa!!! Na rantse da Allah ba zata sab'u ba bindiga a ruwa.!"  a hanzarce ta yo wajen Ammie  ta wanketa da wani wawan mari tare da tsine mata albarka inda ita ma Ammie cikin zafin nama ta samu nasarar mik'ewa tsaye ta kame mata wuyan riga daganan fad'a ya kicime suka shiga buga wani zazzafan dambe a wajen, wani mugun shuri ne Boka ya yi k'arfin halin d'auke Khairat da shi wanda hakan ya saka ta buga wani irin rikitaccen ihu, Ammie na jin hakan ta cilla Hajiya Maryam wani gefe tayo wajen Boka cikin wata shashshek'ar wahala ta ke ce mai "D'iyarka ce fa ta cikinka.!" wata zankad'ed'iyar alfasha ce ya fara zuguro mata kafin ya ce "Allah ya k'ara tsitstsine mata ya had'ata da bala'in yau da na gobe da dikkannin shairin da na shuka a fad'in duniyarnan ya dawo kanta.!" a rikice Ammie ta dank'o wuyanshi cikin fita a cikin hayyaci sai dai kafin ta kai ga aikata wani abin tuni taji an cillota waje da k'arfi sai da faffad'an goshinta ya buge malama k'asa, a rud'e Khairat ta nufe wajenda take ta shak'o mata wuya cikin rikicewar da idanuwanta suka yi take fad'in "Abinda naji gaskiya ne ko k'arya? ki gayaman.!" yanda ta shak'e ma Ammie wuya takin nufashin ma na son gagararta kai tsaye taji Hajiya Maryam na ce mata "Bacin ke d'iyar Boka ce ba ta hakanan kad'ai aka barki ba! Ke shigiya ce ma'ana wadda aka haifa ta hanyar fasik'anc...!" "A'aaaaaaa" ihun da Khairat ta saki kenan a lokacinda taji wannan mugun furucin da Hajiya Maryam ke yi akanta nan take ta sake Ammie daga shak'ar da ta yi mata ta hiranyo saman jikin Hajiya Maryam daganan suka shiga fafatawa, Ammie na ganin ankai Hajiya Maryam k'asa tayi hanzarin tashi daga wani wangalelen kwancin da ta yi ta dank'o wuyan Maryam daganan ita ma Allah ya bata nasarar mik'ewa tsaye suka shiga fafatawa, Boka kam gefe ya koma yana kiran fatalwarshi.  Lamarin su Abba ba k'aramin d'aga hankalin Police d'in ya yi ba domin dik wani kwakkwaran binciken da aka gabatar a wannan lokacin ba asamu wata takamammiyar rashin lafiyar dake damunsu ba wanda hakan ya sa kai tsaye Police d'in suka  d'auke su Izuwa wajen wani babban Malami dan ganin suke idan ma aka kwana kamar sun k'ara ma kansu wani sabon aiki ne inda harda Ya Abir suka d'auka su Intisar kuma suka maida su gida inda anan ne suka samu labarin dawowar su Ammie a wajen Baba mai gadi inda Police d'in suka neme ganinsu Mai-gadin ya gaya masu basu wani jima da dawowa ba suka sake fita wanda hakan ya sa DPO zargin wani abu a rai ne sai dai bai bari kowa ya lura da hakan ba amma dik da hakan ya bar masu sak'o wajen mai gadi da cewa idan sun dawo yana buk'atar ganinsu a Office d'inshi........
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shared

'YAR BALLAJJA'UDonde viven las historias. Descúbrelo ahora