P...14

421 61 4
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan na kasa_*
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

_Assalamu Alaikum My fan's ina mai baku hakuri a bisa jina da ku kayi shiru, dik da na gaya maku uzuri na amma ganin yanda kuka damu da wannan buk sosai yasa na yanke hukuncin yi maku wannan page domin faranta maku kamar yanda kuke kokarin faranta man._
_Ina mika sakon godiya ta ga wadanda suka turoman sakon text message da kuma masu biyo ni ta Private Chat da masu yi man magana a grps dik ina godiya a gareku Allah ya bar kauna Ameen_

*P...14*

_Cikin rashin kwarin jiki da takaicin dake damun zuciyarta ta bude wayar ta shiga wajen text message, sai dai ganin abinda Aunty Intisar ta turo mata yadan saka ta farin ciki kadan amma koda hakan tunaninta da hankalinta dik sun tattara izuwa wajena._
_Bayan ta gama karantawa ta ajiye wayar a gefe ba tare da ta maida mata da amsar komai ba, Sannan tadan kifa kokon kanta a saman kafadar Aunty Intisar dake kusa da ita kamar wata karamar yarinyar dake shan Nono, hadi da furzar da wani zazzafan iska wanda yafi kama da na bacin rai.!_

_Kulhuwallahu Ahad, kafa ukku, tare da salatin annabi da bansan iyakar wanda nayi ba, na tura kofar cikin kwancewar brain da niyyar budewa,_

_"Gufffffff" kawai naji kofar ta bani amsa dashi, wanda hakan ba karamin tsorata na yi ba da jin wannan mugunyar kabra da nayi ma wani abu dake shirin fitowa wajen kamar dutsi._
_Nan take na fara yunkurin guduwa domin na tsorata hanikan, sai dai addu'ata guda ita ce "Allah Yasa ba Ifiritu Shugaban aljannai ne na buga ma wannan makekiyar kofar ba" dan nasan karyata ce ta kusa karewa idan har ya kasance abinda nake tunanin ne._

_A tsawace naji ance "Tako guda idan kika kara anan wlhy sai kin raina kan ki, ke har kin isa ki kabre mutum ba dutsi ba ko hakuri babu sannan kiyi yunkurin guduwa, tukunna ma ke wacece? Kuma me ya kawo ki a gidannan? Me kuma kike yi a part dina?._
_Cikin rawar murya na soma yi mashi bayani kamar wata yakutacciyar almajira, na ce "dama Mummy ce, ta ce nazo na kiranyo ka..!"_

_"Dan kina wa?_

_Na ce, "a'a ni ba haka nake nufi ba.!"_

_Ya ce "Kamar na me? Tukunna ma kinfi karfi ki juyo ki kalleni ne kiman magana?."_

_Kai kawai na iya girgiza mashi tare da juyo Ustaziyyar fuskata ta wajen shi kamar yanda ya ce_
_Bakinshi kawai naga ya tabe cike da miskilanci Ya ce "Awww daman ke ce rigimammiya, saukar yaushe kuma?"_

_"Nadan jima anan" amsar da na iya bashi kenan a razane. Juyawar da zanyi da niyyar barin waje cikin hanzari,_
_A takaice Naji ya danko hannuna guda da karfi kamar mai shirin fince shi, Ya ce "Ina zaki tafi bacin ban maki hukuncin da ya dace dake ba?"_

_Wani kuka ne naji ya yi gaggawar kubce man kai tsaye ba tare da ya yi man sanarwar zuwanshi ba, Na zube kasa ina bashi hakuri domin ban mance da irin muguntar da yake da ita ba..!_

_Mummy da taji shiru ko kadan babu alamun zuwan mu a wajen, yasa ta ce ma "Yumra taje ta kiranyo mu"_

_Aiko dajin Hakan Aunty Khairat ta mike tsaye ko kunya babu ta ce "abari taje ta kiranyo shi"._
_Ba tare da tunanin komai a rai ba Mummy ta ce "To badamuwa tana iya zuwa"_
_A hanzarce tayi kuzut ta mike tsaye cikin wani uban sauri ta soma tafiya kamar ta tashi sama, Aunty Intisar kuwa sai dariyar cikin makoshi take binta da ita kamar zararriya tare da nema mata sauki a wajen Ubangiji._


_D'agani Ya yi sama kamar wanda Ya d'auki wani Jaririn abu tare da tsare ni da kwala-kwalan fararen idanuwansa masu cike da daukar hankali had'i da Jifa na da wani wawan kallon shi kamar ya cinye ni, sai dai a yanda hadaddiyar fuskar shi ta nuna Jin yake kamar ya wullar da ni a saman bangon d'akin har sai na dauke huta tukunna, amma a cikin kogon zuciyar shi wani tunani ne yake na daban wanda ya dade Ya na muradin kasantuwar shi koda zai dade yana bata mashi lokaci._

_Nima tsura mashi ido nayi kamar wata karamar Mage (Mussa) domin na riga da na sadakat hukuncin kawai nake jiran ganin afkuwar shi._

_"Macuci bak'in Azzalumi, daman abinda ya tsaidaka kenan anan?". nan take naji ta fashe da wani fitinannen kukan da ni kaina ba karamin tsorata nayi da jinshi ba, cikin kururuwa kamar Zakin da ya samu nasarar danke Barewa ta shiga tunkarar wajen da muke dauke da fuskar mai shirin daukar rain makiyin shi.!_

_Wasu hadaddin yawu ne naji nayi karfin halin hadiyewa tare da neman kwace kaina daga gare shi kafin ta ida kawowa daf da mu, domin hankalina bai ida tashi ba sai da na sake maida duba na a gare shi, naga har yanzu da irin fuskar dazun ce ya ke kallona, na rasa inda zan saka kaina Makiya biyu sun hade man a waje guda,_
_Bakin da nake kokarin twalewa ne dan sakin ihun neman taimakon gaggawa naji Ya yi hanzarin hadewa da nashi waje guda ya game gammmm kamar cingan, a dai-dai lokacin da Aunty Khairat ke kokarin kawowa daf da mu......!_
_Ban maku alkawarin ganin typing d'ina kullum ba☺️, kuyi hakuri da wannan pls_
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*Be smart*
*^Pls shere*

'YAR BALLAJJA'UOnde histórias criam vida. Descubra agora