*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*_" Munafukar Allah". Ita ce kalmar da tayi gaggawar fitowa daga cikin bakinta, ba tare da ta kara cewa ko uffan a bisa wannan kalmar ba, domin tasan ko zata kwana anan tana cewa na fito ba fitowar zanyi ba sai naga dama,_
_Nan take naga ta zulo hannunta guda ciki tana kokarin janyo Ni waje, dan bata iya shiga cikin karkashin gadon,_
_Aiko a hanzarce na kauce daga wannan gefen na fada wani gefe, a daidai wannan lokacin taji takai hannunta guda tsumbulbul a cikin wata kwallar dake cikin karkashin gadon,_
_Jin babu zato babu tsammani ta danko wani abu a cikinta kamar dutsi wanda ta kasa gane ko ajiyar mene a ciki, yasa a hanzarce ta jawo wannan kwallar, daga nan kuma aka manta da batun dukan da za'ayi man, naga ta kinkime kwallar gaba dai, ta bude dakin ta fita,_
_Mai bakin kara kuwa ana nan palour an kasa zaune an kasa tsaye jiran de ake aji alamun fitowar ihuna waje Ina shan wani likkimin duka, sai kuma a kaga akasin hakan,_
_Cikin mugun rashin jin dadin wannan bakin al'amarin da ya kasance haka ta ce "Inna kuma me aka raramo haka cikin kwallar?"_
_Kaka ta ce "Wallahi Talatu wata tsohuwar ajiya ce da ni kaina na kasa gane ko minane a ciki, kinga kama man na ida fita waje da ita daganan mu duba koma menene"._
_Cike da mugun jin haushin canzawar akalar Rakumi, Gwaggo Talatuwa ta kama mata suka ida fitowa cikin haske,_
_Sai dai ko kasa basu ida kai wannan kwallar ba, ganin ko ma menene buru-buru da hasken da Ubangiji yayi mana ni'ma da shi yasa Kaka buga wani Musulmin Salati, ita ma Mai bakin kara, taya ta tayi suka dauka tare suka aje tare_
_Amma a mamakin ku Fan's me suka gani?,_
_Wasu Hatsine da Kaka ta jima tana tanadi, sun kai wajen kwano biyar, saboda wani gudurinta na bidar fara sana'ar fura idan ta samu lokaci, amma gabadai sunyi hunhuna sun lalace ta sanadiyyar fitsarin da nake yawan yi a saman gadon,_
~~~
_Ni kuma tun lokacin da naga Kaka ta dauke wannan Kwallar ta fita waje, nima na rufa mata baya sai dai na tsaya palourn ne ina sauraren dik abin da suke tattaunawa akai,_
~~~
_Nan take Naji dumin Kaka ya fara canza kala izuwa fari yana kokarin komawa baki, dan dik sanda rainta yayi mummunar baci to dumminta ma kala ya ke canzawa, sai fadin take daga yau na daina fitsarin kwance domin yau ba wanda ya isa ya amsheni a hannunta sai Allah,_
_Wanda hakan yasa, Mai bakin Kara ta shiga kara karfafa mata gwiwa tana kara zugata akan "karta ragaman ko kadan, ta tabbatar da ta ci kaniyata daidai wa daida yanda fitsarin kwancen ma idan ance na sake yi zance na tuba, kuma ta kafe da hujjarta marar kan gado harda su rantse rantse tana cewa " dik da gangan ne nake yi mata fitsarin kwancen dan naga ana kyaleni ne ba'a hukunta ni".__Aiko Ina jin hakan nayi kuzut na fito daga cikin dakin domin nasan idan har na bari Kaka ta rutsani a ciki dakin ba zata yi man da kyau ba, ba tare da sun ga fitowa ta daga cikin dakin ba, kawai sai ganin su kayi na durkushe kasa kamar zakara nabi ta OCn Gwaggo Talatuwa na tayas ina kokarin fecewa daga cikin gidan gabadai, ko da Kaka ta ankara da hakan tayi karfin halin biyoni a guje, itama Mai bakin kara mara mata baya tayi dik dan a samu nasarar danke Ni._
_Sai dai kashhh! Domin rashin sa'ar da suka yi, ita ce, ko da suka iso bakin kofar fita garka, har nabar wajen dan ko kurar tashin iska Na basu samu gani ba, cikin shashshekar wahala ko waccen su ta dawo cikin gidan cike da kunar da zuciyar su ke yi musamman Gwaggo Talatuwa da take jin kamar ta fashe da wani fitinannen kuka akan haushi, ita kuma Kaka kamar ta aza hannayenta biyu a saman kai ta sake ihu a kan bakin cikin rashin sa'ar danka ta da ba'ayi ba,_
~~~
_Ina barin gidan, ban san lokacin da na tsallake Titi ba, ina ta famar sharbar guda bana ji bana gani kamar wata sakakkar Akuya, kafin na Ankara, sai jin nayi kaina ya kabru ga wani gundumen abu kamar dutsi,_
_Tadda kaina sama kadai ke da wuya naci karo da wani garsakeken mutum dik yabi ya kumkume fuskarnan kamar kashin jaki,_
_Ai ko tun yanda naga hakan na juya baya na koma hanyar dana fito, dik da ina jin irin dungureren zagin da wannan garsakin mutum ke jifana da shi amma hakan bai hana man ci gaba da abinda nake yi ba, hanikan akan firgici kamar wata firgitatta Mage,_
_Bansan lokacin da na dawo bakin garkarmu na tsaya ba, ina sauke wani zazzafan nishi mai hade da shashshekar wahala tare da yanke shawarar shiga cikin gidan dan komai ta fanjama fanjan, domin na kudurce dik Kaka ta buge ni a yau dinnan, Ni kuma nayi alkawarin saina Mirgide mata wuyan dan Talatalo ya sheka Kiyama, Ita kuma Gwaggo Takatuwa daman na kudurce ko bataman komai ba ita ma yau sai na jike katifarta ta mulki da ruwan sanyi, dan dole ta kwanta saman Ledar kasa ko kuma saman Tabarma Kamar Allajira,_
_Sai da na tofe ko ina na jikina da addu'a kamar wata malamar kwarai sannan nakai ga shiga gidan dauke da sallamata a baki daga bisani kuma na dauke wata waka ina rairawa, wadda daman ta zame mani jiki dik lokacin da nake jin wani miskilanci sai nayi nake jin komai ya daidai ta,_
_Tun daga nesa na tsinkanyo Gwaggo Talatuwa zaune a saman kujera a waje, ta buga wani uban tagumi kamar wadda aka yi ma rasuwa,_
_Muna ido biyu da ita ta tarbeni da wani Raki'in tsaki mai hade da harara Nima harararta nayi tare da juya fuskata gefe ina kallon wani wajen, sai can na tsinkanyo muryar Kaka a cikin daki tana waya tare da cewa Alhmdu lillah!" cikin dariya take fadin "Allah ya kawo ku lafiya"._
_Tana gama wayar ta fito waje, ko wajen da nake bata kalla ba, ta ce ma Gwaggo'Talatuwa, "Kinji gobe su Balkisu zasu dawo daga Dubai, kuma ta ce "jirgin Sokoto ne zasu biyo su kwana guda sannan su wuce Abuja,_
_Cike da wani irin hamshakin farin ciki, Gwaggo Talatuwa ta ce "Alhmdulillah!, Allah ya kawo su lafiya, kai amma naji dadi wlhy Alhmdulillah! Alhmdulillah!! Alhmdu lillah!!!." Ta karasa maganarta tana mai jifana da wani banzan kallonta wanda na kasa gane dalilin yinsa, sai can na tuno da maganar da naji Kaka tayi dazu, kafin na fara hango komai wani wazgegen mari na fara hangowa Ya Abir ya wankeni da shi ba tare da nayi laifin komai ba, dan ni har yanzu kallon baiwar Allah nake yi ma kaina😂, bansan lokacin da na fashe da wani banzan kuka ba ina yi ina jan majin... da karfi, kamar wata wawanya._
_Wata mugunyar tsawa ce da naji Kaka ta dakaman, ta dawo dani daga duniyar dana fada, a sannan na ankaro da ashe tunani ne nake yi,_
_Kafin in yi wani yunkurin cewa wani abu, tuni ta tarbe ni da fada tana cewa "Maza naje waje na samo mata wanda zai yanka mata kajin, a soya ma su Mummy Balki kafin su iso gobe". aiko tun yanda naji tayi maganar kaji na wartsake domin ko banza nasan yau dinnan zan sharbe harka._
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*Be smart*
*pls shere*
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...