P...20

466 53 8
                                    


*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*P...20*

Gudu nake yi a cikin wanin silisilin daji wanda babu komai a cikin sa sai kukan gawurtaccin Naman Daji.
Ina tsaka da yin wannan gudun ne na had'u da wata ruɓaɓɓiyar tsohowa zaune a saman wani wargajejin dutse, idanuwan ta a rufe gam kamar wad'anda aka saka ma super blue aka manne
Ba tare da na tsaya bin takan wannan tsohowar ba naci gaba da yin abin da nake yi,
Sai da nayi nisa sosai har bana iya hango inda na bari a baya, kafin na ankara sai ganin wannan tsohuwar nayi a gaba na tana tafiya a hankali rik'e da sandar ta a hannu,
Ba tare da fargabar komai a raina ba, naci gaba da sharb'ar gudun da nake yi afujajun,
Nan take kuma na sake had'uwa da wannan tsohowar a karo na ukku harta wuce inda nake cikin wata yak'utacciyar tafiyar da take ta marar lakka a jiki
Wannan karon kam tsoro mai tsanani ne naji ya bayyana k'arara a gareni mai had'e da rashin yarda da wannan tsohowar, nan take nayi ribas na juya baya na da sunan canja hanya ba tare da nayi yunkurin tsinana komai ba
Ban ankara ba naji na sake wani karo da ita a bayana nan take naga ta bud'e bakin ta kamar rabin gari tana k'ok'arin had'iye ni.
Wa'iyazubillah wata irin rikitacciyar k'ara ce wadda ni kaina ban san da na iya ta ba a wannan irin yanayi naji na saka daganan kuma ban sake sanin inda kai na yake ba...!

Naƙurorin dake jiki na ne suka soma tsuwa wanda hakan ya janyo hankalin gabadai ilahirin Doctors din dake k'ok'arin fita daga cikin d'akin da nake.
A hanzarce wad'annan Doctocin suka sake dawowa cikin hamdala ga Ubangiji Sannan suka fara gudanar da aikin su gare ni cikin kulawa.

A b'angaren su Daddy kuwa, su ma sun kasa zaune sun kasa tsaye dan tun lokacin da Doctors d'in suka sanar da su cewa numfashi na ya kasa dawowa suka neme annurin dake cikin zuciyoyin su suka rasa sai dai su ma jin wannan k'arar nak'urorin dake kaina ya sa suka tsintsi kansu cikin wani irin hamshak'in farin ciki tare da godiya ga Allah (S. W. A)

Kasancewar su ma su Mummy na nan zaune a bakin kofar d'akin da nake a saman kujerun dake wajen, su ma da jin hakan suka ji sun tsumduma-tsumdum a cikin tafkin farin ciki
Aunty Khairat kuwa haushi ne tam a cikin kogon zuciyar ta kamar ta buga
A hanzarce ta tashi daga wajen da su Ammie suke ta koma wani wajen na daban inda ba mai iya tsinkanyo ta sai wanda yasan da zaman ta a wajen, ita ma Aunty Intisar rufa mata baya tayi ta biyo ta suka zauna tare ba tare da ko wannen su ya ce da d'ayan ko k'ala ba.

Bayan kamar 2hours haka, d'ai daga cikin likitocin ne wadanda ke kula da Fatima, ya fito waje a dai-dai wannan lokacin kowa ya mik'e tsaye ya tunkari wajen likitan da niyyar jin abin da sakamako ya nuna
Ba tare da ya ce da su ko uffan ba ya ce su Daddy su same shi a Office dan Allah

Bayan sun isa office d'in ne kowa ya zauna tare da bada aron kunnayen shi ga Doctor suna jiran jin abin da zai fito bakin shi

Nan dai Doctor ya d'an yi gyara murya kad'an kafin ya soma kora masu bayani da cewa

"A yanda binciken mu ya nuna, wad'annan ruwan zafin da suka hau kanta sunyi mata mummunar illa a cikin jiki, domin kad'an daga jinin dake cikin jikin ta ya d'an samu matsala wanda dole sai an tace shi an saka mata wani.!"

"Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un, kad'ai Daddy ya iya cewa kafin ya ce
"Doctor to yanzu menene mafita?.!"

Doctor ya ce "Mafita d'aya ce Idan cikin ku akwai wanda zai iya bata jinin shi sai a saka mata, idan kuma babu sai a saya.!"

Nan take Daddy Ya ce "Idan nawa zaiyi a d'iba a saka mata.!"

Ya Abir ya ce "A duba nawa idan zaiyi a saka mata.!"

Shi ma Ya Bikhram ba'a barshi a baya ba wajen tofa Albarkacin bakin sa da sunan a d'ibi nashi a saka mata.

Doctor ya ce a je a duba na kowa dik wanda ya yi dai-dai da nata sai a saka mata

Bayan anje anyi gwaji Jinin, na Ya Abir ya hau dai-dai da nata aka d'iba sannan aka je aka ci gaba da kula da ita, Shi kam Ya Abir baya wani buk'atar k'arin ruwa ko kad'an Allura kawai aka mashi aka wuce wajen.

Sai misalin 6:30pm, sannan wasu abubuwa suka fara dawowa dai-dai dangane da Fatima sannan aka canza mata d'aki

Bayan komai ya lafa ne Daddy ya ce ya kamata su koma gida su d'an watsa ruwa sannan a dawo.

inda aka dunguma ga baki d'aya aka nufi hanyar zuwa gidan harda su Aunty Khairat, Mummy kad'ai aka bari a wajen sai su Yumra da suka kasa biyar su Daddy

Bayan sun isa gidan ne, kowa yaje ya yi wanka ya shirya aka fito babban Palour'n,
Ya zamana Daddy kad'ai ke Part d'in shi domin ya samu ya d'an gincira ko zai iya samun baccin minti talatin, dan dik a gajiye ya ke ranar yau.

Anan babban Palour'n ne Ya Bikhram ya yi kiran masu aikin gidan, bayan sun fito gabadai ko waccen su kan ta a duk'e suka rusuna har k'asa suka kwashe gaisuwa
Kai tsaye Ya Bikhram ya ce
"Yau wa ya aza ruwan zafi a cikin kitchen Misalin k'arfe 11:00am?.!"

Cikin girmamawa Ko waccen su ta ce "Ba ita ba ce.!"

Aunty Khairat da taga lallai idan bincike ya yi bincike su ne za'a tono, nan take ta dakatar da shi ta hanyar cewa
"Ni ko a gani na Ya Bikhram mutumen k'auye wa ya isa ya iya hana shi wanka da ruwan zafi koda kuwa lokacin zafi ne balantana a irin lokacin da muke yanzu! yana yuwa ma ita ce ta aza abin ta dan tayi wank......!"
Wani wawan kallo ne da taga alamun Ya Abir na bin ta da shi, ya yi hanzarin dak'ile mata dik wani kuzarin da take tak'amar tana da shi na makirci ta hanyar sark'ewar yawu, ta kasa k'arasa zancen cikin inda-inda tare da yin muii kamar wadda aka kulle ma baki da salatif

Nan take Ya Abir ya ce ma masu aikin su tashi su tafi
Bayan sun tashi sun tafi ne Ya maido duban shi ga Aunty Khairat da ta gama shiga cikin wata kwatar tozarta mai had'e da wani bak'in munafukin tsoro wanda take fatar rashin bayyanar shi a fuskarta dan kar a d'ago da ita, sai dai irin tsarewar da ya yi mata d'auke da dara-daran idanuwan shi masu matuk'ar d'aukar hankali tare da k'ok'arin gano abin da take k'ok'arin b'oyewa a cikin kwayar idanuwan ta nan take taji Cikin ta ya fara Zazzab'in ciwon kai.
kai tsaye cikin wata zazzafar murya taji ya ce mata
"Fad'aman yanda aka yi har hakan ta faru.!"

Cikin wata karkarwar murya ta ce "Bangane ba! Me kake nufi ?.!"

Ba tare da ya tsaya bata amsar komai ba ya mik'e tsaye ya shiga zwage belt d'in da ke manne a kugun shi
Ya Bikhram na ganin hakan ya tashi tsaye da hanzari domin dakatar da shi sabida gudun aikata b'annar da yake ganin yana shirin aiwatar wa domin yafi kowa sanin halin Yayan na shi sarai, sai dai kuma lokaci guda yaji gabadai gab'b'an jikin shi sunyi sanyi, ma'ana sun daina aiki, kitsen dake jikin shi kuma ya dask'ale ta sanadiyyar wani mugun kallon da yaga ya watsa mashi cikin wani irin mugun yanayi wanda hakan yasa ya shigo rok'on Allah da yasa abin yazo da sauk'in sabida ya san mai iya dakatar da shi a halin yanzu shi ne Allah.
Hankalin Aunty Intisar tare da na Aunty Khairat kam ya kai k'ololuwa wajen tashi domin ko waccen su tana da masaniya akan abin da zai biyowa baya rok'on da suke Allah ya sa Daddy ya sauko k'asa yanzu kafin mai afkuwa ta afku......!
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*Pls shere*

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now