*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*P...46
Haka b'angaren Fatima ma sosai suke jin dad'in zamansu da juna abin dai sai son barka. Wasu salihhan bayi ne ke kok'arin fitowa daga cikin masallaci a lokacin da suka k'ark'are sallar La'asar, sai da suka ci gaba da tafiya na d'an wani lokaci kamar ba zasu ce komai ba sai can d'ai daga cikinsu ya fara gyaran murya wanda hakan ya saka hankalin kowa dawowa wajenshi inda kai tsaye ya soma cewa "Wlhy wani lokacin idan ina tunanin wasu abubuwa a baya wasu su sakani kuka wasu su sakani jin haushi! Kai wani sa'in ma har dariya suke sakani har dai idan na tuna da lokacin da aka ma Jantali ssbuwar kaciya, wlhy a wannan lokacin dan muna cikin wani hali ne na halin k'ak'anikayi da Allah kad'ai ya isa ya hana man yin dariya.!" Nan ya sake k'yalk'yacewa da dariya kafin wani ya cafke maganar da cewa, "Ni kuma Chaki kasan abin da yake yawan sakani nishad'i idan na tuna da shi! Wlhy dik baifi idan na tuna da an tab'a maida farjinku na mata ba wlhy.!" Gaba d'ayansu suka saka dariya a dai-dai lokacin da ya dasa ayar zancen da yake, inda kai tsaye Oga Boss ya soma magana a hankali yana cewa "A gaskiya mun tafka tsiya a wannan lokacin, kuma har yanzu muna masu tuba a wajen Allah da kuma wad'an da muka zalumta, Allah ya karb'i tubanmu.!" gaba d'ayansu suka amsa da "Amin" tare da shafa addu'ar, haka dai suka ci gaba da tafiya suna zantawarsu cikin nishad'i da burgewa. A b'angarensu Ammie kuwa, a halin yanzu Ammie na gadon asibiti ta sanadiyyar Kansar da ta fito mata a farjinta dik ta lalata wajen ya rub'e wanda banda wasu bak'ak'en tsutsotsin da ke fita tare da wasu rub'ab'b'in ruwan k'urji ba abin da ke fita a wajen, inda bata wani jima a asibitin ba rai ya yi halinshi, sai dai kafin ta wulla k'iyama ta bar wasiya da a rok'an mata gafarar dik wanda ta zalunta, wanda rasuwarta ba k'aramin tsoratar da mutune tayi ba, sai dai kuma jin wannan rasuwar ta ta da su Abba suka ji kwatsam ya saka su yafe mata dik wani laifi da tayi masu, Hajiya Maryam kuma ciwon k'afafuwa ya motsa mata afujajun wanda sai da takai ga an yanke k'afafuwan gaba d'ai domin shi kad'ai ne mafita a wannan irin yanayin da ta samu kanta ciki. Alhaji Sulaiman kuwa lokacin da Abba ya yi aure a lokacin shi ma ya yi nashi, kuma suna cike da godewa Allah da ya azurtasu da sumun mata kyawawa masu kyawon halayya, abin gwanin burgewa. Ta b'angaren Papa kuwa su ma sunanan sai abin da yacci gaba, sannan kamar yanda Papa ya man alk'awarin ziyartar Takwarata akai-akai a wajena kuwa hakan ne ta tabbata dan bani sati ban ganta ba.
Bayan shekara hud'u.!
Abubuwa da dama sun faru musamman ma na farin ciki domin sunfi yawa a ciki.
Wasu kyawawan yara ne guda ukku wad'anda kana ganinsu ka ga 'yan ukku Maza biyu Macce guda wad'anda shekarunsu ba zasu haurawa 3 ba sai dai idan ba a sanar da kai ba zaka yi tunanin sun haurawa shekara 5 tsabar hutu da kwanciyar hankali ya zauna a jikinsu, aguje suke suna gudane-gudane a tsakar Palour'n wanda fitowar wata Mata ce a kitchen ya katse hanzarin wasar da suke yi suka nufe wajenta a guje suka rungumeta cikin nishad'i tare da kiranta da sunan da suka saba kiranta da shi, wato Nanny, (wato wadda ke taya Fatima rainonsu tun lokacin da aka haifesu take d'awainiya da su tamkar 'yaranta, shekarunta ba zasu haurawa 40 ba kuma sosai take kula da kowa a gidan kamar d'iyan da ta haifa a cikinta.!) inda cikin damuwa suka shiga yi mata gwalanniyar da suka saba mata sai dai ita dik da hakan tana gane yaren, inda suke cewa "Nanny galam😂Mammy.!" Murmushi ta yi cikin d'aurewa ta d'an tsakule hancin Maccen daga cikinsu wadda ita ce ta yi wannan tambayar, ta ce mata " Anny'ta! Mammy'nku na ciki tana shiryawa, ku zo mu je na d'ebe maku kayan Islamiyya na maku wanka na kaiku wajenta ta baku choooooocolate kafin Daddynku ya dawo ya kaiku ku sha ice-cream.!" Ihu suka saka gaba d'ayansu suka k'ara rungemeta takin sannan suka bita izuwa d'akinta kamar yanda ta buk'ata. 'Yan ukku d'in su Ya Abir kenan shi da Fatima wad'anda Allah ya azurtasu da samunsu cikin ikonshi, biyu Maza d'aya Macce inda d'aya ya ci sunan Mahaifin Ya Abir wato Mukhtar sai dai ana kiranshi da Khaleepha d'ayan kuma ya ci sunan mahaifin Fatima wato Mustapha sai dai ana kiranshi da suna Khaleel inda ita kuma Maccen ta ci sunan Mummy, wato Balkisu amma ana kiranta da suna Anny. Ma sha Allah! abin gwanin burgewa, idan kaga yaran tamkar d'iyan indiyawa, sannan kuma ko waye kai kallo guda idan kayi masu sai ka ji sun shiga ranka sannan suna bala'in kama da iyayensu musamman Anny idan ka kalleta dik Fatima ce ta d'auko haka su ma Mazan da ka kalle su ka ga Ya Abir sannan kamarsu da juna har ta ma b'ace dan su kam ta su kam-kam ce ma...
Bayan wata6: shagalin bikin Auren su Aunty Intisar da Ya Fadil ne ake ta famar zabga kamar ba a mutuwa, inda labarin aurensu ya gama zagaye duniya ga baki d'aya domin biki ne ake bana wasa ba, b'angaren Bak'i kuwa, ba wata mahaluk'iyar k'asar da bata turo wakilin da ya wakilce ta ba, domin ba k'asar da ba a san Daddy ba tun yana matakin Senator har lokacin da ya gaji da siyasa ya ajiyeta gefe, haka ma Abba domin shi ma ba a barshi a baya ba wajen bunk'asar da dukiyarshi ta yi domin dai kan yanzu arzikin bana ya ci uban na Dah har ana ik'irarin a cikin jerin masu kud'in Duniya ko bai shigo sahun gaba ba zai biyo bayanshi, abin dai sai hamdala ga Ubangiji. Inda amarya ta tare a gidan mijinta mai suna Sharafadding d'an gidan Minister'n man fetur na k'asa, wato Alhaji Shamsudding mai Dollars, b'angaren Events kuwa ba irin wanda ba ayi ba domin har Event d'in Dollars sai da aka yi. Haka shi ma b'angaren Ya fadil lokaci guda aka yi komai tare da na Aunty Intisar, inda ya je ya auro d'iyar Shugaban k'asar India, Innadillahi! tsayawa fad'in had'uwar da wannan hamshak'in bikin ya yi ma b'ata lokacin masu karatu ne domin sai da aka shahe wajen wata guda ana gudanar da shagalin bikin kamar ba zaya k'are ba, abin dai gwanin burgewa, a cikin gidansu wanda iyayensu suka mutu a ciki ya zauna da matarshi dik da babu yanda ba ayi da shi ba akan ya bari a k'era mashi wani amma yak'i ya nuna yafi son wannan gidan da dik wanda za a yi mashi, sai dai idan kaga gidan a yanzu yanda aka gyarashi idan baka sanshi yanda yake a Dori ba zaka ce gidan Shugaban k'asar America ne aka d'auko aka dire a Nigeria cikin garin Abuja. Abin dai sai son barka.
B'angaren Ya Abir kuwa shi ma arzikinshi sai k'ara yilwanta yake, inda ya kafe da sai ya gaje Mahaifinshi ta b'angaren komai ma musamman ta b'angaren siyasa, inda kai tsaye aka take mai baya ya fad'a siyasa, nan take ya fito da babban matsayi cikin d'an k'ank'ane lokaci da kuma k'ananan shekarunshi 32year ya lashe kujerar Minister na Abuja, wanda tun lokacinsu Yakubu Gawan ba a taba Minister irinshi ba kuma mai k'ananan shekaru irin na shi. Ma sha Allah abin gwanin burgewa, Fatima da Ya Abir da sauran mutanen gidan har sun manta da sunan wata mai suna Khairat, Allah sarki, idan muka waiwaya a gidan Yari kuwa, da Assubar Ranar Juma'a aka tashi da Jimanen mutuwar Khairat wadda ta girgiza gabad'ai ilahirin mutanen gidan gyaran halin inda a d'an zaman da su kayi da ita na wasu 'yan k'ananan shekaru har sun saba da juna sannan inda ta godewa Allah ba mai fad'in bak'i a gareta sai dai Fari, haka su ma su Abba suka ji rasuwarta kwasam inda su ma sun dad'e cikin jimamen abin har dai suka godewa Allah......................
"........TAMMAT BI HAMDULLAH
ABINDA NA YI DAI-DAI A CIKIN WANNAN LITTAFIN ALLAH YA SA MUTANE SU AMFANA DA SHI, KUSKUREN DA NAYI A CIKINSHI SABIDA K'ARAMCIN SANI ALLAH KA YAFE MAN KA YAFE MUNA BAK'I D'AYA!, AMIN YA HAYYU YA K'AYYUMU."
"DUKA-DUKA ANAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN SUNA DA 'YAR BALLAJJA'U! INA ROK'ON AFUWAR DIK WANDA NA B'ATAWA TA SANADIYYAR WANNAN LITTAFIN, ALLAH YA YAFE MUNA BAK'I DAYA AMEEN.!"
SAI MUN HAD'E DA KU A CIKIN SABON LITTAFINA MAI TAKEN SUNA DA "TSAKAR GIDA" INA GODIYA SOSAI A GAREKU MASU JIMIRIN BIBIYAR LITTAFAINA, NA GODE KWARAI ALLAH YA BIYA MAKU BUK'ATUNKU NA ALKHAIRI AMEEN, KU FUTA KAFIYA...."
Follow me on wattpad and vote @Smart_Feenert
FADINATUL-FIDDAUSI S/BAKI SOKOTO.
SMART_FEENERT
OR
BE SMART
IT's MY FAVORITE NAMES.Start on: 23/2/2020
End on: 30/12/2020SPECIAL THANKS 2U MY FRIEND's AND FAN's, THANKS VERY MUCH
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...