*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*P...39
Malam ne gaba muna biye da shi baya har muka shiga cikin gidan sallama d'auke ga bakunanmu cikin natsuwa, wanda hakan ya janyo idanuwan mutanen da ke wajen dawowa kanmu, sai dai ganina da suka yi dukansu sai da suka mik'e tsaye harda Alhaji Sulaiman, k'ok'arin gasgata abinda idanuwansu ke nuna masu ne suka shiga yi sai dai hakan ya gagara domin sun kasa gane ainahin gaskiyar abinda idanuwansu ke nuna masu, DPO ne ya shiga tunanin abinda CP na Prison ya fad'a masu na cewa "Allah ya yi man ckawa a cikin gidan yarin.!" wanda shi da kanshi ganau ne ba jiyau ba dan ya ga gawata da idonshi kafin a bawa su Ammie ita, murmushin cinnaka DPO ya fara yi kafin ya ce "Dama na san ai a-rina domin ko kad'an jikina bai tab'a bani cewa da gaske mutuwar ki ka yi ba.!" cike da wata mugunyar rud'ewa Abba ya ce "Ba a gidan gyaran hali aka ajiyeki ba? yanzu ya aka yi aka fito da ke Fatima?.!" Yumra ce ta fara fashewa da kuka kafin yubra Aunty Intisar kuwa kukan kura ta yi zata farmin Ya Abir ya yi hanzarin dank'eta, a dai-dai wannan lokacin ne wasu copra su biyu suka shigo gidan tare da Ya Fadil wanda DPO ne ya buk'ace hakan sabida ganin jikin nashi ya fara mirmijewa wanda bayan ya yi magana ne da Doctor dake kula da shi ya neme alfarma da a sallameshi Yau inda ba tare da wata-wata ba ganin jikin ya yi sauk'i sosai ya sa aka sallameshi d'in da yarjejeniyar Doctor'n zai dinga zuwa gida akai-akai yana duba shi. Ammie ce wadda tun d'azu gabad'ayansu bakunansu sun dad'e da mutuwa domin sun kasa cewa da kowa k'ala, hiranyo tayi sama a take da niyyar dank'ar wuyana, sai dai me? jin ta yi an d'ank'e mata hannu takin har sai da ta saki wata razananniyar k'ara wadda ita kad'ai ta san dalilin yinta, sannan aka wurgar da ita gefe tun daga wannan lokacin motsin kirki ma kowa ya kasa yi ganin Fatima tafi k'arfin dik wanda ke wajen zaune, wata tabarmar aka sake d'aukowa aka shimfid'a muna muka zauna a sannan Papa ya yi sallama da su Abba tare da musabuha, jin kaina dik ya yi man nauyi ya sa ni d'aga kaina sama da yake duk'e tun d'azu hawaye sun cika man ido, muka yi 4eyes da shi wanda sai da na ji gabana ya fad'in ridididi ta sanadiyyar wani mugun kallon da yake jifana da shi wanda na kasa gane ko na me ne, sai dai na fi d'aukarshi a matsayi mafi girma da ya ajiyeshi a cikin zuciyarshi, wato na k'iyayya, da hanzari na sauke idanuwana daga kallonshi na dubi wani gefe sai a sannan na halkanta da Khairat dake zaune gefe dik ta wani mak'ure kamar ba ita ba, tana bi na da wani wawan kallonta mai had'e da bak'in ciki zallarshi, lokaci guda kuma ta fashe da kuka tana fad'in "Ammie kin cuceni! wlhy kin zalunceni tsakanina da ke Allah ya isa, wlhy ban yafe maki hakkina ba duniya da lahira, Abba ashe daman ni ba d'iyarka ba ce.!" gun wajen ya yi na d'an wani lokaci, kowa sai sak'e-sak'e yake a cikin zuciyarsa, Ammie ce ta yi k'arfin halin katseta da cewa "Ubanwa ya gaya maki wannan banzar maganar.?" ta k'ark'are zancen ne cikin fuskar son kawar da zance, a tsiwace Khairat ta ce "Ya isa hakanan Ammie! wlhy ni na gaji! na gaji da wannan bak'in bala'in da kike jafani ciki, yanzu dik irin bak'ar wahalar da muka dinga sha akan bak'in halinku wato baki daddara ba har sai kin k'ara jefamu cikin wata? to wlhy ba dani a cikin tafiyarku ba.......!" cikin karkarwar murya Abba ya ce Khairat "Me kike fad'a ne haka! Ki dawo a cikin hayyacinki mana, ni ne mahaifinki ciki da waje kuma kowa ya shaida hakan! wai me yake faruwa ne, ni fa na kasa fahimtar komai da kuma dalilin zuwanmu wanan gidan wai me yake faruwa ne?.!" ya k'ark'are maganar ne cikin siffar tambaya kafin kowa ya bashi amsa tuni Khairat ta cafke tambayar da cewa "Abba baka san komai ba ne! dik da ni ma falkawa na yi kawai na same kaina a cikin wannan gidan a kwance sai dai ganinku da nayi ba k'aramin farin ciki ya sakani ba ta wata fuska domin na san Allah ne ya kub'tar da ni daga cikin bak'in bala'in da Ammie da kuma Hajiya Maryam suka sakani, a halin yanzu Abba mutuwa ce kad'ai maganin damuwar da nake ciki sai dai ko zata d'aukeni na fi son ta d'aukeni a tsarkakakken waje ba a wajenda yake cike da najasa ba, na sani ko kad'an ban tab'a jin ina son Fatima a cikin rayuwata ba kuma har abada ba zan tab'a son Fatima ba, sai dai a yanzu zan fad'i wani sirri wanda ba wanda ya san da shi a wannan wajen daga ni sai Ammie sai kuma Hajiya Maryam da kuma wad'anda suka yi wannan aikin sai kuma Allah da baya bacci balle minshari, amma ina son ku sani badan na cece Fatima zan fad'e wannan sirrin ba sai dan na ceci kaina ko ubangiji zai iya kallona da fuskar rahma ya gafarta man kura-kuraina idan na mutu, kuma wannan shi ne zunubi mafi girma da na tab'a d'aukarwa kaina kuma daga gareshi ne na tuba da aikata ko wannen irin laifi komai girmanshi ko mai k'ak'k'antarshi k..........!" Ammie ce ta yi hanzarin tasowa daga wajen da take zaune, ta wanketa da wani irin wawan mari wanda sanadiyyar wannan marin ne ya hana mata ida k'ark'are zancen da take yi, cikin wata mugunyar fusata Ammie ke cewa "Dan ubanki assirinmu kike bid'ar tonawa bayan Allah ya rufa mana shi! wlhy idan kika k'ara cewa ko uffan a wajennan ban yafe mak.....!" Abba ne ya katse mata hanzari wajen d'auketa da wani kafurin mari wanda sai da ya yi sanadiyyar fashewar bakinta da jini, cikin d'aga murya ya d'aka mata tsawa da cewa "Ke har kin isa ki tsine mata albarka? Ke a wa kuma da zaki hanata yin magana?.!" a rud'e Ammie ta dubi wajenda Hajiya Maryam ke zaune a mak'ure dik ta wani shige gashi dan yau tana da tabbacin watan tone abinda suka shuka ne ya gabato, ta ce "Maryam assiri ya k'arye! wlhy assiri ya k'arye Maryam!! yau na shiga ukku maganar Boka ta tabbata.!" ko uffan Hajiya Maryam bata ce da ita ba illa matsar kwallan da take yi a gefe, ba abinda kowa ke fad'i a wajen sai kalmar "Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un.!" Murmushin takaici Khairat ta yi kafin ta ce "Abba ka k'yaleta indai tsinuwa ce ba yanzu ta fara ba, wanda ma ya haifeni d'in ya tsine man sannan ya yi mummar addu'a a gareni, dan haka ko ta ci gaba da tsineman ko kar ta ci gaba da tsineman ni kaina na riga da na san cewa ni tsinanniya ce, sannan ko zata kasheni a wannan wajen numfashina ya daina aikin wlhy sai na tona assirinsu ita da Hajiya Maryam wlhy dik wani zaluncin da suka dad'e suna aikatawa sai na fad'eshi sai dai su kashe ni.!" Kuka mai k'arfi Hajiya Maryam ta fashe da shi kafin ta ce "Amma dai Allah ya isa tsakanina dake Rafi'at ina ma ace ban sanki ba da har yanzu assirina na rufe ba wanda ya fallasa shi, amma dai Allah ya tsine maki albarka.!" dik a cikin kuka take wad'annnan maganganun, hankalin kowa dake wajen ya tashi sosai musamman ma na mijinta dake zaune yana kallon abinda ke faruwa.............!
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share!
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...