P...38

262 55 2
                                        

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•BE-SMART•»•—*

*_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
 
           P...38

Wayyoo....! Wayyoo ni Allah Boka ya nutse ga gida kuma yana k'ok'arin redewa da mu a ciki, shegiya Khairat! Khairat kina ina ne? ni fa bana ganin komai a wajennan sai duhu, Hajiya Maryam! Wayyoo Allahna.!" a cewar Ammie, Hajiya Maryam ce ke tangal-tangal na bid'ar fad'uwa k'asa ta sanadiyyar wani gumdumemen abu da ta ji ya fad'o mata a saman kwanyar kai, kuka take zubawa hinhinhin kamar ranta zai fita sai dai koda hakanan bakinta ya k'i mutuwa inda take ce ma Ammie "Shegiya bak'ar matsiyaciya d'aibabbiyar albarka! kin tafka mana tsiya kuma kin barmu da jinya, wallahi tsakanina da ke sai dai Allah shi da ya had'ani da ke.!"  Khairat kam tsaye kawai take ta kasa motsawa a inda take sai famar rabe-raben idanu take tana neman ta inda zata ga Ammie ko Hajiya Maryam sai jin ta yi an kwashe mata k'afafuwa da hanzari ta fad'i twiii a k'asa da sauri ta ji an dira ta saman tumbin cikinta ana sukuwa, ihu take mai cike da firgici tana kiran sunan Ammie da Abba, ko waccensu sai da ta daku tuburan ta yi lik'is ga hannun wad'anda basu san ko su waye ba ne sannan aka janyosu giririri kamar Jakkan gidan Alhaji Audu, aka wuntsilosu waje kamar kayan wanki, ba tare da sun tsaya duba halin da suke ciki ba cikin wani mugun k'arfin hali suka mik'e tsaye ba tare da sunyi ma junansu magana ba suka nufi wani gida da suka ga alamun hasken hutar lantarki dik ya gama baje ko ina lungu da sak'o dake cikin wannan gidan, wanda ya fi kama da clubhouse, gudu suke kamar tayoyin mota suna fitar da nishi sama sama kamar wad'anda ke goye da buhun hatsi, da k'yar da wala-haula suka samu nasarar kaiwa ga get d'in gidan, a hanzarce suka  banke wannan get da k'arfi ya bud'e, aguje suka fad'a gidan rawar inda suka cinma mutane cike a cikinshi, godiya mai tarin yawa su kayi ma k'afafuwansu da suka taimaka masu a lokacinda suke buk'atar taimakonsu, jin komai ya tsaya cak a wajen kamar babu mutane a cikin club d'in ya saka su taddo kansu sama dan ganin abinda ke faruwa sai dai sunyi matuk'ar mamakin ganin dik yawan mutanen dake wajen babu ko d'aya a cikinsu, hantar cikinsu ce suka ji ta fara kad'awa kafin su kai ga jin tumbin cikinsu na musu sallamar mird'awa, k'asa-k'asa suka fara jin alamun sautin wata gwararriyar wak'a ta fara ta shi wanda hakan ya sa su maida hankalinsu da hanzari wajen da MC yake, sai dai ganin ko wanene MC'n ba k'aramin firgicewa ya saka su ba, wata dankwasasshiyar basamudiyar halitta ce marar kyan gani mai cike da ban tsoro da ban firgici suka gani wadda kana ganinta ko baka mutu ba sai kayi suman k'arfin hali idan kuma baka suma ba halin da zaka ji ka a ciki sai ka gwammace ma  mutuwar,   "sanin wannan halittar ko wacce iri ce, ya rage naku fan's.. Lol!"  Ihu dukansu suka saki a dai-dai lokacinda su kayi ido biyu da wannan mugunyar halittar, girgiza guda ta yi sai ga wannan club d'in ya koma wani d'ungurumin jeji, ko da su Ammie suka bud'e idanuwansu, kasancewar wani hatsabibin hasken da ya bayyana a club d'in a dai-dai lokacinda wannan mummunar halittar ta yi girgizar ya saka su runtse idanuwansu sabida kaifin hasken da suke ji har a cikin kogon idanuwansu, wannan halittarce suka ga ta bazu kashi-kashi bakunansu kuma sai zubar da jini suke kamar wad'anda suka ci naman mutum d'anye, ihu mai cike da rikitarwa su Ammie suka sake saki kafin su shiga yunk'urin guduwa domin shi suma kam tun a gidan Boka suka neme shi suka rasa, k'afafuwansu ne da suka ji sun kafe waje guda ko motsin kirki sun kasa yi da su ya sakasu sadak'arwa domin sun san yau tasu ce ta k'are, basu an karaba suka ji an jefa kawunansu cikin wani abu da suke tunanin bakin wad'annan munanen halittar ne, sannan suka ji an tazge kawunansu  gabad'ai daga jikinsu suka koma kutumbu, wani firgitaccen ihu ne dukansu suka saka a dai-dai lokacinda suka falka daga nannauyan baccin da suke zubawa a gaban su Abba a wajen wannan Malamin, ihu dukansu suka saka a wajen suna fad'in "Boka Dundum ka cece mu zasu halaka mu.!" wani nannauyan numfashi ne suka sauke a tare a dai-dai lokacinda idanuwansu suka yi masu tozali da mutanen dake wajen dik suna kallonsu, ganin Abba da Ya Abir tare da Alhaji Sulaiman wad'anda tuni daman hankalinsu ya dad'e da dawowa jikinsu tun lokacinda wannan Malamin ya basu wannan rubutun suka sha ya kuma shafa masu yanzu gashi har safiya ta waye misalin k'arfe 9:00am ba abinda ke damunsu hankalinsu ya dawo jikinsu sai su Aunty Intisar da Yumra tare da Yubra wad'anda tunda sassafe suka buga ma DPO sauk'o misalin 8:00am cikin damuwa suke tambayarshi inda ya kai su Ya Abir da nemanshi alfarmar da ya kai su wajensu wanda hakan ya sa DPO tausaya ma halin da suke ciki sosai har ya d'auko su suka zo tare anan suka same su Ammie kwance wanda halin da suka samesu a ciki ya matuk'ar d'aga masu hankali dan ko kad'an basa a cikin hayyacinsu, d'ai daga cikin Almajiran Malam ne ya shigo cikin gidan da sallama sannan ya shiga gayawa Malam sak'on da aka aiko shi da shi, na ana mashi sallama a waje, ba tare da damuwar komai a rai ba ya bawa su DPO hak'uri da cewa "Zai je waje ya dubo mai sallama da shi.!" wanda ko kad'an basu nuna damuwarsu ga hakan ba. wasu dank'ara dank'aran motoci ne sababbi wad'anda kana ganinsu ka ga Dollars, k'irar BMW ne kusan guda Ashirin kuma dik bakak'e ne wulik sai walk'iya suke kamar madubi, sai dai guda daga cikinsu wadda ita ce cikon ta 21 ta babbanta da sauran kalarsu ma ba guda ba ce balle k'irarsu, wasu k'ak'k'arfan matasa ne Maza wad'anda yawansu zaya kai kusan 30, suka fara fitowa daga cikin wad'annan motocin ko wannensu yana cikin shigarshi ta masarauta wanda kana ganinsu zaka san sojojin wata k'asaitacciyar masarauta ce, wasu had'ad'in mata ne suka fito daga cikin mota guda a hanzarce suka tsaya  dai-dai da wannan jahilar mota kirar New Rolls-Royce Phantom, fara ce motar sol kamar girgijen da bai d'auko komai ba a sama, Papa ne ya fara fitowa daga cikin motar kafin Zulfa sai Fatima, cikin wata mahaukwacciyar shiga wadda ke cike da d'aukar hankali, Malam na isowa a wajenda Papa  yake sai da yaji tsikar jikinshi ta tashi wanda kallo guda ya yi ma mutanen da ke wajen ya san ba mutane ba ne sai dai yanda fuskarshi ta nuna mamaki ne k'arara ganin bil-adam a cikinsu kuma yana bala'in kama da wannan hamshak'in basaraken, murmushi Papa ya fara sakar mashi dan ya gama lura da halin da yake ciki, shi ma wannan Malamin murmushin ne shimfid'e a fuskarshi kafin ya kai ga k'arasowa wajenmu suka yi musabuha mai had'e da sallama shi da Papa, sannan suka dan koma gefe Papa ya yi mashi bayanin komai tare da abinda ke tafe da su, murmushi kawai wannan malamin yake wanda yak'i gushewa a fuskarshi kafin ya kai ga yi muna iso har a cikin gidan cikin girmamawa.......!
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now