*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*P...43
Tafiya muke a hankali a cikin motar ba ka jin sautin komai a wajen sai sautin shashshek'ar kukana dake fita akai-akai, bai ce da ni ko k'ala ba, kamar yanda ni ma bance da shi ko k'ala ba tun lokacin da muka baro gidan, sai dai lokaci zuwa lokaci idan na d'an sace kallonshi sai naga yana murmushi wanda bansan dalilin yinshi ba har muka kawo dai-dai da wata super market ya fita ya amso kayan drinks da sauran kayakkin da zamu buk'ata sannan ya dawo ko anan ma shiru mu kayi karatun kurma, anan saman hanyarmu muka had'u da wani mai gashin kaza ya fita ya sayo d'ankwala-dankwalan kaji wajen guda biyu kamar abinda ciki goma zai d'auka, ni dai dik abinda yake kallonshi kawai nake har ya dawo muka sake d'aukar hanya, tun daga wannan wajen ba mu sake tsayawa ko ina ba sai a bakin get d'in wani tsararen gida wanda kallo guda zaka mashi ka ji ya shiga ranka, horn ya yi, a hanzarce mai gadi ya taso ya wangale mashi get ya shiga, tun a bakin harabar gidan nake kallon irin tsaruwar da gidan ya yi da kuma irin had'uwar da ya yi har muka sauk'a a parkin space wanda bai wuce na mota hud'u ba, "masha Allah.!" ita ce kalmar da na fad'a a cikin rai na domin gidan ba mai irin shegen girman nan ba ne na Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un, d'an matsakaici ne dai-dai zaman mutum biyu, sosai gidan ya shiga raina mak'ura, marfin kujerar da nake zaune ce da naji an bud'e ya ankarar da ni, ba tare da wata-wata ba naji ya tallabeni sama tare da rufe marfin motar da k'afarshi ya dannan mata key, a hankali yake tafiya da ni idanuwanshi na kaina hanyar da yake bi ma ba ita ce gabanshi ba, k'ok'arin kwace kaina na shiga yi ina mai mugun jin tsoron karya zukkuceni k'asa, sai da muka kawo dai dai da wata babbar kofa sannan ya ajiyeni tare da bud'e wata k'ofar da nake tunanin ita ce tawa, sannan ya ja hannuna muka shiga d'akin da k'afar dama bakunanmu d'auke da bismillah tare da sallama wa junanmu, nan take idanuwana suka kai ga haskoman palour b'arau-b'arau, Wa'iyazu Billah, had'uwar da naga dakin ya yi sai da ya bani tsoro dan ban san lokacinda wani guntun kwalla ya fad'oman a fuska ba, domin dik abinda ku kasan ana sakawa a dakin amarya sai da aka saka man shi sai dai nawa ya banbanta da na sauran wanda kana ganin wannan tsarin kai da kanka kasan tsarin ba na mutane ba ne, iskan da naji an hura man a fuska ne ya dawo da hankalina a wajen, murmushi ya sakarman wanda ni kuma a lokacin na k'ara tamke mashi fuska, dogon hancina na ji ya ja kad'an kafin ya ce da ni "Madam, har yanzu ba a daina fushi da ni ba.?!" ganin nak'i cewa da shi ko k'ala ya saka shi duk'awa k'asa ya yi kneeldown irin na matsoratan bulala tare da rik'e kunnayenshi biyu ya zumbulo man k'aramin bakinshi wanda hakan da ya yi ba k'aramin kyawo ya k'ara ma fuskarshi ba, sannan ya ce man "Aunty ayi hak'uri, ba zan sake ba.!" yanda ya k'ark'are maganar ba k'aramar dariya naji na k'yalk'yale da ita ba, shi ma tashi ya yi tsaye ya rungumeni yana dariyar tare da shak'ar k'amshin dake jikina yana lumshe idanuwa, k'ok'arin tureshi gefe na shiga yi dan naga alamun abin na shi na bid'ar wuce gona da irinta, sai dai yanda ya matseni ne ko shed'ar ma dak'yar nake jin ina yinta, ganin dik abinda nake k'ok'arin yi kamar shi bai ma san ina yi ba ya sakani sakin wata razananniyar k'ara wadda sai a sannan hankalinshi ya dawo jikinshi ya shiga tambayar abinda ke faruwa tare da lalaben gabad'ai ilahirin jikina yana neman abin da ya sakani sakin wannan k'arar, ganin k'ok'arin cire man riga yake son yi, ya saka ni cewa wannan tambad'ar bada ni za a yita ba, na kwace kaina a hanzarce na gudu na shige cikin d'ai daga cikin bedroom d'ina wanda hakan ya saka shi biyo bayana aguje dan ya gano abinda nake nufi, kai tsaye naji ya cafkeni ya jefa saman gado yana man cakulkuli, dariya nake sosai wanda shi ma ita yake kafin daga baya cakulkulin ya juya izuwa wata harkar ta daban, sai da ya yi man lik'is dariya ta koma kuka sannan ya d'aga daga saman jikina yana min dariyarshi ta k'eta tare da ziyartar wani d'aki da nake tunanin bathroom ne, ya d'auro alwala ya fito, ya ce Ni ma na shiga na yi alwalar, ina sheshshek'ar kuka na mik'e tsaye dan dik ilahirin k'irjina ciwo yake man sannan na shiga na d'auro alwala na fito kamar yanda ya umarceni, ko da na fito daga bathroom d'in har ya fiddo man hijab daga cikin kayan lefena wad'anda aka tsaraman zamansu da kyau a cikin wata jahilar widrobe d'ita, saka man ya yi da kanshi sannan ya tada muna sallah bayan mun gama sallar ya yi muna addu'a sannan muka dawo palour'n ya fiddo dik kayan da ya sayo muna ya je kitchen ya d'auko flat ya zuba muna a ciki, ganin komai nak'i naci a cikin kayan ya saka shi yi man d'ure ina ci ina kuka, da ya ga alamun da gaske bana son cin abincin ya tashi ya gangame kayan gabad'ai ya kai kitchen, ba tare da ya ce dani ko k'ala ba ya shige bedroom, ni ma har a cikin raina naji dad'in fushin da ya yi da ni dan na san ko banza zai barni ne na futa, ko minti 10 bai yi ba ya sake fitowa daga cikin bedroom d'in cikin shirinshi na bacci, ko kad'an bai nuna alamun wajena zai zo ba, sai jin nayi ya d'aukeni gabad'ai ya manna ni a k'irjinshi, sosai naji tsoro da yanda naga lokaci guda ya canza man ya dawo sak Ya Abir d'inshi wanda hakan ya sakani had'iye ihun da nake k'ok'arin saki na bishi kamar yanda yake so, sai da ya kawoni dafda mirro sannan ya direni a gabanshi tare da yunk'urin rage man kayan dake jikina, da k'arfe na fizge kaina ganin da gaske tumb'ur yake son ya maida ni, cikin wata dasasshiyar muryarshi wadda lokaci guda naji ta canza man kala yake ce man "Baby ba kyason na rage maki kayan da ke jikinki ne?.!" a tsorace na kad'a mashi kai alamar "eh.!" murmushin k'urulla ya saki sannan ya mik'oman towel ya ce to na rage da kaina ba zai tab'ani ba na je na watso ruwa na zo mu kwanta dan shi bacci yake ji, ba tare da damuwar komai a raina ba, na amshi towel d'in tare da k'ok'arin cire rigar dake jikina, sai dai ganin ya kafeni da ido kamar wani maye ya sakani turo d'an k'aramin bakina wajena ina cewa "Ni na ma fasa d'ebe rigar.!" zaro idanuwa ya yi waje cike da miskilanci ya ce "To me ya faru kuma yanzu.!" a shagwab'e yake maganar kamar wani jaririn yaro, ni ma yanda ya man nayi mashi, na ce "Ba kai ne ba.!" a d'an tsorace kamar da gaske ya sake zaro ido ya ce "Ni kuma Aunty? me nayi to?.!" sai da nayi kamar zanyi kuka cikin gunguni na ce mashi "Sai kallona ka ke yi.!" murmushin wani babban mazuru ya yi wanda sai da ya fito da sautinshi waje sannan ya ce "To shikenan an daina daga yanzu Aunty.!" yana gama fad'in hakan ya juya ya kalle madubi, ji nayi kamar an d'auke man wani gundumbulin dutse a saman kai nan take na samu kwarin gwiwar zage damtse wajen d'ebe rigar gabada'ai a jikina, ina ce mashi "karfa ka juyo.!" shi kuma yana ce man "ai ba ma zan juyo d'in ba.!" wanda hakan ba k'aramin kwarin gwiwa ya k'ara bani ba wajen ci gaba da rage kayan jikina da nake yi, sai da na d'ebe bra d'ita da fant gabad'ai tare da nad'iye rigata da niyyar idan na fito daga wajen wanka zan ninke ta, har na duk'a zan d'auki towel d'in dake saman gado wanda ya ajiye man, muka yi ido hud'u da shi a cikin madubin, aiko ban san lokacin da na sake wata irin razananniyar k'ara ba a rud'e na fige towel d'in da k'arfi na shige cikin bathroom na kulle ina zuba kuka...................
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shared
![](https://img.wattpad.com/cover/215007905-288-k317588.jpg)
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...