*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*
*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*P...15*
_Wani rikitaccen ihu ne tayi tare da saka duk iya ƙarfin da Allah Ya yi mata da niyyar watsama fuskar ta wani wawan mari mai haɗe da ruwan duka._
_Cak naga ya damƙe hannunta kai tsaye tare da bangazata gefe sai da ta tashi faɗuwa ƙasa, sannan ya sauke ni ƙasa tare da riƙe kunne na guda yana man kashedi akan Gobe ma idan na sake wannan shine hukuncin da zan sake amsa a wajen shi ._
_Cikin rawar murya na amsa mashi da "To" sannan yaja hannu na muka sauko ƙasa muka ziyarce wajen dinning table._
...
_Tun lokacin da ya hankaɗe ta gefe ta kasa ɓarkata aikin komai, sai wani wawan murmushi da taji ya yi gaggawar kuɓce mata wanda ta kasa gane dalilin yinsa, kai tsaye ta ce_
_"Allah ya isa tsakani na da kai Anwar, ka cuceni ka haɗani da wanda nake muradin kasancewa tare da shi har na tsawon illa masha Allah, dama wannan shine sakamakon hukuncin da zan dinga fuskanta a wajen Ya Abir kuma dik ta sanadiyyar ka, inaaaaaa! wlhy bazai taɓa yiyuwa ba, yanda ka tozarta ni a gabansa nima sai na tozarta ka a gaban mahaifanka.Ace abu shekara da shekaru yaƙi ya wuce, hmmm! koda dai kafin nayo wajen ka Anwar kamata ya yi na fara gamawa da babban muzuru.Tabbas shawarar Ammie ta gaskiya ce, dan haka na ɗauka da hannu bibbiyu, sai dai wannan abun duk ni kaɗai, bai man yawa ba kuwa?"_
_Haka dai tayi ta surutan ta barkatai kamar wata zautacciya kafin ta sauko ƙasa._
_Koda ta ida ƙarasowa wajen dinning har Mummy ta gama zubawa kowa abinci dai-dai yanda cikinsa zai ɗauka._
_Zama zata yi amma ƙuli-ƙulin Idanuwanta na gareni wanda hakan ba karamin kwarin gwiwa ya bani ba wajen kange idanuwa na a waje guda domin gudun yin ido biyu da ita ,saboda nasan uwar harara ce zata zabga mini, dan ita kaɗai ce makamin dake hannunta domin ko kaɗan ba zata yi yunkurin aikata duka ba saboda gudun ganin ɓacin ran mutanen dake wajen._
_Bayan kwana biyu..!_
_A bubuwa da dama sai faruwa suke musamman yanzu da wata sabuwar ƙiyayya ta fara shiga tsakani na da Aunty Khairat da kuma Aunty Intisar,dan tun lokacin da wannan abin ya faru tsakani na da Ya Abir da kuma Aunty Khairat, naga Take-taken Aunty Intisar ya fara sauka kaina, sai dai ko kaɗan basa nuna ainahin kiyayyarsu gareni ƙarara a gaban su Mummy da sauran mutanen gidan.Wanda hakan ba ƙaramin mamaki yake bani ba, amma koda hakan nima turjewa nayi na dinga biye musu kamar yanda suke mun._
_Ta ɓangaren Ya Abir kuwa, kar yake kallon mu tare da mamakin wannan irin ƙarfin halin dake gareni tun ina 'yar ƙanƙanuwa ta to inaga na girma kuwa.Shi kanshi yasan za'a tsula tsiya ne a wannan lokacin, sai dai koda hakan tsakaninsa da Ya Bikhram kulawa babu irin wadda bana samu a wajen su, dan duk da da Makarantar boko ya hana direba ya kaini. kasancewar ba skull dinmu guda da su Yumra ba ,wanda hakan ya ƙara bashi damar kaini ya kuma ɗauko ni._
_Tsakanin shi da Aunty Khairat kuwa sai dai kallo, ko shi kuwa sai idan an haɗu a Babban Palour idan za'a gudanar da dinner, dan ko part ɗinshi ya hana ta shiga wanda hakan ba ƙaramin kona mata rai yake ba musamman idan taga yanda nake ta faman sintiri a cikin part din, na mishi shara ko goge-goge._
_Idan naga ruwan comments zanci gaba idan kuma aka samu akasin hakan insha Allah ba lallai ba ne ko bayan sallah ku samu cigaban shi ba Fan's_
*Follow me on wattpad and vote— Smart_Feenert*
*Be smart*
*Pls shere*
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...
