*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**P...7*
_Nan take, taji hawaye na kwaranyo mata ba tare da ta shirya ba, ta ce "Allah sarki Zuwaira! Allah ya kai haske a cikin kabarin ki, tabbas dik cikin halayyanki ba ko guda wanda Fatima ta baro na lokacin kuruciyar ki...." shigowar Gwaggo Talatuwa ne cikin dakin ya katse mata hanzari wajen ci gaba da abinda take, cikin siyasa ta share hawayen da suka yi mata tambari a saman fuska ba tare da ta bari Gwaggo Talatuwa ta halkanta da hakan ba._
~~~
_Sai da na biya shigifar garkarmu na dauke Taya ta dake labe a bayan gambu, sannan nabar gidan gabadai, Na nufe bayan gidan mu, anan na samu 'yan majalissarmu suna tsaire da Tayar, daganan Nima na shiga sahu aka daidaita dani sannan muka tayas,_
~~~
_Sai da naji an fara kiran sallar Magrib sannan na koma gidan dan Ni har na manta da aiken da aka yiman,_
....
_"Ina aiken da akayi maki Ja'ira?."_
_Ita ce tambayar da Kaka ta fara tarbata da ita tun kafin na ida isowa cikin gidan,_
_Cikin shashshekar wahala na ce "Wallahi dik inda naje sun tashi, har tsallaken Titi naje bansamu ba sun kare, karikakaf ",_
_Ba tare da ta nuna halin damuwar komai ba, ta ce "To shikenan na ji bani kudin kije kiyi sallah har gobe sai a'ida, dan tun dazu tunanin da nake kenan sabida nasan basu cika dadewa sosai ba."_
_Gwaggo Talatuwa dake fitowa daga cikin dakin da ba tasan wainar da ake toyawa ba, ta ce "Sai yanzu ki kaga damar kawo Itacen, tun dazu a aike ki amma ki maida waje naki kamar ba jiranki akeyi ba._
_Murmushin mugunta na saki a lokacin da na ji tayi wannan maganar, cikin nuna halin ko in kula da zancen na nufi wajen da jerin botoci suke na duka na dauki guda na wuce na dibe ruwa cikin randa na nufe hanyar shiga toilet kamar wata babbar mace.__Cike da mugun jin haushina, Ita ma ta sake murmushin ta mai cike da kunar zuciya, cikin ranta ta ce "Yaro baisan wuta ba sai ya taka, ta karasa maganar a cikin rainta tana mai maida dubanta ga Kaka da ita har ta shiga kakkantar wajen, dan ta lura da irin takurawar da Gwaggo Talatuwa ke yawan yi mani sai dai bata son muna mata,_
_Ta ce "Inna an karo ita cen kuwa?"_
_Kai tsaye Kaka ta ce mata "a'a, dik inda taje babu sun kare, a bar suyar kawai har gobe da safe sai a ida karkarewa"._
_Ta ce "To Inna Allah ya kaimu."_
_Kaka ta ce "Ameen ya rabbi Talatu"_
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...