*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**_DEDICATE THIS PAGE TO MY WATTPAD FAN's thanks for ur vote and following nd comments thanks a lot!🙌🏻 luv u more_*
*_Alhmdu lillah jiki na da sauƙi yanzu sosai! na gode da addu'o'inku a gare ni Fan's and friends thanks so much_*
*P...27*
Misalin ƙarfe 1:22am su Chaki suka farfaɗo, cikin k'arfin hali irin nashi ya saka hannu ya lalabo wayarshi dake aljihu tare da hamdala ga Ubangiji ganin wayar na tare da shi, ba tare da wani ɓata lokaci ba ya dannawa number Oga Bobi calling.... sai da tayi kusan yankewa sannan ya ɗauka ba tare da ya ce ko ƙala ba
Cikin shashsheƙar wahala Chaki ya soma kora mashi bayani kai tsaye ba tare da ƙaƙƙautawa ba ya kwashe komai ya sanar da shi kafin ya kai ga ida zancen "ƙittt Oga ya yanke wayar ba tare da ya jira ya ida ba tukunna
Hakan yasa cikin rashin kwarin jiki Chaki shi da sauran abokan shi suka tashi suka tattali Jantali suka isa wajen da suka yi parking d'in motarsu suka saka shi ciki sannan suka ɗauki hanyarsuAnan babbar majalisarsu suka same Oga Bobi zaune a saman kujerarshi ta mulki rik'e da kofin giya a hannunshi ta ɓangare guda kuma sauran yaranshi ne zazzaune suna shaƙatawarsu
Da zumud'i suka ida k'arasowa wajen da yake tattale da Jantali a hannayensu wanda suke k'ok'arin jibgewa kusa da Oga'n
Cikin rawar murya Chaki ya ce "Boss" ba tare da shi wanda aka kira da Boss d'in ya tada kanshi ya kalle shi ba ko kuma ya ce da shi wani abu ba
Nan dai Chaki ya soma maimata mashi zancen, inda ya sake cewa "Boss kaga yanda aka yi ma Jantali! wlhy muma dak'yar muka sha dan bamu tsira ba gabad'ai an maida Dicks d'inmu HQ!" Dariya mai k'arfin gaske ta kubce ma dikkanin mutanen dake wajen harda su kyakkewa lokaci guda Boss ya d'aga masu hannun shi sama daganan kuma kowa ya yi tsitt kamar babu mutane a wajen ɗai daga cikin yaran Boss d'inne mai suna Yankuzuna ya soma yi masu magana cikin irin muryarsu ta tantiran 'yan-iska ya ce "To wai ku aikin me kuke yi ne da har zaku bari akai ga yi maku wannan ta'asar ba tare da kun sassare ma mutum k'ok'on kai ba?."
Cikin rawan murya Chaki ya ce "Ba mutane ba ne fa! Wlhy fa gamo muka y........"
Yankuzuna ya sake hanzarin dakatar da shi a karo na farko ta hanyar katse mashi hanzari wajen ci gaba da bayanin da yake son ya k'ara kora masu, ya ce
"Kaii dallah rufe ma mutane baki Macce kawai! Su aljannun ne kunka kasa tsayawa ku gwabza da su ko ta halink'ak'a ne su ma suji a jikinsu susan cewa lallai ku kiwon Oga ne fa, shine har zaku bari su la'antaku haka? Gaskiya fa kun cika manya-manyan raggwaye wlhy! Oga ka ji wai wani zancen to yanzu ya za'ayi da HQ d'in? sai dai fa ku koma wajen su ku amso naku ku mik'a masu kayansu..!"
ESTÁS LEYENDO
'YAR BALLAJJA'U
FantasíaSai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...