P...13

525 71 4
                                    

*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*-•«Start, on 23/2/2020»•-*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*-•«•Be smart•»•-*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*-•@••«•»•@•«•»••@•-*

*🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🍾🍾🍾🍾🍾HAPPY BIRTHDAY 2U, YAYA HAYAT (Admin of Admins) ALLAH UBANGIJI YA KARO DINBIN SHEKARU MASU ALBARKA, AMEEN🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂*

*P...13*

_Basu Zarce a ko'ina ba sai a bakin get din gidan, suna horn, a hanzarce mai gadi ya taso ya wangale masu shi._

_Anan Cikin makeken filin dake cikin gidan, direbobin suka parker._
_Sai da kowa ya gama fita daga cikin motocin sannan direbobin suka halarce parking space, suka gyara tsayuwar motocin._

....

_Cike da tsantsar farin'ciki suke tafiya tare da dan taba fira jifa-jifa har suka ida karasowa a cikin Babban Palour, tun anan suka fara raba hanya inda wasu suka haura sama domin ziyartar nasu part, wasu kuma suka ziyarce na kasa dan ra'ayin kansu._

.....

_Ko da Mummy ta shigo cikin Palour'nta bata same ni anan ba, wanda hakan ya kara bata tabbacin ina cikin Bedroom, domin tana da tabbacin cewa, bana part din su Yumra sabida tasan tare suka fita._

_Tana shigowa tayi kicibus dani kwance a saman gadon nayi shane-shane inata famar sharbar bacci na, ba tare da fargabar komai ba._

_A hankali ta ida karasowa wajena sannan ta zauna kereriyar wajen da nake kwance tare da ciro kaina sama ta aza a saman ciyarta tana shafa gashin kaina a hankali tana kallon fuskata cikin burgewa._

_A dan tsoroce ta maida dubanta ga bangon dakin, ganin ko karfe nawa agogon dake ɗahe a bangon, ya ce, ya sakata kwakkwanto da fargabar Makara wajen gabatar da sallar magarib, wanda hakan yasa ta shiga tayar da ni a hankali tare da kiran sunana kasa-kasa._
_Kamar a mafarki naji ana tayar dani, wanda hakan ya sani bude kwala-kwalan idanuwa na a gajiye kamar wadda tayi wani aikin wahala, na sauke su ga wanda ke kokarin tayar dani din, Ganin Mummy'ce ya sakani sakin wani kayataccen murmurshi tare da tambayarta "Har kun dawo?._
_Itama murmushin ta sakar man kafin ta bani amsa da "Eh." sannan ta ce "Na tashi nayi wanka nayi alwala nayi sallar Magrib, kar lokaci ya kure._

_A hanzarce na mike zaune, ta taimaka man na ida rage kayan dake jikina sannan na shiga bathroom ._

....

_Sai da mu kayi Sallar Magrib da Isha'i sannan muka fito Babban palour, anan muka same sauran mutanen gidan a cikin babban Palour'n harda Daddy sai dai babu Ya Abir a cikinsu wanda hakan ya kara bani kwarin Gwiwar gaishe da kowa a wajen tare da yima Ya Bikhram sannu da zuwa, cikin far'a ya amsa tare da tambayar lokacin da nazo, anan Mummy ta shiga yi mashi bayanin komai._

_Ba tare da bata lokaci ba, gabadayanmu muka halarce saman makeken Dinnig table din dake jibge a harabar shi kamar wani army, ganin babu Ya Abir a wajen yasa Mummy ta ce "Naje part dinshi na kiranyo shi"._
_Wani firgitaccen kallo ne Aunty Khairat ta jefoman mai hade da ruwan harara, kamar dan kaina zan je._
_"To" kawai na iya cewa da Mummy kafin na saita hanya ta, ta tafiyar"._

~~~

_Tafiya nake jiki ba kwari, kamar wata nakkasassar akuya, har na ida dalewa saman matattakalan benen Aunty Khairat bata dauke idanuwanta gareni ba, wanda hakan ya janyo hanklin Aunty Intisar gareta, a hankali ta ciro wayarta ta shiga tura mata text message, domin babu damar yin wata magana a gaban su Daddy, ta ce "Ki kwantar da hankalinki Amaryar Yayanmu kuma Uwargida a wajensa , indai dan wannan ne ba wani abin damuwa bane, dik da nasan irin abinda kike ji game da wannan kazamar yarinyar, sai dai ki sani ba abinda Ya Abir zaiyi da ita, bama shi kadai ba, kaf gidannan bana tunanin akwai wani wanda zai sota kamar yanda kike tunani, dan wannan daukar 'yan waje ce bata cikin gida ba." Ta karkare rubuta text dinne tare da kyakyatar idanuwan Aunty Khairat dake kunkume da fuska, kamar Kabushi (Kabewa), Suna yin 4eyes ta kashe mata ido guda tare da nuna mata alamar ta dubi wayar dake hannunta da wutsiyar idon ta...._
_Kuyi hakuri da wannan, wlhy jiya da misalin 3am na tashi da wani azababben ciwon ciki, amma yanzu jikin da sauki bayan munje asibiti, Insha Allah gobe idan na kara mirmijewa zan maku typing mai yawa._
_Dan Allah ku saka ni a addu'a, Nagode!_
*Follow me on wattpad and vote-Smart_Feenert*
*Be smart*
*Pls shere*

'YAR BALLAJJA'UTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang