*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*P...45
"Kallon ya isa haka karki canyeni Malama.!" wannan maganar ce da naji ya sako man kai tsaye, ya ankarar da ni, wani dogon tsaki na ja tare da meda fuskata gefe a dai dai lokacin da yake ajiyeni a wani wajen na daban, ya shiga rage man kayan da ke jikina yana ce man "Idan ki ka sake man tsaki sai na cire wannan k'aramin bakin.!" Aiko sabida tsabar jin haushin wannan maganar ta shi ban san lokacin da na sake sakin wani tsakin ba ina mai janye jikina daga gareshi tare da rik'e pant d'ina takin da yake k'ok'arin zagewa, a takaice na ce mashi "Bana son haka fa gaskiya, ka fita zanyi wankan da kaina ni.!" hankad'a hannuna ya yi gefe ya ci gaba da d'ebe man pant d'in ba tare da ya sake cewa da ni ko k'ala ba har ya yi nasarar maida ni tunb'ur sannan ya sake jefani cikin ruwan zafin, ihu na buga zan mik'e tsaye akan wani sabon rad'ad'in da naji k'asana ya sake d'auka, wani wawan kallo ne da naga ya sake sakarman tare da maida ni zaunen, ya saka ni had'iye kukan da nake k'ok'arin saki sai ambaliyar hawayen da suke sauka a saman fuskata, wanda shi kanshi da yana da yanda zaiyi ya tare zuwan wadannan hawayen nawa wad'anda yake jinsu tamkar ruwan dalma a saman zuciyarshi da ya yi ya samar ma zuciyarshi salama da kwanciyar hankali sai dai dik da hakan bai bari na fahimta da hakan ba domin yana da tabbacin idan har ba ta hakan ya b'ullo man ba, to ba zan tab'a bashi had'in kan da yake buk'ata ba a gareni. sai da ya gama tsuma ni sosai, sannan ya muna wanka tare, bayan mun gama ya saka muna rigunan wankan (bathrobe) sannan muka d'auro alwala muka baro bathroom d'in ina dingirisa dan haushi ya bani da ya zo zai daukeni ma k'in bari na yi, sai da muka fito daga cikin bathroom d'in babu zato balle tsammani na ji ya cirani sama ya d'aukeni caraf kamar mage, kukan dake k'ok'arin kub'ceman ne tun d'azu, na fashe da shi ina dukan k'irjinshi tare da fitar da sautin wani azababben kukana mai mugun cin rai'n wanda ake yi wa shi, ina ce mashi "Mugu.!" Ina ci gaba yin kukan da nake yi, matseni ya yi gam a jikinshi ya runtse idanuwanshi sosai domin har a cikin zuciyarshi yake jin sautin wannan kukan da nake yi, sai da ya ajiyeni zaune a saman gado, sannan ya durk'ursa k'asa tare da kamo hannayena biyu ya sumbata sannan ya dubeni da idon basira tare da kiran sunana a hankali cikin wata rikitacciyar murya ta shi mai saurin narkar da kitsen zuciya, tsayar da kukan nawa nayi cikin da wani shauk'i wanda ya yi nasarar jefani cikin wani yanayi wanda ban ma san da zuwanshi ba tare da d'ago k'uli-k'ulin idanuwa na kalleshi ido cikin ido ba tare da na kyafta ba numfashina da dukan na shi a hankali, mun kusan shahe wajen mintuna 10 a hakan da yaga alamun Shaid'an na k'ok'arin mantar da mu hanyar gaskiya ya tuna da Lokacin Sallar Subahim na son k'uremu, ya saka nan take ya janye fuskarshi tare da janye hannayenshi daga rik'on da ya yi man kai tsaye ya ce "Ni ne Mugu ko?.!" Maganar da naji ta fito daga bakinshi ne ta katse man hanzari wanda sai da na d'anyi tunani kad'an kafin na gane inda zancen na shi ya dosa dan ni har ma na manta da munyi haka da shi, a d'an shak'iyance na ce gyada mashi kai alamar "Eh na fad'a d'in.!" tare da juya mashi fuskata baya dan karma ya ga alamun wasa a tattare da ni, sai da ya d'an sake wani rak'in murmushinshi wanda a iya sanina da shi wannan kalar murmushin da ya yi shi ne cikon makaminshi na mugunta idan ya samu k'eta, sannan ya ce "Cewa kika yi fa idan kika yi aure, yara goma ki ke son ki haifa! Ko kin manta ne?.!" A d'an tsorace na juyo na kalleshi tare da turo d'an k'aramin bakina na ce mashi "Ni yaushe na ce da kai haka?.!" dara-daran idanuwanshi ya waro man a wajen alamun mamaki ya kamashi ya ce "Zan fa tono lokacin fa?.!" Cikin k'aguwa da in san wannan lokacin na ce "Eh tono d'in.!" Ya ce "To shi ke nan! Kin tuna wannan lokacin da ku ke d'aki ke da su Yumra bayan na d'auko ku daga islamiyya.. to ai ba d'akina na shiga ba a wannan lokacin har zan wuce ne na ji k'ishin-k'ishin na tashi irin na ku na mata, ki ka saka ni jiyo abin da kunnena ba zai iya d'auka ba.!" kunya ce naji ta ruftumomin zane ta lullubeni gaba d'ai da jin wannan furucin nashi wanda hakan ya sakani dukan k'irjinshi cikin wasa ina lullub'e fuskata a cikin jikinshi. Dariya ya yi shi ma kamar yanda nayi tare da kok'arin janyeni a jikinshi ya taimaka ya d'agani muka nufi wajen da zamu gabatar da sallar Subahim, muna ida k'ark'arewa kuwa na barshi a wajen zaune yana lazimi ta dalilin wani azababben baccin dake ta famar tsokalata wanda hakan ya sakani gincirawa kad'an na kwanta saman dardumar da na k'ark'are sallah daganan kuwa sai bacci. bansan lokacin da ya k'ark'are lazimi ba ya kwanta wanda K'arar wayarshi ce dake ta famar ruri tun d'azu ya falkar da mu, Yunk'urawa na yi zan tashi amma dik naji jikina ya man nauyi sosai, wanda ya zamana k'afata ma bana iya d'agata sama ga wani azababben zazzab'in da nake jin yana tasoman afujajun, a hankali ya mik'a hannunshi ga wayarshi daketa famar rure mashi kunne, ba tare da ya duba sunan wanda ke kiranshi ba ya d'auki wayar da sallama cikin natsuwa, muryar Abba ce da yaji ta ankarar da shi ya mik'e zaune, inda bayan sun gama gaisawa ne Abba ya ce mashi ya sameshi a gida zuwa anjima yana son su tattauna wani batu ne, bayan sun gama wayar ne sun yi sallama a sannan hankalinshi ya kaiga dawowa gareni, sai dai ganin halin da nake ciki ba k'aramin tashin hankali ya sakashi ba. Misalin k'arfe 12:40pm ya bar gidan kasancewar mun tashi a makare, sai dai kafin ya fita sai da ya tabbatar komai ya fara sauk'i a gareni sannan ya fita wanda bai jima da fita ba su Yumra suka zo wad'anda nake da tabbacin shine ya turosu kuma sosai naji dad'in ganinsu hankalina ya kwanta. Bayan ya isa wajen Abba, suka tattauna muhimman abubuwa game da auren shi da Khairat wanda a halin yanzu ba a san makomarshi ba, inda Abba ya bashi shawarar da ya mata saki d'aya dik lokacin da Allah ya k'addara ta fito daga gidan yarin idan da sake had'uwar aurensu sai su ci gaba da zaman aurensu kamar yanda shari'ar addinin musulumci ta tanada, sosai ya yi amanna da shawarar da Abba ya bashi wanda ba a d'au tsawon wani lokaci ba suka nufi hanyar gidan yarin da aka ajiyesu tare da takardar sakin a hanunsu. Bayan sun isa gidan yarin tare da bin dik wasu k'a'idodin gidan yarin har suka samu ganawa da Khairat kad'ai, sai dai kafin a bata takardar sakin a hannunta sai da Abba ya yi mata nasihohi masu ratsa zuciya wad'anda sosai suka gamsar da ita kuma ta aminta da hakan d'ari bisa d'ari sannan Ya Abir ya bata takardar sakinta da ya yi mata, wani dummm! ta ji a lokacin da ta amshi wannan takardar tana juyata tare da nanata kalmar "Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un!!!" har sau ukku kafin wasu hawayen nadama masu zafin gaske su fara wanke mata fuska domin iya tashin hankali a wannan lokacin ta ganshi sai dai abu d'aya ne wanda idan ta tuna yake dad'ad'a mata rai shine inda Ya Abir ya tabbatar mata da cewa "Zai ci gaba da jiran dik ranar da ta fito za a sake d'aura masu wani auren.!" godiya ta masu sosai kafin ta bar wajen zuciyarta cike da nadamar abinda ta aikatawa rayuwarta, a hanzarce suka bar wajen zuciyoyinsu cike da matuk'ar tausayin halin da ta tsintsi kanta a ciki.................
Bayan wata ukku!abubuwa da dama sun faru sai dai hamdala ga Ubangiji, a cikin wata biyu kacal Abba ya sake aure, inda ya aure d'ai daga cikin 'yan uwanshi na lak'e-lak'e, ranar da aka d'aura aure a ranar amarya ta tare a gidanta, haka su ma su Aunty Intisar a nan gidan suke zaune tun bayan rasuwar iyayensu, wanda kuma a halin yanzu sosai suke jin dad'in zama a gidan kuma sun d'auke mutanen gidan tamkar wad'an da suka haifesu.............
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
Be smart
Pls share
![](https://img.wattpad.com/cover/215007905-288-k317588.jpg)
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...