🌹🥀🌷
*K'WARK'WARAH*
🌼🏵️🌺
'''{ITAMA MATAR SARKI CE}'''_AREWA HISTORICAL_
Daga
OUM MUWADDAH"Sannu Annah! Tashi mu karasa kofa!"
"Junnuh! Bazan tashi ba, tafiya zanyi. Dama ba daraja ce dani ba, Junnuh ko bayan raina karki tab'a kaucewa tsarin addini musulunci, Junnuh karki zubda kimarki! Ki rike darajarki na Y'a mace ki zama mace me daraja"
Tari ne ya sarkefa.
"Wayyo Annah! Karki mutu ki barni"💮💮💮💮
Kura mata ido yayi sosai itama kallon d'anta tayi cikin tausayi tace.
"Jamal!"
"Ai ranka shi dad'e! Ko akwai abinda kake bukata!"Tausayin matar da kuma yadda ta damu dashi, wanda ko uwar da ta haife shi bata damu dashi haka ba.
Girgiza mata kai yayi ya d'an tab'a keken shi ya tura zuwa gaba!
Cike da mamaki take kallon shi, idan idanunta bai mata karya ba! Taga yana kallon ta, kenan yana gani? Itace tambayar da zuciyarta ta wurgo mata,
💮💮💮💮
"Rumanah! Na miki iyaka tun ba yau ba da Jamal kinki ji, na biyaki duk wata hakkin da ya dace! Toh daga yau bazaki kuma ganin shi ba zan sauya miki aiki kije can Katangar bayi ki zauna! Ku fita da ita"
"Ko baki ce a fita dani ba Durdanah zan fita! Durdanah Allah ba azzalumi sarki bane!"
"Hahhhha! K'WARK'WARAH tana da bakin magana!"
"Tabbas! Kinzo inda ya dace! Itama matar sarki ce!"
💮💮💮💮
"Junnuh! Ki bar kuka Mahaifiyarki zata ji sauki! Kiyi mata addu'a"D'ago jajjayen idanunta tayi sannan ta kalli Matar da take duba mahaifiyarta!
A hankali Ta mike tare da zama a kusada Mahaifiyarta tace.
"Tun tasowata muke yawo daga nan sai nan! Har yau bamu huta ba! Sannan baki gaya min wacece Ni ba"💮💮💮💮
Karar fashewar kofin kwalba ya sashi karkawa daga mafarkin da yake, ya lallubo keken shi ya gyara sannan ya hau.
💮💮💮💮
"Galadima! Kana ganin abinda zamu aikata dai dai ne?"
"Shamaki! Iya daidai kenan! Idan muka kashe sarki Jalaludeen mulkin Daura tamu ce!"
"Lallai kai Jakine! Jamaluddin ɗin Fa!"
💮💮💮💮
Kura mishi ido tayi yana jin haka amma bai sashi ya juya ba, sai ma gyaran muryan da yayi can kasa da murya yace.
"Kiyi abinda ya kawo ki, ki bar kallona"💮💮💮💮
"A duniya bani da kowa sai ke! Ummah! Kin hanani kuka kuma kenan kuka kike!"
"Junnuh sun rabani da d'ayana! Sun rabani da kowa sai shi, zan iya tunawa nima baiwa ce a shashin sarki kafin mai dani K'WARK'WARAH shi,Ki kawar da wannan al'adar, ki nuna musu K'WARK'WARAH itama matar sarki ce!"
💮💮💮💮
"Cin Amanar da zaku min kenan! Fulani har dake!"
_Hmmm wata miyar sai a makota_
OUM MUWADDAH.....

ESTÁS LEYENDO
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Ficción históricaA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...