001

1.2K 60 6
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             _{Maimaici}_
*_Return on 28/5/2020_*

*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*

➡️001

Na rasa page 6 da page 24 na wannan buk, amma in sha Allah idan na samu isasshen lokaci zan maimaita pages d'in.

.................Kwance take a saman wata yagaggiyar tabarma da wani komuɗaɗɗen zanen da aka shimfiɗa  a samanta, Cike da jin dad'i da walwala take yin baccin ta tare da yin wani daddad'an mafalki wanda ya tafi da gabad'ai ilahirin hankalin ta wanda har ya yi sanadiyyar mantar da ita yanayin da take gudanar da rayuwarta ta yanzu.

Inda a cikin mafarkinta kuma, take zaune saman wani katafaren dinning table wanda aka kawatashi da ado da kwalliya wanda tsayawa fad'in had'uwarshi ma b'ata lokaci ne.
              cikin isa da tak'ama take yagar cinyar Kaza kamar wadda bata da lakka
          Ci take tana yatsine fuska kamar wadda ke cin kashi, a wani gefe daga saman dnnig table d'in  kuwa wasu kuloli ne kala-kala cike da abinci kusan kala biyar sai wanda ranta yaso ci, a gefe guda kuma soft drink's ne kala daban daban wasu kalaluwan ma ba lallai ba ne ace kasan da su ba..........
              Bata ankara ba ta ji ana kwala mata kira da suna irin na ta kamar haka
          "Fatima.....! Fatima....!!"  ita dik a tunanin ta a cikin  mafarkin ne wannan  kwalelen kiran ke fitowa,  bud'ar bakin ta kad'ai ke da wuya cikin i'sa da tak'ama  ta ce "wai menene?."  saukar wani mugun bugu ne da taji ya yi gaggawar ziyartar k'aramin bakin ta yasa  a fusace ta mik'e zaune domin ganin waye wannan da keson yi mata katsalandan a cikin harkokin ta, kafin ta kai ga sake bud'e bakin ta ta sake sakin magana tini taji an ce   "Shegiya bak'ar munafuka makira, 'yar'iska, mayya, ba zaki tashi ba ne sai naci ubanki shegiya mai k'irar awaki mai fuskar tinkiya, ko ba zaki tashi ba ne?." cikin mugun tsoro mai cike da firgici ta mik'e zaune tana sauraren wajen da muryar ke fitowa, domin ko a cikin mafarki taji sautin  wannan tafasasshiyar muryar zata gane mai ita nantake, sannan tad'an bud'e  idanuwan ta kad'an domin ganin abin da ke faruwa, kamar icce taga Aunty Rukayya tsaye asaman kanta sai cika take tana batsewa, a sannan ta gane cewa ashe d'azun  mafarki ne take, cikin ranta ta ce "Ohni Fatima." bata ankara ba taji saukar wani lafiyayyen mari  a saman lallausar fuskarta, tatassssssssss......   aiko a kan wani irin mugun firgicin da ta tsintse kan ta ciki ba ta san lokacin da ta mik'e tsaye ba.

                Cikin d'aga murya mai had'e da balbalin bala'i  Aunty Rukayya ke magana.

"Ke yanzu dan ubanki ba magana nake maki ba?."
        Cike da karkarwar murya ta ce "Ina jin ki Aunty".

"To dan ubanki maza kije waje ki dauko man zanen khalifa dake  saman igiya shanye  wlhy maza d'auko shi ki kawo man yanzunnan bak'ar makirar banza".  
           Ta ce "To Aunty"
Cike da jin tsoro tare da fargabar fita waje ta dinga tafiya a hankalin kamar wadda kwai ya fashe ma a jiki, kasancewar dare ne misalin karfe *1am* ga shi ko haske babu kuma baka jin motsin komai sai dai na karnuka da ko za'a kashe ka ba zaka ce ga inda suke ba,  sai dai dik da hudun da ya karad'e wajen hakan bai hana ta hango zanen a k'asa ba a yashe
             Cikin hanzari  ida isa gare shi domin daukowa, koda ta duk'a ta d'auki zanen dik ya gama  lalacewa da ruwan dake k'asa, cike da fargaba da jin tsoron abin da zai biyo baya wajen ta ga Aunty Rukayya ta koma daki don sanar da ita abin da ta gani,

    Wata irin k'atuwar kalima ce Aunty Rukayya ta buga kamar wadda akayi ma wani mummunan abu,  Ita dai fatima roqon Allah'n da take yi shi ne  kar Hajiya Kaka ta tashi domin tasan idan ta tashi ba za suyi mata da kyau ba.

Ai kuwa cikin hanzari da zafin nama Hajiya Kaka  ta mik'e tsaye domin har a cikin  baccin ta  take jin wannan kalimar da tayi saurin yanke mata zuciya don ita a dik a tunanin ta wani ne daga cikin ''yan'uwa aka kira Rukayya aka sanar da ita cewa babu shi da sauri ta iso cikin parlour domin tabbatar da abin da take tunani, sai dai da mamakin ta sai ganin fatima tayi tsaye a bakin kofa sai faman kuka take yi, ita kuma Aunty Rukayya ta hakimce zaune a saman kujera kaman wata sarauniya sai karkad'ar k'afafuwa take
            Hajiya Kaka na k'arasowa  wajen su, ta shiga tambayar Aunty Rukayya da cewa "Halan  wani abu ne wannan bak'ar muna fukar ta maki?."
        Ai kuwa kamar daman jiraye take Hajiya Kaka tayi tambayar, Cike da bala'i tare da d'aga murya take magana kamar wata 'yar-tasha  ta ce "Yanzu Hajiya har ni zance wannan shegiyar ta d'auko man zanen Khalipha dake shanye a saman igiya don na shimfid'e shi sabida Ya lalata  wannan da fitsari sai lallab'en ta nake  domin naga dare ne kuma babu haske a wajen  amma dan bak'in ciki da yake  gadarshi tayi, shi be ta yada shi a k'asa cikin ruwan kazanta ina fa kallonta a lokacin da ta finciko shi da k'arfin Allah a saman igiya ta jefa shi cikin ruwan qazanta dik ta lalatashi wai yanzu kuma dand'e bak'in munafurci zata tsareni tana mani kukan iskanci saboda na buge ta a ce dan ba Nusaiba ba ce.!

Hajiya kaka tace "Iyyyeeeeeee lallai  wannan yarinyar ta cika babbar munafuka lamba d'aya  shine ke kuma kikayi zaune kamar wata shegiyar karuwa kina kallon ta ba zaki ci ubanta ba jikinta ya gaya mata?"
          Ai ko daga nan Hajiya Kaka bata tsaya wani b'ata lokacin ta ba wajen jiran amsar da Aunty Rukayya zata ba ta ba, ta wazge aguje kamar wani kwancaccen Doki taje ta kulle d'aki da sakata kamar d'an-sanda zai kama mai laifi, da  hanzari ta zago wayar huta ta nufato gurin da fatima take.
         Ai kuwa nan  fatima tace k'afa me naci ban baki ba, suka shiga zagayen parlourn Ita da Hajiya kaka, idan tayi nan tayi nan Hajiya kaka kuwa an koma kamar wata jaririyar yarinya  ga yanda take gudanar da zagayenta a tsakar daki kaman 'Ita da sa'ar ta (warinta) Ita dai Aunty Rukayya  haushin duniya dana lahira dik yabi ya Ishe ta kamar ta hira sama ta danko wuyan fatima haka take ji akan haushi, Hajiya kan har an gaji da gewayen parlourn  kamar a fad'i k'asa ayi ta mulmula a saman capet haka ake ji akan haushi.
             Kamar k'addara Allah ya jefa Fatima tayi gefen da Aunty Rukayya ke tsaye cikin rashi sani  aikuwa Anti Rukayya dama abin da take jira kenan, ta saka hannayen ta  biyu da k'arfi ta kwashe k'afafuwan fatima sai ga ta kwance a k'asa reram abin tausayi  bata ankara ba kuma taji Aunty Rukayya ta saka k'afarta da iya k'arfin da Allah ya yi mata tayi mata wata mugunyar danna sai da k'ashin k'arfarta ya amsa, wanda har bata san lokacin da ta saki wata irin razananniyar k'ara ba ta azaba Hajiya Kaka kan dama abin da aka dad'e ana jira kenan, wajen sauri azo a dake Jaka Fatima harda fad'uwa aka tashi yi sai dai ita ko a jikin ta gabanta gad'i tadai samu ta iso gurin ta d'in buk'ata ta biya, tun daga nan ta samu sa'arta ta shiga salatin jibgarta kamar Allah ya aiko ta,
                fatima kuwa banda famar kuka ba abin da take yi domin ahalin yanzu cike take da buk'atar taimakon gaggawa.
           Aunty Rukayya kuwa an koma gefe tsaye sai sharbar dariyar mugunta take tana k'ara zuga Hajiya kaka.
                Ita kuma Hajiya kaka an koma kamar injimin markad'e ko alamun gajiya babu a tattare da ita kamar wadda ake k'arama k'arfi sai jibgar Fatima take babu k'ak'k'autawa.
           A dai-dai wannan lokacin ne su kaji an fara dukan kofar d'akin da k'arfi kamar a b'allata Cikin mugun b'acin rai ake masu magana ana cewa a bud'e kofar yanzu ko a b'ab'b'alle ta "wannan wanne irin rashin imani ne da ya yi maku yawa? Ke Rukayya zaki bud'e kofar ne ko kuwa?."
            Cikin ta ne ya shiga ciwon kai a tsorace ta mik'e tsaye tare da fargabar ganin wanda  ke kan kofar.
            Ita kam Malamar duka Hajiya Kaka bata ma San wainar da ake toyawa ba domin har ta fita hayyacinta wajen jibgar Jaka
         Aunty Rukayya na bud'e kofar, da k'arfi aka bangazo ta sai da ta tashi fad'uwa k'asa reram...........
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*Be smart*
*^Pls shere*

WAHALA DA GATA season1Место, где живут истории. Откройте их для себя