♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*EPISODE 46
9:30pm daddy ne zaune a cikin motar shi a bakin get din gidan shi (da yake wannan karon ba tare yake da direban shi ba, ya kasayin horn balantana mai gadi yaji ya bud'e mai ya shigo
Abin duniya dik yabi ya addabe shi musamman lalurar da ta shafe su Ammie dan yau kusan kwanan su goma basu san inda kansu yake ba.
Zuciyar shi ce tayi gaggawar tsundumar da shi a cikin tarkon tunani mai cike da zund'umemen zargi k'arara dangane da Doctor Kulli dan har ta kai ga ta fara ayyana mashi cewa Su Ammie sun dad'e da mutuwa kawai dai baya son sanar da shi ne har sai lokacin da ya tabbatar da kudin shi sun gama k'arewa a wajen shi shiyasa yake wasa da hankalin shi dan kawai yaga ya zalince shiA fili ya ce "Amma zan nemi mafitar wannan al'amarin yanzunnan domin ganin na fidda su a cikin wannan k'angin da suke cike na neman makwancin su."
Wanda hakan yasa ya yanke shawarar cewa gobe tunda safe zai kira 'yan Uwa da Abokan arziki ya shaida masu rasuwar su Ammie domin ayi masu sutura akai su makwancin su na gaskiyaBa tare da b'ata lokaci ba wata 'yar siririyar kwalla tayi mashi zuwan ba zata a saman kumatun shi ba ji ba gani ya antayar da kan shi a cikin dakin tunanin rayuwar su ta baya shi da iyalan shi cikin farin ciki da jin dad'i tare da walwala, nan saiga wata Katifar kuka tazo tayi katutu a wajen da yake, aiko ba tare da b'ata lokaci ba ya dale a saman ta ya kwanta cikin wani raki'in kuka hinhinhinnn baji ba gani kamar k'aramin yaron da ya yini baiga mahaifiyar shi ba.
Sai da ya sha mai isatai ya tabbatar da ya gama k'oshi da shi, sannan ya latsa horn din motar shi,
A guje kamar wani sabon mahaukaci Baba mai Gadi ya antayo ya wangale mashi get d'in, slow-slow Ya shiga daga cikin kamar wani mai jin bacci.-------
Zuhriyyah ce da Nadiya zaune a saman kujeru a waje bakin k'ofar shiga dakin da su Ammie suke, zaune kawai suke suna kallon junan su sun kasa cewa ko uffan kowa da abin da ke damun shi a cikin zuciyar shi, still dai damuwar su bata wuce ta su Ammie ba.
Nan take Nadiya ta jiyo sautin fitowar wani munafukin Twari k'asa-k'asa kamar kukan wata karuwar Mage da ta wuni bata ci abinci ba, har ta d'an share da abin amma sai taji abin ya fara yin yawa kuma a inda take jin shi ne ta kasa fahimta, sai ta dan zunguri k'afar Zuhriya kad'an a daidai wannan lokacin Ita ma ta maido hankalin ta ga Nadiya ta ce " lafiya Nadie?.!"
Ta ce "Aunty Zuhra! wlhy kamar sautin fitowar twari nake ji amma na kasa gane a inda yake fita sai dai ina ji a jiki na kamar a cikin dakinmu ne yake fitowa.!"
Zuhra ta ce "Ke ban son shirme!."
Ta ce "Wlhy Aunty da gaske nake, saurara ma kiji da kan ki.!"
"Ni fa bana son hauka Nadie, meyuwa fa a d'aya d'akin majinyatan dake kusa damu ne kike jin sa dan Allah ki barni da abin da ke damuna.!"
KAMU SEDANG MEMBACA
WAHALA DA GATA season1
FantasiSeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...