044

116 8 0
                                    

♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

Episode>>>44

Gumi ne ya yi bala'in wanke mai fuska dik da sanyin AC'n dake ratsara wajen lokaci guda kuma yadan kwakwalo murmushin k'arfin hali Ya yi gyara murya wanda ba lallai ba ne kaji ba.

Ya ce "Ai kai baka san wani abu ba, Ni kaina bazan baka shawarar zuwa wajen shi ba domin wannan wajen da kake ji mugun waje ne mak'il yaked a 'yan Are'a wlhy sai su ka she mutum ma ba wanda yaji ko ya gani.

Uncle Mustapha ya sake wani murmushi na gefen baki mai cike da abubuwa marar misiltuwa ya ce "Sa'idu kenan ai inje da kaina ma b'ata lokaci ne sai dai in tura mai sojoji suje suyi man maganin shi cikin ruwan sanyi, wallahi ko kashe shi ma zan iya sakawa ayi ba tare da kowa ya sani ba, Unhuhuhun". murmushin cikin mak'oshi kenan,

Nan da nan Sa'idu munafuki yaji wani irin dummmm a cikin zuciyar shi kamar yarikid'e ya koma aljani yab'ace akan fargabar wannan kalamin da yaji ya fito a bakin oncle Mustapha domin ahalin yanzu dik wata Idea ta munafurci da yake tak'amar yana da gabadai ta shude acewar shi, Yau ya shiga ukku bai san lokacin da ya saka hab'ar rigar shi ba ya share gumin da keta keto mai a saman fuska.

Ya ce "Ai kai Alhji Mustapha ba ka san wani abu ba ita Fatima ita ya kamata atsawatar wa domin wannan abin shi ake kira da ba'a rabu da Abu ba an farma Bakar! Yanzu idan har aka dauki wani kwakkwaran mataki ga wannan yaron gobe fa wani zata fad'awa Ni a gani na dik abin da ya faru laifinta ne, Yo inda bata sakar mai fuska ba akwai abin da ya isa ya shiga tsakanin su ko kuma ya isa ya saka ta dole ne! shawara guda daya ce fisabilillahi ka rabata da wad'annan 'yan'iskan yarannan diyan Alhaji Mu'azu sannan kuma sai ka dauki kwakkwaran mataki akan ta dan wallahi k'aramin abu wata rana zai iya zama babba sannan ni zanci gaba da saka idanu akan dik wani motsin ta sabida gudun bacin rana domin wlhy abin da bana son ya faru ga yarana haka yaran wasu ma, amma kayi tunani.!"

Cikin kwanciyar hankalin Uncle Mustapha ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya domin shi harga Allah baya jin k'aunar Fatima ko kad'an a cikin rayuwar sa dik abin da yake mata ya nayi ne dan dole dand'e ba yanda ya iya ne, zaifi kowa farin cikin lalacewar Fatima a rayuwar shi domin tin lokacin da aka haifeta irin so da k'aunar da yaga kowa ya dauka ya azama ta fiye da nashi Yaran wanda hakan ne sanadiyyar tsintar kanshi cikin tsananin k'iyayya da k'yashi a gare ta, sai dai bai tab'a nuna hakan a fili ba.

_Tun yanda yaga alamar saukowar da Uncle Mustapha ya yi cikin Jin dadi da k'arama abu tested ya ce " Ko ya kagani Alhji Mustapha?.!"
Ya ce "Hakan ma ya yi daidai ka kawo shawara mai kyau dan narantse da Allah yau sai ta fadi uban da ya aiketa biyar mazan wato so take ta maida mu mutanen banza ko! to wallahi bata isa ta b'ata mana tanadin da muka shekara muna yi ba!."

Sa'idu ya ce "Hakan dai ne take nufi wlhy Alhj Mustapha dan haka kayi gaggawar daukar kwakkwaran mataki akan ta domin k'arfe da zafi-zafi ake dukan shi.!"

WAHALA DA GATA season1Donde viven las historias. Descúbrelo ahora