*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ>>>25
_Yana isa a bakin get ya ajiye motar shi a waje domin akan sauri bai ma tsaya shiga da ita a ciki ba ,sannan ya nufi cikin harabar gidan,
Ko da ya isa ciki bai cimma kowa a waje ba, Wanda hakan yasa ba tare da bata lokaci ba kai tsaye ya nufi dakin da yake Jin hayaniyar Tv na tashi a can.
Ko da ya shiga ciki Yara kadai ya cinma a dakin da suna kallo, wato Fatima da Zinatu tare da Suhaila,
Da sallama ya k'arasa dakin su Zinatu na hango shi da gudu su kaje suka ruftuma mashi da oyoyoo ita da Suhaila.
Yaji dad'i sosai da ganin su cikin farin ciki, sannan yad'an duk'a kad'an ya d'an tsokale hancin su ya masu wasa da shi,
Da yake sunyi girma sosai wajen d'auka, Suhaila ce kawai yad'an kwikwita hakanan badan yana jin zai iya imata ba ya dauka._Itama Fatima ba abar ta a baya ba wajen nuna nata farin cikin mai cike da kewa ta k'raso wajen da yake ta durkusa har kasa ta gaida shi cikin girmamawa,
Sai dai kuma a yanda take ji a cikin zuciyar ta kamar an saka mata wani irin mahaukacin Mashi mai bala'in tsini an tokare mata Mak'ogoro da shi domin tasan yau kwattaho ya taru sai ta koma gidan da yake tamkar kwanciyar K'abari a gare ta._Cikin wani daddad'an murmushi mai cike da farin ciki ya amsa gaisuwar ta yana mai ajiye Suhaila a saman kujerar da ke cikin dakin, ya juyo kenan da niyar tambayar ta Mummy'n su amma da mamakin shi me zayaga Fatima ta yi?..........
Follow me on wattpad and vote— Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
