*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—**_ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ>>>22_*
_Ꭲun yanda yaga ya kammala aikin daya maido shi gida, sai ya fita cikin tako.,sut..sut..sut kamar wani babban b'arawo Ya koma bakin garka ya dan tsaya Jim kadan sai ya sake shigowa cikin gidan kamar ba shi ba d'auke da sallama tai a baki.
Matan shi na Jin sallamar shi cikin tsantsar farin ciki kowacce ta nufato haryar fitowa waje.. domin tarbar shiSai dai ko waccen su ta na isowa daf'da bakin kofarta ta fitowa waje ta tsaya cak kamar wad'anda aka rike ma k'afafuwa, wanda hakan ba k'aramin farim ciki ya jefa Oga Munafuki a ciki ba da jin dadin da ya riga da ya k'ume shi sabida dama abin da yake son gani kenan ko wacce ta halkanta da abin da yake bakin kofar ta,
Ba tare da ya ce masu ko k'ala ba ya yi sauri ya dauke Buta ya yi makewayi sabida kar ya dak'ile masu kuzari domin da ma shi abin da yake so kawai ganin danben su shiyasa ma yana shigowa cikin gidan ya kulle gidan da sakata dan kar azo wajen raba su idan sun fara,
Tsaye kawai ya ke a cikin makewayi yana sauraren su abin da ke faruwa yana jin dadi yana k'ara jinjina ma kan shi da makircin daya iya hadawa matan shi har ma da mutanen waje.Sumayya ce ta fara cewa
"hmm☹ wallahi dik yanda akayi da Jaki kar yaci kara sai ya ci." Ta k'ark'are maganar ne tana me kallon Asma'u, sannan ta k'ara da cewa "dama an dade ana gaya man amma ban taba yarda ba sai gashi zahiri na gani da idona gashi har abakin kofa ta ana bidar a asirce ni Ni da d'iyata don mubar gidan tunda dama babban takaicin ku kenan ke da diyanki ganin mu a cikin gidan, kuma wlhy yanzu aka fara mu zuba ni da ku shege ka fasa d'an halak sai yanka wlhy."
"ke dan Allah dakata malama ai daman ance tabarmar kunya da hauka ake nad'iye ta, ke har kina da bakin yima wasu gori, kinje dik kin asirce miji ya zama tamkar rak'umi da Akala, kina tunanin halan dik abubuwan da kuke yi ban sani ba ne bakar makira wallahi ni da ke sai lahira dan hakkina da amanata da kika ci wallahi har abada bazan taba yafe su ba, wai yanzu dande bak'in ciki wato an zata Ni ma ba'a sayoman Naman ba shi ne aka jefo man takardar banza a bakin kofa dan na gani na ji haushi, to bara kiji na gaya maki abin da baki sani ba dik abin da kika san ana sayowa ana kawo maki nima haka ake kawo man! mayya kawai."
"Hhmmm Asma'u kenan! ai ba iri na zakiyi ma borin kunya ba domin ga zahiri nan kina gani, aini tun yanda naga banji d'uriyar ki a waje ba na san akwai kullalliyar da kike kullawa sai gashi assirin ki ya tonu, kuma wallahi har abada ba abin da zai same mu ni da d'iya ta sai alkhairi, ta Allah ba taku ba, kuma ku da ke biyar mu da Sheri Allah ya maida maku abinku ya koma kan ku."
"Ke ni wallahi bana da lokacin cacar baki da ke idan fad'a kike so sai yanzu abawa hamota iska." A cewar Asma'u, sai Sumayya ta ce
"Ke har kin isa na tsaya sa-in-sa dake mtswww" nan take tayo kukan kura da hanzari ta fad'a kan Asma'u aka fara kaftawa._B'angaren Sa'idu Munafuki kuwa ba abin da yake yi a cikin Bathroom sai godiya ga Shed'an daya cika mashi burin sa na taimakawa ya buga masu gangar shi aka fara bada nishad'i, dariya kuwa ko wacce kala ya samu yi yake harda su tsalle yana godewa Allah da ya azurta shi da mata 'yan bala'i.
