015

154 12 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

➡️015

Sai da ta tashi shan k'asa, sai gata tsaye tsamgal a tsakiyar su sai famar huci take tana furzar da iska a bakin ta, haka ma magen (Cats) basu ma san da zuwanta a wajen ba.
           Irin manya-manyan nan ne wad'anda ake yi ma kirari da (mazurai) kusan guda ukku ne irin wad'anda basu da tsoron nan ne ko kadan kuma basa jimirin daukar raini da wulakanci😝

Hajiya Kaka kam da ta  gama fusata har sosai har sai da fuskarta ta koma jawur kaman attarugu tare da k'ara  kumbura kamar ta fashe, sai dai abin da bata sani ba shi ne, suma su Oga Mazuran dik sun gama harzuk'a da katse masu farin cikin su da take k'ok'arin yi suna cikin shanawar su 😜 Lol

Ai kuwa akan wani  mugun bacinran da taji nan take ya lullub'e ta bata san lokacin da ta dauke d'ai daga cikin Mazuran nan  da wani irin mahaukacin shuri wanda sai da ya yi sanadiyyar buguwar Mazurun a bango, kaji abinnan ya ce guguff kamar anyi wurgi da wani k'atoton dutsi.

Wani irin hiranyowa ne da ya yi  sama-sama ya fad'o a saman  hannun Hajiya kakatare da kame mata tsokar hannu da gabadai ilahirin k'arfin hak'oranta ta ta cije takin tak'i saki ta kafe sosai hak'oranta suka zauna damm a saman hannun Hajiya Kaka.
        Cikin wani mugun tashin hankali Hajiya Kaka ta buga wata kafirtartar kyallowa kamar wata k'aramar yarinya 'yar kimanin shekara biyu, bata san lokacin da bakin ta ya dinga fadin
  "Wayyoo..wayyoo..wayyoooo Allah na ta cire man hannu yau na shiga ukku ni Lauratu wayyoo ni Allah na.. wai dan ubanku ba wanda zai fito waje ne?, wayyoo na shiga ukku dan Allah ku taimake ni, shaggu munafukai, wai bakwa jina ne."
          Kuka hinhinhin take kamar ranta zai fita,
             magen kuma  kamar ana k'ara mata qarfi tak'i sakin hannun sai jini ke fita.

"Wayyouhunhihihiii. Ina neman taimakon gaggawa dan Allah da Annabi ku fito waje yau ni nashiga ukku mak'iya sun man yawa hihihiuhuhn, jama'a ba kowa ne ta sake buga wata razananniyar k'ara wadda sai da hankalin kowa ya tashi tun daga cikin d'aki aka shiga yin rigangan din fitowa waje tsakanisu su Uncle's Mu'azzan da Mukhtar domin dik hankalin su a tashe yake da Jin wannan razananniyar k'arar da Hajiya kaka ta buga hanik'am.

Nan take yara suka cika gidan,  kan kace me? yaran gabadai sun wazge aguje sun tafi su tallata ma wad'anda basu ji ba inda suka dinga shiga gida gida suna kiran gashican ana cire ma Hajiya kaka hannu.!

Da gidan Uncle Almustapha da gidan Uncle Uzaifa da gidan Alhaji ibrahim har ma da mak'otan su na kusa da na nesa, kowa yayo gudu domin ganin shedun-zur, wasu nayin murna har da godewa Allah wasu kuma na tausayin ta har da su koke koke.

Uncle Aminu da su Uncle Mu'azzam kowa  rigangan isowa gurin da Hajiya kaka take yake domin dukan su suna cikin gidan ba wanda Ya fita illa Uncle Aminu da dawowar shi kenan a gidan bayan ya huce.

Ita kuma Aunty Rukayya tin lokacin da  ta k'are shan wannan dan neman dukan  bayan komai ya lafa ta koma daki ta haye gado bata san lokacin da baccin k'arfin hali ya dauke ta ba, dan ita harta ma manta da tahowar yaran ta Wad'anda tun lokacin da su kaga an fara mazgar mahaifiyar su suka bar gidan aguje suna kuka.

Cikin tashi hankali ita ma ta fito waje, ita da Hajiya Saudatu ba abin da  ke fita a cikin bakin su sai kalmar INNADILLAHI WA'INNA ILAIHIM RAJU'UNA

Cikin hanzari da zafin nama Uncle Aminu ya riga su Uncle Mu'azzam kaiwa wajen, bai san lokacin da ya yi ma wannan magen wani irin mugun bugu ga baki ba har sai da ta fadi k'asa tuyyyyy tana fad'owa ta gudu.

Haka ma Hajiya Kaka da tari ga ta galabaita hanikan  bata san ma lokacin da ta zame jiki ta fad'i k'asa ba,
           Cikin mugun tashin hankali Su Uncle Mu'azzam  suka dauke ta su kayi daki da ita, kafin ka ce me  har jama'a sun cika gida ko wajen takawa ma ba bu dik irin girman wannan gudan sai da aka cika shi da mata da maza kowa jiran yake ya tabbatar da  abin da ya kawo shi  da kuma jin wani mummunan  labari akan ta.

guda-guda suka dinga shiga cikin d'akin  dubata domin ganin k'wan sai dai dik wanda ya fito sai ya yamutse fuska kamar anwa zawo yayyafi🙊 wad'anda ba su samu shiga ba  jiran d'ai suke suji wani mummunan abu ya same ta Ko kuma suga  an dauko masu hannun annuna masu  kamar yanda aka gaya masu d'in.

Sai dai da mamakin su dik wanda ya shiga  saibdai yaga tanbunan hak'oran magen  suka yi mata tambo a sama hannun, daganan wasu suka shiga yin tsaki ciki-ciki suna fad'in Allah ya isa ga wanda ya zo ya tado su daga mazaunin su, domin su ba haka suka so gani ba, wasu kuma murnar ce suka shiga yi ganin ba hannun ba ne ya cire kamar yanda aka gaya masu ba.

Nan dai hayaniya ta gauraye ko ina wanda hakan ne ya yi sanadiyar falkawar ta cikin hanzari, ko ida saka mata bandejin ba ayi ba ta tashi ta farma masifa da bala'i ta ce
"Iyyeeee to sannun ku da zuwa babbak'un munafukai,  da ma na sani ai wato an zo ganin k'wam ne ko? dan  a gani idan na mutu aje zuwa wajen shela."
             Nan da nan wajen ya yi tsit hayaniyyar ma sai aka daina kamar wajen da aka d'auke wutar nefa, kowa sai famar sauraren abin da take fada  yake yi kamar masu sauraren Tafsir,

Ta k'ara da cewa "To  wallahi zama daram-dak'am a cikin duniya kamar yanda bakwa son gani na haka zaku barni sai sanda lokaci na ya cika na barin duniyar munafukai shegunan banza 'yan-tsiya wad'anda ba abin da suka iya sai tsintse da tsegumi, kuma wallahi na rantse da Rabbul-samawati wal-ardi dik wanda bai bace man da gani ba Ubangiji Allah ka-isar man ka fidda man hakki na bisa ga kan uban kowa".

Anan wasu suka ce "Ba amin ba" Cikin mugun jin haushin wannan bak'ar addu'ar aka fara watse taron a hanzarce kowa yabar gidan suna mai jin haushin irin wannan halin na Hajiya Kaka.

Wasu kuwa  cewa suke  ina ma ace zana-izar ta ne suka zo yi da sai sun fi kowa farin cikin wannan ranar.

          haka dai wasun su suka yi ta fadin albarkacin bakin su har su ka kai ga watsewa kadan-kadan kowa cike yake da abin da ke cin shi a cikin zuciyar shi.

Family din cikin gidan ne kad'ai basu fita ba amma dik wani makwabci da bare wad'anda suka zo wucewa suka ji ana yin wannan hayaniyar  kowa yan bar gidan dai rai a bace tare da fad'in  albarkacin bakin shi.

....

Alhaji Kabiru shi da Alhaji Ibrahim sun dawo daga masallaci wajen sallar La'asar, suka tsinkanyo taro jama'a a kofar shiga gidan su an cika mak'il kamar wajen da aka yi zanen Suna ko kuma d'aurin Aure,      Cike da wani matsanancin tashin hankali suka nufato cikin gidan ba tare da sun tsaya tambayar kowa abin da ke faruwa ba domin  dik a tunanin su  Rasuwa ce akayi a cikin gidan, sai dai kuma ganin mata da yawa na fitowa a cikin gidan tare da tsegumin da suke famar yi wasu na cewa Allah ya kara wasu kuma na cewa Allah yasa wannan hannun gobe-gobennan ya rube har sai an kai ga d'ebe shi.

Su Alhaji Kabiru na isowa daf da shiga cikin gidan suka ji wasu mata su ukku suna fadin Allah ya sa gobe-gobennan muna cikin dakunan mu zaman mu muji labarin mutuwar ta kai tsaye wlhy da Allah kadai ke hana min yin wani gagarumin party a wannan ranar,  guda kuma ta ce wallahi Ni kuma da sai na taka rawar da bantabayin irin ta ba,  guda  kuma ta ce wallahi Ni kuma da sai nayi sadakar Dubu Ashirin kyauta ba tare da na  ji haushin kyautar ba  Ko kuma bak'in cikin rasa su da nayi ba.

haka dai kowaccen su take ta famar fadin albarkacin bakin ta tare da kyakkewa ta dariya kamar su fadi k'asa suna cikin haka sai ganin su kayi  sun yi kicib'us da su Alhaji Kabiru a wajen..........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere

WAHALA DA GATA season1Onde histórias criam vida. Descubra agora