*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*EPISODE>>>34
_wannan ba kowa bane illah Azzalumin bokanta da Ake ik'irarin ya dade da barin duniya wato Fintinkau, sanin dik lokacin da taje wajen shi idan zai gudanar da tsafin shi sai ya fara kiran sunan Tsinyu, Shi ya sa farat guda ta iya gano shi sai dai bata ida tabbatarsuwa ba sai da ta ganshi ido da ido sannan ta tabbatar.
Tana cikin yin wannan tunanin ne mai cike da ban firgici da ban Al'ajabi sai ganin tayi yana k'ok'arin mik'a mata wannan k'azamar kwaryar mai cike da k'azanta zallar ta.
Kauda kan ta tayi hefe cikin mugun firgici da mugun k'yamatar wannan kwaryar tun da babu k'afafuwar gudu balantana a tashi a wazge.
Kafin ta ankara sai ganin wannan kwaryar tayi zaune daram a saman gabadai ilahirin hannayen ta, Wa'iyu billah wani Irin Bak'in Aljanin tsoro ne ya shiga cikin ta wanda bata taba tsammanin tana dashi ba a dik tsawon rayuwarta ta.
Daganan kuma taji tana k'ok'arin yi ma kanta dure da k'arfi-da-yaji Kafin ta kaiga ambatar sunan bokan ta an riga da an tamanta da Ubangijin halittu, Sai jin wannan kwaryar tayi a saman bakin ta d'asss tana kwad'ad'ar wad'annan babbak'un ruwan dake cikin ta kamar mai shan ruwa sanyi_ Sai da ta sha su sosai da sosai ta jisu har a cikin tumbin ta suna yawo, sannan aka janye wannan kwaryar daga bakin ta a daidai lokacin ne kuma ta fad'i kwance a wajen kamar matacciya ko wani motsin kirki babu a tattare da ita.
_Hankalin Balkisu ya yi matuk'ar ar tashi da Faduwar da taga Mahaifiyar ta tayi,
Da rairafe mai had'e da jan k'afafuwa kamar (mai shan Inna) ta k'araso wajen da Ammie take tare da jijjiga mahaifiyar ta ta, Ihu take son yi amma babu bakin yinsa, kafin tayi yunk'urin taimakon Mahaifiyarta tini ita ma taji alamun ana k'ok'arin yi mata d'uren da wannan kwaryar, saukarta kawai taji a saman bakin ta Sai Kamdamar ruwar take yi Ita ma babu kakkautawa. daga bisani Ita ma aka janye ta a bakin ta, ba tare da b'ata lokaci ba ita ma ta zame jiki ta fad'i...
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
pls share
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season1
FantasySeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...