043

115 8 0
                                        

♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

Episode 43

Ko da suka isa daf da bakin get din asibitin, mai mashin ya sauke shi, domin ba'a bari a shiga da abin hawa a ciki sai mutum ya yi sign Ko kuma irin Emergency haka.
Sannan ya fiddo Naira dari biyu ko canji babu ya mik'amai tare da nuna harkar fankama had'ida hurar hancin nan mai kama da kunnayen shanuwa tare da shan k'amshi yana tafiya, dan jinshi yake kamar wanda ya dauke wata irin jadduniya sukutun ya mik'a ma mai machine din, haka mai machine din ya karb'a ba yabo ba fallasa dan shi dik a tunanin shi kudin da zai bashi sai sunfi hakan,
Cikin Jan wani dan siririn tsaki na bak'in cikin abin, ya tayar da machine din shi bai bar wajen ba sai da yarufeshi da kalmar Allah ya'isa.

Ya na ida shiga a cikin harabar asibitin, direct sai office din Uncle Almustapha ya nufa, yana isa ya yi knockin sai da aka ba shi Izinin shiga ciki sannan ya fada cikin zanzana da rawar jiki.

Ya koyi sa'a domin shi kad'ai ya tarar a cikin office din ba abokin shi ko guda da ya kawo mashi yawo wanda hakan ne yak'ara bashi kwarin gwiwar ida shiga ciki, cikin zumudi tare da sallama.

Tun yanda Uncle Mustapha ya hango shi cikin wani dan guntun murmushi wanda bai kai ciki ba ya amsa mashi sallamar shi sannan ya ce "A'aaa Sa'id yau da kan ka ko'ida warkewa bakayi ba! ya gida ya jikin na ka?!"
ya ce "Alhmdu lillah da sauk'i wlhy ya aiki?"

"Lafiya k'alau"

Sai dai tun kafin a bashi izinin zama a saman kujera ya soma cewa "Wlhy Alhji Mustapha Fatima ce na kama a dakin wani k'ato shi ne musabbabin zuw......!"
Tun kafin ya iyar da maganar ta shi Uncle Mustapha ya ce "Bissimillah Malam Sa'id dan Allah zauna a saman kujera tukun.!"
Sai bayan da ya zauna ne Uncle Mustapha ya ce "ina jinka."

Kamar daman jira yake ya yi harzarin sharb'e maganar da cewa, "Wallahi dama na dawo ne daga wajen duba shagona ne zan wuce gida na tsinkanyo ta ita da Binta diyar Alhaji Mu'azu."
Cikin mamaki Uncle Almustapha ya ce "Binta shin?.!"

Ya ce "Eh ita din dai lalatacciyar yarinyarnan."

Ya ce "Ina Jin ka!"

Ya ce "To sai na gansu wani yaro yazo da mota zai d'auke su kafin ink'araso wajen da suke domin in tabbatar da ainahin inda zasu je, idan ya kama ma na hana su tafiyar d'in na hana su sabida naga yaron ne kamar ba wani kimtsatstse ba ne dan karya je ya lalata mata rayuwa a banza tunda daman ita Binta'r ba wani sababben abu ba ne a wajen ta ba, kafin na k'araso wajen su har wannan Yaron ya cira Fatima sama ya dank'ara mata wani makeken kiiss a saman goshi sannan ya cinnata cikin motar shi gaban su gadi sai kwasar dariya suketayi abin su, nan Ita ma Binta ta bude gidan baya ta shiga ciki suka tayas.

Sai nayi saurin tare masu hanyar dan na samu na hana su tafiyar, suna tsayawa cikin hanzari nayo kan motar, sai da suka bari nayi kusan kawowa daf da motar su kayi dariya harda su tafa hannu da wannan namijin, sannan suka fizge motar dak'arfi badan nayi saurin kaucewa ba da takaina zasu bi su wuce saida nakai ga faduwa k'asa reram
Nan da nan na tare mai machine na haye muka bisu daga baya dab'b'oye dan karsu ganmu su kara gudu harsu b'ace ma ganin mu, sai ganin muka yi ya shigar da motar shi a cikin wani katafaren gida kamar na Karuwai, banyi wata wata ba nace mai machine din ya ajiye ni a bakin get din, na biya shi kudin shi, sannan na bisu daga ciki. har dakin da suka shiga, sai dai ba'abar ni ba na k'arasa daga cikin ba, nan na dawo dai dai ga Tagar dakin na tsaya Ina hango dik abin da suke yi, sai ganin nayi suna k'ok'arin cire kayan su ni kam nayi saurin walkadowa daga baya domin bazan iya kallo' wannan mummunan abin ba sannan kuma gashi a cikin watan da muke mai tsarki, kayi hak'uri dan Allah Alhaji Mustapha wallahi da Ina da dama da tin wuri na dakatar da tafiyar ma to kasan Yaran yanzu ne sai a slow Ita ma Fatima'r dik kwaya nawa ce!?"
ya k'are maganar ne cikin wani sabon salon kukan munafurci.

Uncle Almustapha kam kallon shi kawai yake cikin wani irin yanayi na ban mamaki sannan gabadai ya tattara yardar shi ya dora akan wannan zancen k'aryar, bai yi wata-wata ba ya tambaye shi "Ina ne wajen?."
cikin muryar tashin hankali,

Lokaci guda Sa'idu munafuki ya tsayar da shasshek'ar kukan da yake yi ya dinga inda-inda tare da rabe-raben idanuwa kamar agolar nufawa, yana k'ok'arin kwakwalo dibarar da zai ma Uncle Mustapha dan ganin ya dakar da wannan bak'in al'amarin dake shirin bata mashi tsarin sa......
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang