♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*Episode 47
A b'angaren Alhaji Usman kuwa, Yana katse kiran cikin wani matsiyacin sauri ya tayar da motar shi kamar wani zautacce.
Aiko tun da Baba Mai gadi ya ga irin wannan walkadowar da ya yi da motar kamar ya tashi sama da alamun fita zai sake yi ya yi gaggawar tashi tsaye cikin hanzari domin bude mashi get dan a yanda ya fuskance wannan halin da Daddy ke ciki zai iya bangaje get din ya wuce
kafin ya ida wangale get din gabadai tini Daddy har yakai ga k'arasowa wajen aiko cikin wani matsiyacin hira sama kamar tsuntsu Baba maigadi ya ce har yanzu ina son rayuwa ta, nan take wazge daga nan domin kadan de ya rage Daddy yabi ta kanshi ya wuce.
*** *** ***
Bai zarce ko ina ba sai a bakin parking space d'in dake cikin Asibitin Sokoto Clinic, ko gyara parking din baiyi da kyau ba ya fito waje cikin wani matsiyacin sauri mai kama da gudu-'gudu, ba tare da wani b'ata lokaci ba ya antaya a cikin harabar Asibitin, direct bangaren Aminity Room ya nufa, tafiya yake cikin sauri, dan shi baik'i jinin ya kyafta girar shi ba ya ganshi tsunbulbul a cikin dakin da su Ammie suke.
Dakyar dai da wala'haula yakai ga kofar shiga dakin cikin zanzana mai cike da zumudin son ganin halin da iyalan shi suke ciki.Ya bangaza k'ofar dakin da k'arfi Allah sai da ya kusa dabewa, sai dai shi ko ajikin shi, sannan ya fad'a cikin dakin da sallama.
Cak ya tsaya yana kallon wadda idanuwan shi suka fara yi mashi to zali da ita wato Balkisu da har tayi wankanta ta canza kayan jikin ta sai su n
Nadiya dake zaune kusa da ita a saman gado sunai mata fira tana dariya had'i da jefa lomar tuwo a cikin bakin ta ita kuma Ammie an shege toilet tun dazu da sunan watsa ruwa dan a samu k'arfin jiki, wanda Ta kusa share 1hour a ciki.Ya na iza gambun dakin ya rufe hankalin kowa ya dawo wajen shi cikin mugun farin ciki suka taso gabadayan su suka rungume Daddy'n su har da ita ma Balkisu'n ba abar ta abaya a cike da murna mai kama da zallar farin ciki.
A daidai wannan lokacin ne Ammie ta fito daga cikin toilet nan fa farin ciki ya sake ninkuwa a wajen su musamman ma Daddy da shi yanzu ne ma ganin shi da su.
Masha Allah abin dai sai son barka Ammie da Balkisu an tsallake rijiya da k'aya, sai kuma a jira hari na gaba tsakanin su da Boka Mintsinkyu hmmm..Doctor kulli ne ya shigo a daidai wannan lokacin domin sake binciken lafiyar su don lokacin da aka gaya mashi falkawar su baya kusa, yana shiga yacin ma Daddy a ciki, cikin farin ciki suka gaisa sannan Daddy ya yi mashi godiya abisa kwarewar da ya nuna wajen gudanar da aikin sa ta hanyar bada tashi gudunmawa a wannan Bak'in Al'amari da ya shafe su Ammie.
Ya ce mashi "Aiwannan ba komai ba ne, dik abin da su kayi sunyi ne abisa taimakon Ubangiji sabida haka shi ya kamata mugode ma.!"
Daddy ya ce "Wlhy haka ne doctor!"Sannan doctor ya k'ara duba lafiyar su tare da tambayar su abin da ke damun su, Ammie ta ce Ita dai tana jin kasala-kasala kamar jikin ta nai mata nauyi, Balkisu ita ma Ta ce abin da ke damun ta kenan."
Ya ce "Ba damuwa akwai Allurorin da za'ayi masu sannan za'a daura su akan hanyar su ta shan magunguna, Idan dai har su kabi k'a'idodin wadannan magungunan da za'a daurasu akai to zasu samu saukin wadannan abubuwan nan bada jimawa ba.!"
Gabadayan su sukai mashi godiya, sannan ya fice daganan daddy ya rufa mashi baya suna tafe suna fira cikin annashuwa, saida suka isa a office'n d'in Doctor Kulli bayan sun zauna ne Doctor ya ce mashi "Ni da keta famar in gama duba su d'in in kira ka na tare ka da albishiri sai gashi kai har ka ma rigani ganin su.!"
Cikin wata irin dariyar su ta manya Daddy ya ce "A'aaa wannan karon kam diyarka ce ta riga ka!"Suka kece da dariya ya sake cewa " Alhmdulillah Doctor gaskiya nayi matuk'ar godiya ga Allah (S,W,A) da ya wanke mana damuwar da take damun mu tasss a cikin gaggawa kuma da irin jajircewar ka ce yasa har aka kai wannan lokacin domin ni tini har na fidda rai akan su, gashi Allah ya nuna man ikon shi da matsayin shi a wajen bayin shi, gaskiya nayi matuk'ar godiya a gareka doctor Allah ya sakama da mafificin abin da kayi man.!"
Kulli ya ce "Habaa Alhj dan Allah ka daina man godiya hakanan, tarayyar mu ai ta wuce wannan komai nayi maka ai kaina nawa iyalan ka ai kamar nawa suke dan Allah kabdainabman godiya Alhji Usman kaifa amininabne na gaske sannan ko ga wani naga irin wannan matsalar ta faru ai zanyi gaggawar ceto rayuwar shi ne daga halaka balantana ma naka habaaa ai sai inda karfina ya k'are.!"
Daddy ya ce "Gaskiya hakane Kulli! Allah dai ya tsare gaba.!"
Kulli ya ce " Ameen Ameen"_Sannan Daddy ya ce "Yanzu kima sallamar su kamar zata kai yaushe doctor?!."
Ya ce "Insha Allah ina sa ran ko gobe indai sun ida wartsakewa za'a iya sallamar su sabida binciken mu ya nuna mana ba wata sauran matsala da take damun su illar wannan kasalar da suka ce suna ji, shi ma kuma wannan ba wani babban abu ba ne mai girma sabida dadewar da su kayi ne a kwance ya janyo masu wannan matsalar amma ina sa ran insha Allah zuwa gobe zasu koma daidai, idan muka tabbatar da hakan to zamu shirya masu takardun su na sallama daga yau zuwa Tuesday.
Godiya Daddy ya sake yi mashi sannan sukayi sallama yawuce b'agaren su Ammie ya sake duba su, ya dauki hanyar shi ta zuwa gida.
.....
Ta b'aangaren Fatima kuwa........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
