*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*EPISODE>>>33
Tun lokacin da Ammie ta fuskance dagaske wajen su ne yake k'ok'arin tunkara, nan da nan taji Cikin ta ya fara Mird'awa akan wani irin mahaukacin tsoro da yake ta addabar rayuwar ta.
Ita kam Balkisu tun lokacin da suka falka Suka tsinci kansu a wannan mugun wajen tini tayi suman zaune da kuma mugun Nadamar biye ma Mahaifiyar ta da tayi har ta ka ga tsintar kanta a cikin irin wannan Mumunan yanayi na Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un._ Aiko ba tare da wani bata lokaci ba, suka ji k'arar fitowar wata babbar TUSA. BURRRR🙊 daga wajen Ammie Kamar wajen da wani mahaukacin BOOM ya tashi, sannan a daidai wannan Lokacin ne kuma Tsinyu ya ida k'arasowa daf dasu Rik'e da wannan kwaryar ta ruwan K'urjin a hannun shi.
_Nan take Wajen ya ida gaurayewa da wani irin Mahaukacin warin tsiya wanda Idan da mai karatun wannan littafin yana kusa da su da babu shakka har Suma ma zai iya yi.
_Abubuwa wajen kala biyu su kayi bala'in damuwar Balkisu afujajun.
Na d'aya dai, Mahaukacin tsoron da ke damun ta
Na biyu kuma, wannan munafukin warin da ya keta famar ziyartar hantunan ta na bala'i wanda har ta fara jin zuciyar ta na bid'ar kasa daukar shi, dan Ji take kamar ta tashi aguje ko haukace ta zuba Idan de har zai sa ta samu wannan damar da zata gudu daganan sabida Idan har taci gaba da zama a wannan wajen to babu shakka wannan irin warin dake dukan hancinta zai iya sanadiyyar da zata rasa rayuwar ta kai tsaya a wajen.Kafin su ankaro tuni suka ga wasu Mutane Masu fuskokin Akuyoyi Idanuwansu kuma Jawur kamar Ninannen attarugu duk sun gana gewaye wajen da suke sannan ga k'ari da k'arau wata wawiyar dariya mai cike da ban firgici da ban tsoron da suke zuba ma su, dik suka ji sun rurrude masu kunnaye kamar su fashe.
Lokaci guda kuma su kaga wawan haske kamar wutar murhu gabadai ya gauraye wajen. a sannan Ammie tak'ara tsorata ta sanadiyyar ganin fuskar wanda ake kira da Tsinyu wanda hankalin ta Idan ya yi dubu sai da ya tashi domin tabbas I dan ba gizo bane I danuwanta ke mata ba wannan Mutumin mai siffar Aljanu ba zata tab'a mantawa dashi ba...
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
BẠN ĐANG ĐỌC
WAHALA DA GATA season1
Viễn tưởngSeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...