*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
_{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—**➡️004*
To wallahi ba abin da zai tayar da ni yanzu, diddika yaushe ne na kwanta har na samu yin baccin? wannan ai bakin cikin ne mtsww." taja tsakin ta mai ban haushi Sannan ta kara da cewa ta "To sai na tashi d'in" Ta gyara kwanciyarta taci gaba da baccinta cikin horewar shed'an.
Ita kam Aunty Rukayya dama ba sallar take yi ba Sai taga dama, kwasar baccin ta kawai take hankalinta kwance, zuciyarta zaune bata ma falka ba ballantana tasan abin da yake gudana
Shi dai Alhaji Kabiru tun lokacin da yaji ta fara masifar ta Ya wuce ya bata guri.
Fatima kam daman Ta saba, cikin hanzari ta tashi ta bude daki taje ta dauro alwalarta sannan tadda sallar ta.
Su Hajiya Kaka kuwa tuntuni shedan Ya yi wata Uwa-duniya da su ta mugun jin dad'in yin baccin. minsharin su kad'ai kake ji da keta famar fitowa waje babu k'ak'k'autawa.
Fatima na k'are sallarta taje ta fara dibar ruwa kasancewar ma akwai fanfo a gidan shi ne saukin da ta samu a gurin dibar ruwan.
Sai dai dik da hakan d'ibar ruwan take tana zuba su a muhallinsu amma kamar bata zuba komai a ciki sabida girman dirom-dirom d'in, irin manya manyan nan ne masu bala'in zurfin tsiya har wajen guda biyu
Bayan tukanen ruwa (( randa)) irin masu qattan cikakkannan ne
Kasancewar dori akwai tiyo wanda ake jawo ruwan dashi amma Hajiya Kaka dand'e mugunta ta dauke shi ta bawa masu wankin kafet dake kusa dasu kyauta Alhaji Kabiru shi da ma ya saka aka sayo bai ma san anyi hakan ba.
Tana tsaka da dibar ruwan tayi wani azababben tuntub'e da wani dutsi da ita sam bata san dashi ba, kawai sai gata a k'asa kwance reram ita da bokitin da take d'ibar ruwan da shi, dik da irin mummunan raunin da taji a k'afa wanda har ya yi sanadiyyar fitowar jini a wajen malalala kamar fanfon da ya burge ya na zubar da ruwa.
Ko kad'an hankalinta bai ma kai ga k'afar ba balantana har ta san halin da take ciki, ita dai damuwar ta guda ce ta yanda za tayi da wannan bokitin da Ya tsage na Hajiya Kaka uwar bala'i Ita da ko cokalin ta aka yada a k'asa cikin rashin sani ko waye kai sai taji kamar ta shak'eka balantana bokitin da take ji kamar rabin rayuwar ta.Ta na cikin wannan tunane-tunanen ne ta tsinkayo fitowar Aunty Rukayya a d'aki tana k'ok'arin fitowa waje ta aza Khalipha a saman Fo, a hanzarce ta yi sauri ta kauce daganan dan kar ta samu damar ganin ta.
Sai dai abin da bata sani ba shi ne, Anti Rukayya jira kawai take Hajiya Kaka ta tashi daga nannauyan baccin da take ta sanar da ita b'arnar da Jakar su tayi mata yau, dan tun lokacin da Fatima ta fadi k'asa Aunty Rukayya ta hango ta tin a cikin daki
Cike da mugun tsoro Fatima ta lab'e a wani gefe na daban ta na jiran ganin lokacin da Aunty Rukayya zata koma daki domin ta samu damar ajiye shi a wani gurin salin-alin ba tare da ta gani ba domin ta na da tabbacin dik sanda Aunty Rukayya ta lura da abin da ya faru yanzu to Allah kadai zai iya kwatar ta a hannun Hajiya Kaka
