003

334 25 0
                                        

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             _{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

➡️003

Da hanzari ta juyo ta kalle Aunty Rukayya da ita sam ba tayi tunanin ta ji ta ba.
            Cikin wani irin yanayi na b'acin rai da niyyar falla mata wani wawan mari tare da rufe ta da d'anbanzan duka domin a halin yanzu daidai take da su har tana tunanin Idan har ta kama da ayi danben sai su ware a bawa hamota iska domin ayi ta ta k'are kowa ya san matsayin sa, sai dai kuma a wani b'angare na daban daga cikin zuciyarta ya yi nasarar dak'ile mata dik wani yunk'uri da take k'ok'arin aiwatar wa dan huce takaici ta hanyar bawa zuciyarta ruwan sanyi ta sha tare da tuli-tulin maganganun da shawararin da suka dace wanda hakan ya yi nasarar galaba a gare ta ta dakatar da abin da ta so aiwatar wa ta hanyar sakar ma su wani mugun murmurshi wanda yafi duka ciwo sai da Hajiya Kaka ta tashi zubda hawayen bak'in cikin abin domin ita ba haka ta so ba, so tayi ta tamka masu yanzu a bawa hamota iska dan ita yanzu tsaf take ganin zata iya dukan ta har ma ta ji mata mummunan rauni wanda sai ya yi sanadiyyar zuwanta asibiti, tana cikin yin wannan zazzafan tunanin ba ta san lokacin da bakin ta ya tsuke ba kamar mun....Kaza taja wani d'an ballaja'un tsaki mai tattale da bak'in cikin rashin biyan buk'ata, haka ma Aunty Rukayya da tun d'azu ta riga da tayi mutuwar tsaye a kan tsoron abin da zai biyo baya sai dai tun lokacin da taga alamun Hajiya Saudat ta nuna halin ko in kula da zancen, hankalin ta yad'an kwanta tare da k'ara ma kanta wani fattakeken k'aton kai da famkamar cewa ita wata babbar shegiya ce anan da ta ke, kyalkyalkyal ta sake fecewa da dariya har da su kyakkewa sai ka ce wata sabuwar kamu sannan ta k'ara da cewa "Aikin banza yin shara a kasuwa ai dama ba yanda aka iya da m......... a hanzar ce Hajiya Saudat tabar wajen domin ba zata iya tsayawa sauraren wad'annan banzayen k'ananan maganganun ba daga bakin wadda ta ke kallo a tafin hannun ta domin ta san idan har taci  gaba da tsayi a wajen za'ayi tashin hankali ne wanda ba a tab'a yin irin shi a gidan ba amma ita kawai ba ta son tashin hankali ne da yau sai Aunty Rukayya ta yabawa Aya dan zak'in ta dan sai tayi mugun nadamar abin da ta aikata mata yau, haka dai ta ci gaba da tafiya ta na tunanin wannan abin har ta ke ganin tun da take ba'a tab'a yi mata irin wannan d'anyen rashin mutumcin ba  sai yau da rana ta b'ace a gare ta  sai dai ta na da tabbacin ita ma komai daren da d'ewa reshe zai juya ma Mujiya tana cikin wannan tunanin ne har ta isa part d'in ta ko da ta isa da mamakin ta har Alhaji Kabiru ya yi bacci Ita ma kwancin ta yi domin ta gani ko zata iya yin baccin sabida dik ta tuno da abin da Aunty Rukayya ta mata ita da Mahaifiyarta ba k'aramin k'ona mata rai yake yi ba.
A yanda take ji a zuciyar ta kamar ta fashe da kuka ko zata samu salama a cikin zuciyar ta,  a fili kuwa ta ce "hmm wallahi dan d'e ana barin halak dan kunya ne amma  da yau kin gane kuren ki na bud'e bakin ki har ki samu damar zagi na..... a cikin ran ta ta k'ara da cewa  "Amma  ina da tabbacin wataran zamu gauraye  ni da mahaifiyar ki" , sannan k'ara gyara kwanciyar ta da niyyar  ko zata samu tayi baccin ko da zai iya rage mata wannan radadin da take ji a cikin  zuciyar ta sai dai ko da hakan kuma ta kasa, sai tunane-tunanen  irin kalaman da suka yi mata take yi, da taga abin yana son yafi k'arfinta  sai ta dangana shi  a gurin Ubangiji, inda ta dinga fadi *"LA'ILAHA ILLALLAHUL HALIMUL KARIMU,, SUBHANALLAHI RABBU ARSHIL AZIMI,,ALHAMDU LILLAHI RABBU ALAMINA"*

WAHALA DA GATA season1Où les histoires vivent. Découvrez maintenant