045

120 8 0
                                        

♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

EPISODE 45

A b'angaren su Ammie kuwa, waiwayowar su baya kad'ai keda wuya suka hango wasu d'in-d'ima-din-diman Akuyoyi Zaune a saman kujerun shan-iska suna shak'atawar su ko waccen su taji d'an uban eyeshadow ga wani dan-uban lipstick da suka mannawa bakunan su sai famar walkiya yake kamar k'illin-billin. Sai famar sharholiyar suke, sai dai tun lokacin da suka an karo da su Ammie suka mik'e tsatstsaye a gurguje suka nufato su cikin wani matsiyacin gudu.

Aiko cikin wani mugun firgici su Ammie suka neme hanyar fita wajen su ma aguje, wanda fitar su kad'ai ke da wuya, ko da suka waiwayo daga bayan su basu ga ko k'urar wad'annan Akuyoyin ba, nan da nan su kaji hankalin su ya d'an kwanta har da godewa Allah,
Sun duk'a k'asa kenan suna saukar da nunfashin su sama'sama kamar masu nak'uda k'asa-k'asa suka fara jin ihun mutane na fitowa kamar wajen da ake gudanar da wani gagarumin Yak'in kwatar 'yanci, sai can suka hango wata skeleton a guje kamar fanka tuk'e da Baro sai famar tinkaro su take, kan su ce "HA" tini suka hango su gurguzu guda ko wannen su rik'e da wani mummunan makamin shi a hannu had'i da Frying-pan.

Basu ankara ba suka ji wannan Zakaran Ya ce masu "Kad'an ma kuka gani!"
Sai a sannan Ammie ta tuno da shi a hannun ta domin ita harta ma manta da shi kwata-kwata Balkisu ce ta d'anyi k'arfin halin cewa "Ammie! gasunan fa tunkaro mu suke gabadai, wayyo ni yanzu ina zamu b'uya yau mun shiga ukku munga takan mu wlhy nasan daga Yau tamu ta k'are.!"
Sai jin su kayi wannan bak'in Zakaran ya ce masu "Yawwwa ''Yan-Na'u! sai mu antaya a cikin wancen kogon dake kallon mu.!"

Aiko da jin hakan, cikin wani matsiyacin gudu su Ammie suka fece gashi wadannan azababbin Skeletons har sunyi kusan cin masu, sai famar kururuwa suke suna ihu, sai dai da sukaga alamar da gaske su Ammie zasu tsere masu, nan take d'aya daga cikin skeletons d'in ya jidda haushin shi a saman Bayan Balkisu, inda take cikin gudanar da aikin ta na gudun wahala taji saukar wani gundumemen abu a saman kwankwason ta kamar Guduma
Aiko bata san lokacin da ta sake wata irin razananniyar k'ara ba mai cike da ban firgici, sai da koda haka ba tayi k'asa a gwiwa ba wajen gudanar da aikinta na ci gaba da zund'ar wani matsiyacin gudu,
Haka Ita ma Ammie tuni ta halkanto da hakan, dan ita ma kad'an d'e ya rage a antaya mata gudumar a goshi, sai dai tana jin yanda Balkisu keta famar sharb'ar kuka tana gudu rik'e da Bayan ta, sai dai ba abin da ta iya domin Ita ma ta kanta take.

Dak'yar da walahaula suka samu suka kai ga wannan kogon har suka kurd'e a ciki, nan take kogon ya rufe da su wanda hakan yasa suna jin lokacin da wadannan skeleton's din suka iso daf da wannan kogon sunata famar yin ihu suna bubbugar dutsen da dik abin da suka dauko su rakkata mai dan ya burme su samu damar fasowa coki amma abin ya citira.

Tunda su kaga wannan kogon ya yi bala'in rufewa da su a ciki, nan take hankalin su ya sake ninkuwa wajen tashi, nan take suka dinga ta kwasar gudu suna sharb'ar Ihu cikin wani mugun tsoro sannan ga wani mahaukacin sautin kidan da ke tashi a wajen kamar a Club d'in America ga wadu fitillun dake basbanniya a wajen kala'kala sai sun kawo kuma su d'auke.

WAHALA DA GATA season1Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt