*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*
*_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*
*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*
EPISODE>>>35_*
_Bayan kamar 30second haka, ko waccen su ta farka cikin karfin jiki da kuzari da kuma rashin tsoron sama-sama domin yanzu dik wani Mugum tsoron da suke fuskan ta gabadai ya fara gushewa a cikin zukatan su har ma a fuskokin su.
_Basu ankaraba su kaji Boka-Mintsinkyu cikin wata kakkaurar Murya wadda tafi kama da ta mutane bila a dadin yana cewa.
"Barkar ku da shigowa fadar Minsinkyu, ya ke Zainabu da Balkisu."
daga bisani kuma sai ya yi shiru, Jim kadan ya sake cewa
Nasan baku san ko ni wanene ba! hasalima wadda ta baku labari Na Ita ma bata san komai dangane da ni ba kawai dai ji na ne take amma bata tab'a kawo kanta gareni ba,! abin da nake son ku sani a yanzu shine Ni ba Mutum ba ne. NI ALJANI NE aljanin ma Miskili marar Imani kuma Marar tausayi! sannan dik wani wanda ke buk'atar aiki a waje na sai na jarabe shi da abubuwa da dama wad'anda zasu sa tsoro a cikin zuciyoyin ku daga bisani kuma nafara gushe maku shi a cikin zuciyar ku domin bana harka da matsorata, sannan dik wani boka da kuka sani a fadin duniyarnan yana aiki ne a karkashi na, sai dai Ni kuma ina da sharad'i wanda dik ya kuskura ya bijire ma umarni na koda a cikin rashin sani ne to babu shi babu jin dadin Rayuwa a cikin fadin duniyarnan domin na kan hukunta shi daidai da abin da ya aikata agate ni, Na san kin san wannncenn sosai," Cewa da Boka TSINYU da tun d'azu tsaye tsaye kawai yake kamar icce ko wani salihin motsi babu a tattare da shi.
Sannan ya kara ce mata "domin nasan kin gane ko wanene shi, sai dai baki san dalilin da yasa ya ke nan ba ko?.
"To doka ya taka shi ya sa karshen shi yazo mashi a haka kuma har duniya ta nade bazai taba dawowa daidai ba, sannan a koda yaushe zai kasance ne a matsayin da kuka same shi ne a yanzu.!"
Sannan ya k'ra da cewa "dik wani mahalukin da ya kuskura yat aka dokar da na kafa na tsawon tsawon kimanin shekaru Dubu saba'in da shidda {76,000Years} ni kuma na d'auki alwashin sai na nkkasa shi koda Kuwa ku ne.!"
Cewa dasu Ammie....
nan da nan Ko waccen su taji alamun Hantar ta na kad'awa sanadiyyar wani mahaukacin tsoro da ya
tsokalo su, kasancewar dazu sunriga da sun gama wartsakewa da tsoron..amma yanzu sai su kaji kamar na yanzu ma yafi na d'azun ta sanadiyyar wannan Mummunan furucin da su kaji ya fito daga bakin wannan tantirin Aljani.
Sannan ya k'ara da cewa "dik wani assiri da kika san ya yi a dari, to yananan har yanzu bai karye ba, domin na mik'a shi ne a hannun daya daga cikin Aljannan da suke taya shi yin aikin, kema kuma dan nasan zaki zo hannu na ne shi ya sa ban wargaza shi ba, sai dai dik kuka kuskura kuma kuka bijire ma umarni na kuwa dik wani Abu da kika san an tab'a yi maki na assiri to sai ya kare sannan zan nakkasar daku ku koma tamkar dabbobi a wajen Bil'adam daga bisani kuma sai na maida ku ciyawa na bawa dabbobi na su cinye.!"
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
