*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—**_ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ :21_*
_Amma da mamakin ta sai Jin tayi Uncle Mukhtar ya ce "Balkisu jira ni zan dawo yanzu"
"a'a shin ba tare zaku tafi ba ne" a cewar Hajiya kaka... ya ce "Wai ina son in duba shi ne ko yananan sabida kar ya zan kuma ya yi masallaci."
"masallanlaci yanzu karfe 12pm fa wasu ma ko daga bacci ba su tashi ba balantana ma suyi aikace-aikacen gidan su sai gashi an d'auko masu bak'in sauko tun da sassafe".
Ta karkare maganar ne tare da waiwayo wajen da Balkisu take zaune, tadan watsa mata harara ta bayan ido ba tare da ita Balkisu'n ta halkanta ba sannan ta ce
" to sai ka dawo shanshani uban yawo uban kwashe-kwashe_Shi dai Uncle Muktar Allah-Allah kawai ya keyi kar Balkisu taji har ta kai ga jin zafin maganganun da Hajiya kaka ta dage take yi dan ya san bada kowa take ba sai da shi da Balkisu, cikin inda-inda da fargabar ganin bacin rai a fuskar Balkisu ya juyo gare ta amma da mamakin sa sai ganin Ya yi ta sakar mashi da wani mahaukacin murmushi wanda sai da Ya yi sanadiyar fadawar shi cikin wata uwa duniya ta daban, cikin ran shi ya ce " Alhamdu lillah da'alamun kamar bata ji abin da Hajiya ta ce ba domin baiga alamun damuwa a tattare da ita ba, Ꭺmma fa a yanda ta nuna mai a bayya ne,
Haka dai shi ma bai san lokacin da ya mayar mata da martani ba domin hakan bakaramin farin ciki ya saka shi ba sannan ya ce "Jira ni ina zuwa yanzu kinji".
A shagwabe ta kad'a mashi kai alamar to!" kamar tayi kuka
ita dai Hajiya Kaka dik haushin abin ya gama turmuk'e ta, bata san lokacin da ta janye fuskarta da duban da take masu ba kamar wata babbar munafuka._Ita dai Balkisu ba abin da take sakawa a ran ta sai idan ta koma gida dole ita da mahaifiyar ta suje wajen BOKA MINSINKYU domin tun yanzu a asirce mata Mukhtar din ta tun kafin ta kaiga shigowa gidan domin taga alamun Hajiya Kaka zata iya zame mata matsala nan gaba zata iya hana ta taka rawar gaban hantsin ta domin tana son ta samu damar cin karen ta babu babbaka,
.....
Bayan fitar Uncle Mukhtar cikin bak'in hali Hajiya Kaka ta tashi ta shiga bathroom din cikin daki domin watsa ruwa,
Ta tashi ko kala bata cema Balkisu ba, ta shige cikin bathroom ta kulle gambu gafff da karfin Allah,Balkisu ta danyi wani murmushin ta na mugunta sannan ta ce "Wlhy watarana zaki ce ba kiyi ba! zaki san dani kika yi,"
sannan ta tashi ta dauki tsintsiya ta fara share-sharen d'akin tana yi tana tsake-tsaken takaici masu cike da ban haushi domin ko a gidan su abin da ta tsana kenan aiki._har ta gama shara ta fara kakkantar kayan wanke-wanke jibgege guda wanda ita ma sai da ta razana da ganin shi, amma ko wulgawar Hajiya Kaka bata gani ba sannan Uncle Mukhtar har yanzu bai dawo ba, bata san lokacin da bakin ta ya furta "Sheguna yan'iska"
_sannan ta je ta dauko omo da susun wanke-wanke wanda dama suna ajiye ne a saman tagar dakin kayan komutstse, koda waje kana iya hango su, abin da bata sani ba shi ne Hajiya Kaka ko da ta shiga ciki bathroom aikin komai bata barkata ba tun dazu zaune take saman kujerar wanka tana tunanin yanda zata ci uban Aunty Rukayya anjima idan ta dawo
_Sannan shi kuma Uncle Mukhtar ko da Ya shiga dakin Baba bai ganshi ba wanda hakan ya sa yasan dik yanda aka yi yana masallaci, kai tsaye ya wuce part d'in su yaje yadan watsa ruwa.
•••••
_Koda Hajiya Kaka ta gama lalurar ta ta fito daga wajen wankan taga waje ko ina tatas sannan ga wanke-wanke har anyi an gama kaya sun wanku tatatas, wanda haka kawai taji Balkisu ta shiga ran ta har ta manta da wata damuwar da ke damun ta,
tana tsaye tana kallo ko ina cikin annuri, sai ga Balkisu ta dawo tare da Uncle Mukhtar, dan dama tana gama wanke wanken tadan kimtsa jikin ta, koda Uncle Mukhtar Ya zo, ya dan zagaya da ita cikin gidajen 'yan'uwan shi ya kaita ko ina suka gaisa har da gidan Yayan Mahaifin su wato Alhaji Ibrahim, masha Allah , a ko ina taje Sai anyi mata goma na arziki.Bayan sun dawo
ko da suka cimmata tana tsaye ta tsurama ikon Allah ido domin bata tab'a tunanin haka a gurin Balkisu na dik da wannan shi ne karon ta na farko da ta fara ganin ta sai dai tana yawan jin labarin ta a gurin Uncle Mukhtar,
Tana ganin su ta sake fuska tana murmushi ta ce "har kun dawo" Uncle Mukhtar Ya ce "Eh wlhy Hajiya dama na dan zagaya ne da ita a cikin gidajen 'yan'uwa domin ta gaida su,
Sosai tayi farin cikin jin hakan sannan ta ce "hakan ma yana da kyau, Allah yayi maku Albarka,"gabadayan su suka amsa da "Ameen"
haka dai suka zauna cikin farin ciki da annashuwa ana ta kwasar fira.Balkisu ba tabar gidan ba sai misalin karfe 5pm dan Alhaji kabiru bai dawo gida ba sai da ya yi sallar La'asar sannan ya shigo gida bayan ya ganta, sosai shi ma ya yaba da hankalinta matuka kuma yana yin tarbiyar ta yaburge shi sosai sannan ya yi masu tafatan ALKHAIRI tare da goma na'arziki ga Balkisu sannan su kayi godiya suka wuce.
*****
_banganren Fatima kuwa tun lokacin da ta tafi gidan su tun tuni ta manta da batun su Hajiya Kaka a ran ta domin gata ba irin wadda bata gani a wajen iyayen ta musanman a wajen Mummy da kuma kannenta har bata son tunowa da saura sati daya Uncle Mukhtar yazo daukar
Ta*****
"Wai yau me matannan suke nufi ne? har yanzu fa sun kasa yin fad'a Yau kusan satin su daya fa.! kai Wallahi ba zaiyu ba ina son ganin yanda zasu caccab'i junansu dan haka yau dole sai nayi kallon dambe a cikin gida na, ko da dai na san abin da zanyi yanzu."
a cewar Sa'idu Munafuki, sai da ya biya ta wajen mai Nama ya saye tsiren shi na dari da hamsin sannan ya biya ta wani guri inda mutane basu cika biyowa ta wajen ba yaci mai isa tai sannan ya wuce da kingin takarndar a gidan shi,
ya koyi sa'a yau koda ya shigo cikin gidan dik suna cikin dakin su, nan da nan ya fiddo wannan takardar da yaci nama ya jefata a bakin kofar dakin matar shi guda, Asma'u wadda dama yau ba ranar girkin ta ba ne, sannan kuma ya fiddo wata 'yar karamar leda wadda ke kunshe da wani abu kamar magani a cikin ta amma ba komai ba ne illa tulin maganin Iska, sannan ya jefa ta a bakin kofar shiga dakin Sumayya....
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
ESTÁS LEYENDO
WAHALA DA GATA season1
FantasíaSeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...