*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
_{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—**➡️007*
Ko kadan basa son ganin abin da ya tab'a ta ko kuma ya faru da ita Idan ma cikin yaran mak'ota suka dake ta ko cikin wasa ne ta'aza kuka yanzu Hajiya Kaka na yafa mayafin ta taje gurin mahaifiyar yaron ta zubda tarkacen rashin mutumcin ta acan.
Goyo ba'irin wanda batasha ba a gurin Aunty Rukayya dik da tsakar dare ne ta falka tadan fara fitinarta yanzu kana ganin Aunty Rukayya ta falka komai nauyin baccin da take yi sai ta mik'e tsaye ta dauki fatima ta goya ta dinga jijjigata har sai lokacin da tayi bacci sannan ta samu tadan gincira kwance goye da Fatima a saman banta domin ta san yanzu idan ta jishsheta wata sabuwar fitina ce zata sake tashi sai safe sannan take jiddata koshi sai idan ta falka daga bacci ko Fatimar ta tayar da ita da fitina, haka ma ko tufafi Aunty Rukayya zata dinka sai anyi ma Fatima ko doguwar riga ce a ciki, sannan dik inda zata tafi Fatima na biye da ita, ko fita zata yi zuwa wani guri tare suke tafiya
Haka dai su kayi ta tafiyar da al'amurran su cikin tsantsar Kaunar Fatima tare da tattalinta da kuma bala'in son ganin farin Cikin ta.
Kwatsan sai ga auren Aunty Rukayya ya tashi zangargadi cikin dan k'ank'anen lokaci akayi komai aka gama cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tashin hankali baBayan kwana biyu Aunty Rukayya ta zo ganin gida ba yanda bata yi ba akan Hajiya Kaka ta bata rik'on Fatima amma tak'i
Haka dai Aunty Rukayya tayi hank'uri dik da irin k'aunar da take yiwa Fatima amma haka ta dangana dan ta san tun da Hajiya Kaka ta turje idanuwan ta haka ba zata tab'a ba yar da Fatima gare ta ba.Bayan wasu lokutta Aunty Rukayya ta samu juna-biyu har ta haife d'iya macce wadda taci sunan ta da NUSAIBA, lokacin biki aka sha bukukuwa marar misultuwa an ci an sha har ma wasu sun kwasa sun tafi da shi komai dai a wadace akayi shi.
Bayan haihuwar Nusaiba dik wani farin ciki da jin dadi da walwala ya k'are agurin Fatima domin dik wata soyayya da ake nuna mata tsakanin Hajiya Kaka da Aunty Rukayya dik suka juye suka koma wajen Nusaiba
Wahala ba irin wadda bata sha ta dalilin Nusaiba tun tana ganin abin a matsayin kuskure har ta dinga daukar shi a matsayin k'iyayya.
Shekara guda da 'yan watanni ke tsakanin Fatima da Nusaiba.
Nusaiba dai yarinya ce wadda ta taso cikin shagwaba ga bala'in sakarci da rashin ganin girman kowa da kuma rashin d'a'a had'i da kuma makirci tun tana 'yar k'ank'anuwar ta ta saba da munafurci da anyi ance da had'e-had'en fad'a
Sannan kuma ko kadan bata ragama Fatima domin irin tsanar Fatima da take ji na tsokalo ta ya ma a kira shi da k'iyayya ya koma zalinci tsagoron shi.
Fatima tun tana yar shekara hudu aka saka ta a primary school kasancewar ta tashi da babban jiki Idan ma ba kasan shekarun ta ba a wannan lokacin zaka ce yar shekara shida ce Allah ya yi mata baiwar da ko wanne malami take burge shi akan hankalin da gare ta da natsuwa ga kuma kwakwalwa da saurin fahimtar karatu dik yanda yake kuma gata da natsuwa kaman wata babbar mace, tana class5 a primary skull aka yi mata
jumping ta rubuta exam's tare da 'yan class6 ta shiga babbar makaranta wadda take gaban primary schoolIta kuma Nusaiba ta kasance yarinya ce dak'ik'iya wadda komai bata iya fahimta da kyau sai famar shashancin da take yiwa mutane, tana class3 tin yanda taji ance za'a yiwa Fatima jumping ta matsa ma iyayen ta akan Ita ma ayi mata domin kar Fatima ta wuce ta.
Haka aka yi tattaki har izuwa school d'in su aka gana da headmaster d'in su domin gabatar da wannan k'udurin amma sam malaman makarantar suka ce basu yarda ba ko Class4 take ko sai ta kai Class6
sannan zata k'are Makarantar.Haka Aunty Rukayya ta yi ta matsama ATTAHIR wato baban Nusaiba mijin ta ) akan sai an fidda Nusaiba daga cikin wannan makarantar a saka ta wata domin Ita ma ta yarda da k'udirin diyar ta, haka dai Attahir dik da baya son canza makarantar dole Ya canza mata ya kai ta wata private school aka saka ta Class4 da niyyar idan ta shiga Class5 Lokacin da ''yan Class6 zasu rubuta Exams sai
ayi mata jumpingbayan Fatima ta shiga Jss1 a lokacin tana da shekara 10, ita kuma Nusaiba ta shiga class5 ta nada shekara takwas da 'yan watanni,
A kwana a tashi, shekara ta sake zagayowa inda Fatima kai tsaye ta shiga Jss2 ita kuma Nusaiba a sannan ta gama primary school dan anyi mata jumping d'in
Ta jona wata makaranta aka kai ta Jss1 amma ko da hakan ta so a kai ta Jss2 domin kar Fatima ta wuce ta, sai dai tun a wajen interview ta fad'i inda komai bata sani ba ko Jss1 din da qyar ne aka amshe ta.
_____
A halin yanzu Aunty Rukayya ta nada d'iya kusan guda ukku wad'anda Nusaiba ce babba a cikin su sannan bayan shekara biyu aka haife Marwan bayan wasu shekaru Aunty Rukayya tayi b'ari har wajen biyu na ukku ne Allah ya tsaida inda ya ci sunan shi da Kabiru amma ana kiran shi da (Khaleepha) shekara biyar ne tsakanin Marwan da khalipha.
Tun lokacin da Khalifa yake da wata biyar Attahir ya sake Aunty Rukayya ta dalilin zagin iyayen shi da take yi dik lokacin da su ka samu wani dan sab'ani a tsakanin su, tunda ta koma gidan su ya amshe diyansa gabadai Khalifa kadai ya bar mata kasancewar yana shan mamma ba'a kai ga yaye shi ba.
Sai dai wani lokacin idan anyi hutun makaranta yakan kawo su suga mahaifiyar su suyi ko da sati daya ne ko biyu yazo ya dauke abin shi su koma gida.
Tun a lokacin da ta dawo gidan su da zama ba wanda ya yi ko b'atan hanya yazo gurin ta da sunan neman auren ta sabida kowa yasa halin ta da na mahaifiyar ta ba mutunci ne da su ba.
____
Yanzu Hauwa'u wato mahaifiyar Fatima ta nada diya wajen guda ukkuDa Fatima da Zinatu da Suhaila
Shekara bibbiyu ne a tsakanin su tun lokacin da ta haife Suhaila bata sake samun wani Cikin ba
Haka dai al'amurra su kayi ta tafiya wasu cikin jin dadi wasu kuma cikin bacinrai da tsangwama da bak'in ciki.
*QARSHEN TARIHIN*
_________Muhammad ne a tsaye wato mahaifin Fatima wanda kusan dik rabin abin da Hajiya Kaka tayi a Idon shi dik da irin tausayin yarinyar shi da yake ji na tsokalo shi amma hakan ya cije dan yaga alamun muzanta a tattare da Ita wanda hakan yasa har yanzu ta kasa tashi a saman ruwan cikin Fatima da ita har yanzu bata ma cikin hayyacin ta.
*PLS KUYI MANAGE DA WANNAN GOBE BA ZAN SAMU DAMAR TURO WANI BA AKWAI WANI UZURIN DA TA GIFTA MIN NE SAI JIBI IDAN ALLAH YA KAI MU,,, I'M REALLY SORRY MY FAN'S*
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be - smart
Pls shere
ESTÁS LEYENDO
WAHALA DA GATA season1
FantasíaSeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...