013

144 14 0
                                    


*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
_{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

➡️013

cikin mugun tashin hankali kowa ya nufato wajen da Hajiya Kaka  take, kafin su ida k'arasowa awajen kuma kowa Ya tsaya cak yana kallon ikon Allah

Cikin mugun bacin rai da zafi nama Hajiya kaka ta mik'e tsaye kamar wata army, Sai cika take tana batsewa ta ce,
       "Dan'shegiya tantirin dan'iska wanda Ya yi godon iskanci bak'in bunsuru munafukin Allah dan kazat-kazat."

Ba wanda ya iya cewa da ita ko uffan domin mamaki da tsoron Allah  ya cika idanuwan dik wanda ke wajen sabida ga yanda   ta bawa k'asa hakkin ta ba wanda yayi tunanin zata ma iya tashi zaune  balantana har tamik'e tsaye da kwarin ta ta dinga yin  irin wannan  bakin sababin da  koda yaushe ba k'arewa wa yake ba.

Cike da bacin rai ta nufato su tare da danneman bakin bala'i  sai zage'zagen ga kawai ke fitowa a bakin ta, jikin kowa ya dauki rawa domin su dik a tunanin su aljannunta ne suka tashi🤣Lol

Tana isowa daf  da su ta d'aga hannun ta sama-sama  ta dauke Uncle Mu'azzam  da wani wawan mari mai cike da bacin rai zallar shi  sannan takara da cewa "billahillazi anyi hasarar rayuwa kuma anji kunya dan shegiya jikokin karuwwai  jikokin 'yan tasha wad'anda su kayo gadon fitina."

Ran Hajiya Saudat idan Ya yi dubu sai da ya b'ace domin wad'annan kalaman na Hajiya kaka ba k'aramin bajanta rayuwar ta su kayi ba domin tunda take ba'ataba jifan ta da irin wad'annan miyagun  kalaiman ba marar asali marar tushe ba sai Yau.

Hajiya kaka ta sake daga hannun ta sama da sunan sake marin Uncle Mu'azzam  sai Jin tayi wani k'ak'k'arfan   hannu ya rik'e mata hannu a bayan ta.

Ai kuwa nan cikin ta ya fara mirdawa sannan ga wani mahaukacin fitsarin da yake son kubce mata s anan wajen da take, jikin ta ya fara makarkata cikin kasala da mutuwar jiki ta dinga waiwayowa kadan kadan domin ganin ko waye wannan k'ak'k'arfan  mutum daya dank'e mata hannu haka ko motsawa ta kasa iya yi da shi........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere

WAHALA DA GATA season1Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin