*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
_{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*➡️012
A lokacin da Hajiya Kaka ta shiga gidan Uncle Uzaifa lokacin Uncle ATTAHIR Ya kawo NUSAIBA da MARWANU gida dan dama ya kan kawo su dik lokacin da aka yi masu hutu a skull domin suga mahaifiyar su
Ko da suka shigo cikin gidan lokacin FATIMA ta tashi daga bacci har ma ta dan fito waje ta sha iska.
Koda ta hango su Nusaiba daga nesa suna tafowa ta washe baki cikin tsananin murna da farinciki ta mik'e tsaye da guda domin ta tarbo su.
Ita kuma NUSAIBA tun yanda ta hango FATIMA na nufato su da sunan wajen su zata zo domin tarbar su, daga nan haushi da bak'in cikin Fatima da take ji ya k'ara turmuk'e ta domin ita harga ALLAH ta tsane FATIMA ko son ganin ta bata yi, dan dai kam FATIMA ta zamar mata tamkar haki a mak'ogoro ta rasa yanda zata yi dan ta daina ma ganin ta acikin rayuwarta da kuma idanun ta, kafin FATIMA ta kaiga 'isowa wajen su, ta lura da dingirisar da take yi wajen tafiyar ta da sauri ta dubi k'asan k'afar FATIMA domin ganin inda tambon yake, sabida ta samu damar aiwatar da wani mummanan abu a saman k'afar, ko da taga inda Fatima ta samu mummunan rauni a k'afar ta taji wani bala'in dad'i ya ziyarce ta har da k'ara godewa ALLAH (S W A) daya nuna mata inda raunin yake, cikin gaggawa domin ta samu damar aiwatar da shirinta cikin sauk'i ba tare da wata wahala ba. Bata san lokacin da tayi wani zazzafan murmushi ba mai dauke da mugun ta zallar ta.
Kafin Fatima ta ida k'arasowa har ta shirya shairin da zata yi mata ko zata samu salama a cikin rayuwar ta.FATIMA na ida k'arasowa wajen su cikin sauri da tsantsar farin'ciki MARWAN yazo yarungume ta yana murnar ganin ta kamar yanda take yi masu.
Ta dubi bangaren da NUSAIBA take cikin farinciki da tsantsar qauna taje gurin ta tana ta washe baki kamar wadda aka yi ma albishir da kujerar zuwa hajji
Ita kuma NUSAIBA tayi kamar bata ganta ba, ta k'ara yamutse fuskarnan kamar wadda aka ce ma ta taka kashi a k'afarta, ta wani bintsere gabadai ilahirin labbanta suka koma sama kamar wata bintsirarrar Kaza,
Dik da FATIMA ta lura da haka amma sai ta share da abin domin ta saba da irin wannan abin a gurin NUSAIBA, da gudu tayo wajenta tana kiran oyoyoo...oyoyoo tayo wajenta daniyar ta karb'e akwatin su ta shiga da shi ciki, nanfa NUSAIBA tayimata wata irin bankad'a wadda sai da ta fad'i k'asa kwance, sannan ta saka takalman k'afarta masu tsini ta danne k'afar FATIMA wajen da ciwon yake a kafarta, aiko cikin tsantsar mugun bala'in jin ciwon data ji ya ziyarce cikin k'assan k'afarta da kuma mugun radadin da wajen yake yi mata, ta buga wata irin k'arar da ita ma kanta bata san lokacin da tayita ba sabida tsananin azabar da take ji a cikin k'afar kamar ta d'ebe, nan take jini ya dinga fita malalala yana taruwa kamar wajen da aka yanka Dabba.
cikin tsananin takaici da mugun jin haushin abin da NUSAIBA tayi ma FATIMA
Uncle'Al-Ameen ya fito daga cikin daki domin yaga lokacin da NUSAIBA ta tunkude ta har ta kai da faduwa k'asa kafin ya fito daga cikin dakin har ta saka k'afarta ta danne mata inda jimuwar take,
cikin Hanzari da mugun sauri ya'iso daf'da wajen da NUSAIBA take nan take ya saukar mata da wani lafiyayyen mari a saman kuncen ta wanda ita ma sai da takai ga kasa rik'e kanta a wajen da take, sai gata a k'asa reram ta fad'i a daidai wannan lokacin ita ma Aunty Rukayya ta fito daga cikin dakin, cikin mugun firgicin ganin abin da Uncle'Aminu ya aikata a gurin gudan jinin ta, wato NUSAIBA wadda take jin ta tamkar rayuwarta, wanda hakan yasa bata san lokacin da ta daga hannun ta guda da niyar d'auke Yayanta da wani wawan mari akan diyar ta.
Ai ko cikin zafin Nama ya dank'e hannun ya mirgid'e shi sai da ta saki wata irin razananniyar k'arar da bata ma san lokacin da tayi ta ba, nan take ya falla mata wani irin wawan mari wanda sai da ya yi sanadiyyar fashewar bakin ta da Jini Nashe-nashe sannan ya ci gaba da dukan ta kamar ALLAH ya aiko shi.
ihu take kamar ranta zai debe cikin mugun firgici su Hajiya Saudatu ita da 'Ya'yan ta gabadai su kayo waje domin ganin abin da ke faruwa.
Cikin hanzari Uncle Mu'azzam shi da Uncle Musaddiq su kayo wajen shi domin cecenta sabida yanayin yanda yake dukan ta ko kashe ta zai iya yi a wannan lokacin
Aunty Rukayya kuwa sai ihu take tana kuka hanik'an har sai da muryar ta takai ga shak'ewa domin kukan ko fitowa baya yi da kyau, dan dai kam a wannan lokacin ta galabaita dai-dai wa dai-da domin tana cikin wani matsanancin hali na taimakon gaggawa
su Uncle Mu'azzam daqyar da wala-haula suka samu nasarar kwatar ta a hannun shi domin suma sai da suka ji jiki wajen rirrik'e shi
Ita kuma tun yanda taga an cece ta a hannun shi a sannan tayi wata nannauyar ajiyar zuciya ta qarfin hali ta kwabce mata, sannan ta dinga d'uro mashi ashshar tana ta zagin kan su da kan ta domin dik wani zagi da zata yi mashi sai ta gama da iyayen su.
sannan ta dinga fadin "mugu bak'in azzalumi mai matacciyar zuciya dan'iska marar imani wanda ba abin da ya iya sai cin amana, kuma wallahi dik dukan da kayi man sai na rama shi a gurin wannan munafukar, dan wlhy yau kwattaho yattaru sai naci ubanta tunda har ka iya daukar hannunka akan wannan shegiyar bakar munafuka debabbiyar albarka kayi man irin wannan dukan wanda ko maqiyinka ba zaka yi ma irin shi ba narantse da Allah sai na ci ubanta".Shi kan Uncle Aminu yanda zuciyarshi keta tafarfasa ji yake yi kamar ya je ya shak'e mata wuya har sai lokacin da yaga ta dauke numfashi sannan ya saki,
Ana cikin yin haka sai ga HAJIYA'KAKA ta wazgo aguje rik'e da kulilin abincin kamar wadda aka biyo aguje za'a kashe ta
Bata ankara ba sai jin ta yi tayi Wani mummunan tumtub'e da wani k'atoton dutsin dake cikin shigifar garka wadda zata yi da kai a cikin filin gidan inda ake yin casun😜.
Sai jin kayi abin nan ya ce " gufff " tare da tulle-batsulle a wajen ta fad'i reram kamar wata tihwa, kulolin dake hannunta kuwa gabaki daya ko wacce ta nemi hanyar ta ta fecewa
Jin faduwar wani abu guguffff a shigifar garka yasa hankalin kowa Ya dawo a
wannan wajen.....
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere
