026

125 12 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ>>>26

Kyau da kuma girma,
gashi hasken fatar ta yak'ara fita kamar wata Ba'india, kamannun ta da komai nata sak ya koma kalar na mahaifiyar ta
Sai da ya sake kallon ta da kyau domin tabbatar da abin da yake gani ba magalki ba ne, har ya tsunduma cikin duniya tambayar kan shi da cewa, Ita ce ko kuwa gizo ne idanuwan shi ke mashi, wata zuciya tace mai ba wani gizo ita din dai ce Fatima'r da ka sani, aiko bai san lokacin da bakin shi ya furta "ALLAHU'AKBAR Allah sarki lallai dik yanda WAHALA take ko kadan bata kai ga kwanciyar hankali ba."

Dik da shi ma Mahaifin nata ba'a barshi a baya ba wajen kyau Da kuma kyan'hali ba, domin zan iya cewa gaba daya kaff Family'd'in su babu munanne a cikin su, Sabida kyawon nasu ya samo asali ne ta sanadiyyar iyayen su da kuma Kakannin su gabadayan su Toronkawa ne haka suke tamkar Larabawa, haka ma matan su daga Buzaye sai Fulani

_Cikin ran shi Ya ce "Allah sarki fatima ashe dik ᏔᎪᎻᎪᏞᎪ ce ta maida ki kamar wata komod'addiyar ᎷᎪᏩᎬ yanzu kuma kin samu ᏩᎪᎢᎪ kin koma tamkar wata shahartacciyar balarabiya, kaiii duniya kenan, duniya mai cike da abubuwa na ban al-ajabi.

_Yana cikin yin wannan tunanin ne ya jiyo muryar Mummy a bayan shi tana mashi sannu da zuwa, sannan tak'ara da tambayar shi mutanen gidan.
Gabadai ya ce "suna lafiya k'alau sun ma ce a gaishe da ku."
Cikin far'a da murmushi ta ce "Muna amsawa, 'Yar Baba kazo dauka ko?, dan na san ita kad'ai ce zata iya kawo ka anan tunda zumuncin ma kuna son ku daina."
Da dariya yake cewa "wallahi Aunty ba haka ba ne ayukkanne wlhy sai a hankali dik su ne ke rik'e mu.!"
Ta ce "Bawani dai, wato kare kanka kake son kayi ko?."
gabadayen su suka ruftuma cikin wata arniyar dariya mai cike da ban sha'awa da kuma tsantsar farin ciki.

_Sannan ta ce " 'yar mama kije ki shirya ga Uncle dinku nan yazo daukar ki"
Cikin wata kasalalliyar murya ta'ansa da "Ok Mummy." kamar wadda kwai ya fashe ma a jiki, haka take tafiya jiki ba kwari kamar ta fad'i k'asa.

Mummy ta shiga kitchen ta had'o ma Uncle Mukhtar kayan motsawa a baki,
Farfesun kayan ciki ne da hollandia yoghurt vanilla and orange flavoured ta kawo mashi a flet sannan ta shiga dakin su Fatima domin duba ta dan taga alamun tana son ta b'ata mashi lokaci.

Ta b'angaren Oga farfesu kuwa tun lokacin da Uncle Mukhtar ya saka cokalin shi a ciki Flat har yanzu ya kasa fiddawa akan dadin da ya yi dan ji yake kamar ya hadiye flat din gabadai a cikin Cikin shi.

_Bayan kamar Mintuna biyar haka da shigar Fatima daki sai gata ta fito cikin wata kafirtacciyar shadda Getzner pink color, sosai wannan dinkin ya yi matuk'ar amsar ta, ko da ta fito Uncle Mukhtar ita kad'ai yake jira,
Nan take su kayi bankwana da su Mummy sannan suka dauke hanyar su ta tafiya gidan kakannin ta.

........

Ko da suka kawo gidan a daidai lokacin su kuma su Nusaiba Mahaifin su Attahir yazo daukar su,
Uncle Mukhtar na gyara parking d'inshi da kyau Fatima ta fito daga cikin motar tayi daidai da fitowar Nusaiba a cikin gida rik'e da akwatin su a hannu, cak ta tsaya kamar wadda aka kafe a wajen ko motsin kirki ta kasa yi, wa'iyazu billah wani mahaukacin kallo ne take dauke da shi wajen bin Fatima da shi mai d'auke da bak'in ciki tare da hassada da kuma nakkasa.

Sosai Fatima ta lura da hakan dik da ko kallon banza bata isheta ba ta nufe wajen Mahaifin su Nusaiba'r cikin girmamawa tare da dukawa har kasa ta gaida shi,
Cike da tsantsar farin ciki da annashuwa ya amsa mata, sai ga Marwan ya fito daga cikin gidan shi ma, yana ganin Fatima ya shiga yi mata oyoyoooo tare da tambayar ta yaushe ta dawo?."
Ita ma cikin murna da farin ciki tabi ta gaban Nusaiba taje har wajen da Ya ke dan a lokacin har Uncle Mukhtar ya zo wajen Attahir suna gaisawa.

_Bayan su Fatima sun gama ganin junan su ita da Marwan, sannan ta wuce cikin gida shi kuma ya nufi wajen da Uncle Mukhtar yake ya gaida shi cikin ladabi da biyayya, Uncle Mukhtar yarike hannun shi yaje da shi har wajen da ya yi Parkin din motar shi ya fiddo wata bak'ar leda a cikin boot ya bashi,
Da farin ciki Marwan ya duk'a har k'asa ya amsa tare da godiya,
Wanda dik abin da suke yi a idon Attahir, shi ma kallon su yake cike da jin dadin ganin yanda yaron shi yake da matuk'ar arbiyar, bayan ya amshi ledar Uncle Mukhtar ya kara yi ma Attahir sallama sannan ya wuce tare da bin gefen da Nusaiba take tsaye ko kallon inda take baiyi ba ya wuce, ciki ciki ta ce "Uncle an wuni lafiya"
Ba tare da ya tsaya bata amsa ba ya yi wucewar shi ciki, balantana ma ya tsaya sauraren abin da take fad'a d'in.

Ita ma wucewa tayi ta shiga Mota, daganan su ma suka dauki hanyar su ta tafiya gida.

....

Ko da Fatima ta isa ciki gidan, tun a bakin k'oofa ake yi mata barka da zuwan kilinbibi kamar haka "Sannunki da zuwa diyar Munafuka d'iyar tantiriyar makira Jikanyar algunguma amma ta wajen Uwa dan acan kika yi gado."
Ko kad'an wad'annan maganganun ba su damar da Fatima ba domin indai wannan ne ba sababben abu ba ne a wajen ta dan tasha jin fiye da irin wannan a gurin su.
Tana isa cikin Parlour'n wajen da suke ta durkusa har kasa ta gaida su.
Amma Ko kad'an basu da niyyar amsa mata, sai babbakun maganganun da suke ta famar zabga mata, sai dai ita dik da hakan ba su ne a gaban ta ba. Kai tsaye ta tashi ta wuce bangaren da aka fidda mata domin ajiye kayan ta sai dai da mamakin ta saiji tayi ance "Ke dan ubanki kawo Jakar nan muga abin da aka kunso ciki, dan-uban waye ma ya baki damar wucewa da ita cikin d'aki.........?
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin