040

111 10 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

EPISODE>>>40

Ko da Ammie tad'an waiwaya daga baya ta hango Balkisu tsaye tsangal acan nesa da ita kamar icce ko tangadi babu balantana karka, sai huci take tana cika tana batsewa.

Hakan ya yi matuk'ar faranta rai Ammie wanda har yakai ga ta fara ayyanawa aranta cewa Idan har ita ta kasa to tana da makamin da zai maye gurbin ta cewa da Balkisu.

Sai da ta dan ja daga baya kadan sannan ta walkadar da kanta daga baya hadida Saita gab'b'an jikin ta waje guda, sai ta fara takonta kadan-kadan a cikin isa da tak'ama kamar wata Army.

Ammie kan tsaye kawai take dik farin ciki ya gama lullube ta harta kaiga ta neme damuwar da ke damunta amma ta rasa, nan take ta cira hannunta sama ta saita shi a gefen goshinta ta dade da dubin Balkisu cikin Jinjinawa da martabawa ta Sara mata akan irin wannan namijin k'ok'arin da taga diyar ta ta, ta nuna.

Nan take Ammie ta tsinci kanta cikin wata irin Izza da jiji dakai hadi da shankanshi ..tare da hurar da hanci sannan ta wani bala'in tamke fuskarnan mai kama da ta jarirai, ba tare da b'ata lokaci ba ita ma ta rufama Balkisu baya.

Balkisu na isa daf da wannan motar tayi knocking galss din wajen mai tuk'i cikin wani irin k'arfin hali, da yake glass din motar dik tink ne da bak'in fenti wanda shi ya hanata ganin mutumin da ke cikin wannan motar.

Ita kuma Ammie ko da ta iso daf da motar direct sai ta shiga gewayen bayan motar kamar wata COSTOM, sai dai kuma abin da ta gani ya yi matuk'ar tsoratar da ita domin a maimakon ganin wata cikakkiyar mota mai rai da lafiya sai kuma aka samu akasin hakan domin mota ce a gaba kamar yanda suka gani amma a baya kuma honko ce, sabida iyakacin motar gaba ne amma a baya ko motar kwali ta fita zama cikakkiyar mota sannan ga wani zumdumemen rami a bayan mota, nan da nan hankalin Ammie ya yi mummunan tashi domin ta san babu shakka wannan ba mutum ba ne kamar yanda suka zata.

koda ta kalle wajen da Balkisu take tsaye sai ganinta tayi daure da fuska ta wani sha omo tana jiran fitowar shi kamar D'an-sanda da B'arawon asali, domin ita jira kawai take abud'e kofar motar ta fizgo wuyan mai Ita.
Kafin ta ankara sai ganin tayi an fara saukar da glass din motar kadan-kadan kamar ba'a son budewa, wanda
hakan ba karamin mugun bak'anta mata rai yayi ba, wanda har ta fara jin wani k'ololo bak'in ciki ya fara taso mata a can cikin k'ark'ashin k'asan zuciyar ta yana k'ok'arin tokare mata mak'ogoro akan haushin abin, nan take ta kauce fuskarta daga kallon motar domin ta san Idan har taci gaba da kallon wannan abin to babu shakka zata iya daukar motar sukutun ta cirata sama ta yar da ita.

Gyaran muryar da taji anyi ne ita ce tayi sanadiyyar sake maido da hankalin ta a nan cikin wani mugun b'acin rai.
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang