♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*EPISODE 41
kanta sake maida duban ta a wajen shi, nan take taji gabanta ya dinga duka uku-uku amma hakan ta matse cikin mugun k'rfin hali ta maida dubanta a wajen shi.
Hankalinta ne ya yi wani irin mummunan tashi a lokacin da idanuwan ta su kayi mummun tozali ga fuskar mamallakin wannan motar, kan tayi wani yunk'urin dauke fuskar ta daga kallon shi, tuni ta jita kamar abin da aka saka mata wani irin makeken icce aka tukare hab'ar ta, cikin k'arfin hali ta shiga kwace kanta daganan, amma ina sai dai abin ya citira dik yanda take tunanin abin yafi k'arfin hakan.
Wato a maimakon ganin wani cikakken mutum kuma hadadden gaye kamar yanda muryar shi ta nuna, sai dai an samu akasin hakan domin wani tangamemen B'era ne zaune a saman kujerar mai tuk'i, ya saka wani itin kafirtaccen madubin ido bak'i wulik wanda ake kira da No respect, sai tufafin dake sanye a jikin shi, Trousers ne blue sai wata black T-shirt,
Baki bud'e take kallon shi cike da mamaki da kuma wani wawan tsoro don tuni ta yada makaman yak'inta a k'asa ta zumduma tsunbulbul a cikin ramin tsoro, sai ganin tayi ya cire madubin da ke sanye a fuskar shi, sai ga wannan tatsatstsiyar fuskar ta shi tak'ara bayyana k'arara, tare da d'age mata Girar shi guda a sama tare da cewa "To yane My meat?."
wani abu ne taji ya ratsa cikin jikin ta ya wuce tsammmm, nan da nan taji jikin ta ya fara makarkata, kafin ta ankare sai jin tayi yana cewa "Na san na had'u ne sosai ba sai kinfad'a ba, to ya kika ganni kin san ko afuska dai mun dace da juna, I hope you ar erupting to havens love with me? so ki sake jikin ki mu wataye kawai, sannan karki damu da komai domin a gida na ba abin da narasa acikin sa, dik wasu abubuwan da kuke buk'ata zaku same shi a can!"
Balkisu kam ba abin da take yi sai famar kallon shi domin ba k'aramar firgici ne a tattare da ita ba wadda har ta fara bayyana k'arara a saman fuskar ta.
Tun yanda Ammie ta lura da hakan hankalin ta ya yi mummunan tashi domin tunowa da kashedin da Boka Mintsinkyu ya yi masu nan take ta gewayo ta wanjen su ba tare da ta sake kallon ko tayar motar shi ba dan tasan Ita ma ba wata jarumta ba ce awajen ta ba, Idan har ta tsaya kallon abin da Balkisu ta gani to babu shakka Ita ma zata iya tsintar kanta a cikin irin halin da ta tsinci Balkisu a ciki, cikin k'arfin hali taja Balkisu da k'arfin Allah kamar wata babbar jaruma, atake suka bar wajen cikin gaggawa.Kafin su kaiga wucewa daganan sukaji sautin mata makirar dariya yab'arke masu da'ita sannan ya ce masu "Karkuji komai zamu sake hadewa daku a sabon zangon ku taimaka kuyiman tattalin Naman jikin ku domin ba zaku tab'a kaucewa tarko na ba Ehihihihi!"
Ko da suka dan waiwayo ta bayan su, basu sake ganin ko tashin k'urar shi a wajen ba, aiko basu san lokacin da wata nannauyar ajiyar zuciya tazo masu ba kai tsaye.
Walkadar da kan su kadai keda wuya suka jiyo rididdinniya a bayan su anata sharb'ar gudu had'ida ihu, aiko cikin wani mugun firgici ko waccen su ta juya daga baya domin ganin abin da ke faruwa,
Sai dai kuma wani abu, nan take ko waccen su ta ce k'afa me naci banbaki ba, kan kace me ko waccen su ta wazge aguje cikin wani kafirtaccen gudu kamar masu Tayoyi ak'afa, domin abin da suka gani ya yi matuk'ar tsoratar da su.
Wani mahaukacin Jaki ne suka gani tsaye tsangal kamar mutum sai dai da ka kalli fuskar shi da k'afafuwan shi su zasu tabbatar ma da ainahin surar shi,
Sai famar tunkaro wajen da suke yake rik'e da wani jibgegen Marak'i, aiko tun yanda yaga su Ammie sun wazge aguje, nan take ya saki igiyar da ke daure ga wannan marak'in cikin wata mugunyar harzuk'a wannan Marak'in ya rufa masu baya aguje,
Su kam sai famar ihu suke suna sharb'ar gudu wanda ya zamana su kan su basu san inda suka nufa ba.
Nan take suka hango wani dan k'aramin kogo daga nesa aiko ba tare da tunanin komai akai ba suka fada acikin sa tsumdum tare da samun wani gefe na daban daga cikin wannan kogon suka dan labe, ko waccen su sai famar shashshek'ar wahala take yi, kafin su ankaro su kaji bayyanar fitowar wata murya a bayan su ana cewa "Wayyo dad'i bisa zallah! Rask'iyas kinga abin nema yazo ya same mu har wajen da muke, cikin mugun firgici ko waccen su ta waiwayi bayan ta.------
A b'angaren su Sa'idu munafuki kuwa.....
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
KAMU SEDANG MEMBACA
WAHALA DA GATA season1
FantasiSeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...